Labarin sarin Kirista saboda ba ya azumi kirikira ne – Al’ummar Kakuri
A’ummar Unguwar Kakuri da ke karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna sun karyata labarin da ake yadawa cewa an sari wani matashi Kirista mai suna Francis Emmanuel (IBoyi) da makami saboda ba ya azumi.Sai dai shi Emmanuel Francis da ke kwance a gadon asibiti ya ce ba haka abin ya faru ba domin […]

A’ummar Unguwar Kakuri da ke karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna sun karyata labarin da ake yadawa cewa an sari wani matashi Kirista mai suna Francis Emmanuel (IBoyi) da makami saboda ba ya azumi.
Sai dai shi Emmanuel Francis da ke kwance a gadon asibiti ya ce ba haka abin ya faru ba domin shi ya je sayen itace ne aka kai masa hari. “Yaya za a yi in rike wuka bayan na je sayayya a kasuwa. Na sayo Opka ina ci, sai ga matasan sun zo suka tambaye ni me ya sa ba na azumi na ke cin Okpa sai na fada musu ni ba Musulmi ba ne. Kafin in ce wani abu sai kawai dayansu ya mare ni suka kuma sare ni da wuka. Idan ina da wuka a hannuna zan tsaya ne su kashe ni. Nan take na fita hayyacina, bayan na farfado aka fada min cewa wani dan kato da gora mai suna Sunday ne ya kawo ni asibiti,” inji shi.
A cewar, al’ummar wadanda suka yi magana a karkashin kungiyar Raya Kakuri wannan labari ba gaskiya cikinsa domin fada ne a aka yi a tsakanin Francis da wadansu matasa a Layin Sakkwato da ke Kakuri kuma sun yi fadan ne a bakin wani otel da ke layin a lokacin da matasan suka je layin domin kwato wata wayar hannu, shi kuma Francis wanda ake zargi da buguwa da giya ya nemi hana su ta hanyar cewa zai tona su idan suka kwace wayar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka rika yada jita-jitar cewa wadansu matasa Musulmi sun far wa Francis wanda aka fi sani da Iboyi a Kakuri suka kuma daba masa wuka saboda ba ya azumi. Yaduwar labarin ya sa Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’i da wadansu jami’ansa suka garzaya zuwa asibitin Saint Gerald inda matashin ke jinya.
Shugabannin Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci reshen jihar su ma sun ziyarci asibitin inda suka kai wa matashin taimakon kudi domin jinyarsa. Wannan ne ya sa ita kungiyar ci gaban Kakuri wanda Garkuwan Kakuri Rabi’u Ahmed ya jagoranta suka kira taron manema labarai domin bayyana musu cewa abin da ake yadawa ba gaskiya ba ne. kungiyar ta ce sun bincika sun gano ainihin abin da ya faru inda suka gano cewa shi dai Francis da wadancan matasa sun yi fada ne a bakin otel a unguwar wanda kuma jayayya ce a tsakaninsu kafin matasan su ji masa rauni.
Rabi’u Ahmed ya ce a wajen taron gaggawar da suka yi, mazauna unguwar, Musulmi da Kiristocinsu sun bukaci a ji tsoron Allah a daina dangata abin da ya faru a tsakanin matasan da Musulunci. “Muna da fahimta a nan Kakuri tsakanin Musulmi da Kirista. Saboda haka abin da ya faru babu ruwansa da addini domin ba saboda addini yaran suka yi fada ba. Da shi da suka yanka da wuka da su da suka yi yankar duk ’yan iskan unguwa ne. Su wadanda suka yi yankar ba sa ma yin azumin. Wannan abu ne da muka sani yana faruwa a nan Kakuri. Saboda haka kuskure ne wani ya jingina batun da addini ya ce wai an sari matashin ne saboda ba ya azumi wannan ba gaskiya ba ce. Ko Gwamna da ya je wajensa a asibiti ba a fada masa gaskiyar abin da ya faru ba,” inji jagoransu.
Ya kara da cewa: “Yaran da suka sare shi duk yaransa ne na aika-aika, sai dai mun ji dadi da ya ce idan suka shiga ciki suka kwaci waya zai tona musu asiri, me ya kawo maganar addini a ciki? Ba ruwanmu da bambancin addini, mu fito mu tona asirin irin wadannan yara wanda duk mun sansu a cikin Kakuri domin a zauna lafiya. Ya kamata mu daina irin wannan labari wanda ba gaskiya a cikinsa. Kullum muna zaune lafiya a nan unguwarmu. Duk mun san wadannan yara kuma ko Musulmi ko Kirista mu ji tsoron Allah mu rika fadin gaskiya domin abin da ya faru ba saboda ba ya azumi ba ne.”
A cewar wani matashi da ya yi bayani a wajen taron mai suna Solomon ya ce hakika matasan sun fito ne daga wata gona suna musu a tsakaninsu kafin suka riski Francis a bakin otel din bayan ya kammala cin alalen wake (Okpa). “Lokacin da yaran suka zo wajen su uku ne kuma kamar daga gona suka fito suna tafe suna musu. Bayan su iso inda Francis yake, sai ya bukaci su bar wajen da suka ki, sai rikici ya barke a tsakaninsu. Sai daya daga cikin matasan ya fito da almakashi domin caka wa Francis amma sai wani Nasiru wanda abokin Frandis din ne sai ya kare shi. daya daga cikin matasan ya riga ya karbe wukar da ke hannun Francis ya kuma yi amfani da wukar wajen daba wa Francis din,” inji Solomon.