Labarin Raliya a gidan aure (5)

“Hakan ya sanya ni cikin tunani, inda na rika ramewa kamar kudin guzuri. Kallo daya za ka yi mini ka fahimci na shiga cikin ragar duniyar ukuba mai azalzalar zuciyata. Na rika kukan zuci da na fili, ni da walwala muka yi hannun riga. Amma babu abin da ya shafi Auwal. Da yake mahaifina bai […]

Labarin Raliya a gidan aure (5)

“Hakan ya sanya ni cikin tunani, inda na rika ramewa kamar kudin guzuri. Kallo daya za ka yi mini ka fahimci na shiga cikin ragar duniyar ukuba mai azalzalar zuciyata. Na rika kukan zuci da na fili, ni da walwala muka yi hannun riga. Amma babu abin da ya shafi Auwal. Da yake mahaifina bai cika zama a gida ba, kasancewar babban dan kasuwa ne da yake kasuwanci a kasashen duniya, don haka bai san dawan garin ba. Ya samu labarin halin da ake ciki ne wata rana ina tuki sai na yi hadari. Dalilin hadarin kuwa sakamakon tunane-tunane da mafarke-mafarke da na rika yi ne. A kullum idan ina barci, sai na rika jin ina koyon girki, idan kuma a farke nake, babu wani tunanin da nake yi sai na koyon girki, gaba daya na susuce, na kuma zautu.
“Hankalin mahaifina ya tashi, a nan mahaifiyata ta ce ba za ta sabu ba, bindiga ruwa, a kan batun girki ’yarta ba za ta mutu ba. Auwal ya nuna damuwarsa matuka a kan halin da na shiga. Ba wai ba ya sona ba ne, rashin iya girkina ne yake dada shi da kasa.
“Bayan na samu sauki ne mahaifana suka kira shi, sannan suka yi zaman yadda za a nemo bakin zaren. Mahaifiyata ta ce ba za ta yiwuwa ya kashe mata ’ya. Ya ba su hakuri hade da alkawarin komai zai zo karshe.
“A takaice ya yarda aka dauko mai girki hade da sharadin zan koyi girki. Hakan ya sanya na jajirice, wanda a yanzu Auwal ba ya iya cin abinci a waje idan ba nawa ba. Idan zai yi tafiya kuwa kullum yana cikin bakin ciki, domin ya ce zai yi nesa da abincin da ya fi gamsar da shi a duniya. Hakan ya sanya da zarar ya gama abin da ya je yi zai dawo gida. A yanzu dai rayuwar aurena ta inganta, komai ya daidaita, aminci ne a zuciyata, babu kuma sauran jigata.
“A karshe ina fata ’yan mata za su dage wajen koyon girki, domin girki wani sinadari da sihiri ne na mallake miji, dubi yadda ya nemi kassara mini aure. Ga sauran mata ma’aurata kuwa ina fata za su inganta, hade da samo dabarun girki don mallake miji. Ya kamata iyaye mata su tsaya kai da fata wajen koya wa ’ya’yansu girki don su cire musu kitse daga wuta a fannin gamsarwa ta bangaren girki. Ina kuma fata mazaje za su rika sauke nauyin da ya rataya a kansu ta fannin ciyarwa, shayarwa da sauransu. Allah Ya taimake mu, amin.
Launukan Soyayyar Ma’aurata
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwarmu cikin wannan fili. Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A yau kuma, inshaAllah, za mu tattauna kan ire-iren soyayyar da akan samu tsakanin ma’aurata; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu