Labarin wasan buya a rayuwar aure (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku mai taken ‘labarin wasan buya a rayuwar aure’. Muna fata za ku ci gaba da bin labarin sau da kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa: Daga Al-Bint’s DiaryFassara: Bashir Musa Liman “karfe 12:15 na dare […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku mai taken ‘labarin wasan buya a rayuwar aure’. Muna fata za ku ci gaba da bin labarin sau da kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa:
Daga Al-Bint’s Diary
Fassara: Bashir Musa Liman
“karfe 12:15 na dare sai ta ji kararrawar kofarta ta kada, a lokacin ’ya’yanta uku sun yi barci, ita kadai ta rika kai wa da komowa kasancewar mijinta bai dawo gida ba. Bayan ta karasa bakin kofar ne sai ta tambaya wane ne? Mijinta ya ce shi ne, wani dadi ya ratsa zuciyarta a lokacin da take bude masa kofar, abin da ta gani bayan ta bude kofar ya matukar girgiza ta. Wani yaro dan shekara biyar da alamar barci a idanunsa a tsaye kusa da mijinta ta gani. Bayan ta kalle shi ne ta ga yana kama da mijinta. Shi da mijinta kamar an tsaga kara, ta kalli mijinta amma ya yi shiru kamar an dasa shi, a lokaci guda ya kasa cewa komai, inda hakan ya jefa ta cikin rudani, ba ta san lokacin da ta ba su hanya suka shiga cikin gidan ba. Ta rufe kofar gidan. Bayan sun shiga gidan ma Bala ya kasa cewa komai, ya dai samu kansa kamar wani mutum-mutumi. Bayan ta kalli yaron sai tausayinsa ya kama ta, hakan ya sanya ta ce: “Bari in kai shi gado ya kwanta.” A lokacin ne Bala ya samu damar cewa: “Na gode.”
“Zahra’u ta kai yaron dakin ’ya’yansu bayan ta yi masa wanka ta sanya masa kayan barci na mata (na daya daga cikin ’ya’yansu). Bayan ta kwantar da shi ne sai ta dawo falon gidan, amma ba ta ga Bala ba, wanda hakan ya sanya ta leka dakinsa, a nan ta gan shi yana sallah. Bayan ta kwanta tana jiransa ne sai barci ya kwashe ta. Washegari bayan sun tashi za su yi sallah sai ya ki yarda su hada idanu, ba ta ce masa komai ba har ta shirya ’ya’yansu don zuwa makaranta, ’ya’yansu suka rika tambayar wane ne yaron, amma da yake ba ta san komai a kansa ba, sai ta ce musu wani dan uwansu ne. Bayan sun tafi makaranta sai ta ba yaron abinci, sannan ta tambayi Bala ko akwai kayan da za ta sanya masa, amma bai yi mata bayanin komai ba. Bayan dukkansu ukun sun ci abincin safe ne, sai Bala ya mike zai tafi wurin aiki ba tare da ya ce mata wani abu ba. A wannan lokacin ne ta ce:
“Ya kamata a sanya shi a makaranta.” Ta fadi hakan ne don ya zama matashiya ga tambayar da take so ta yi masa a kan yaron daga ina yake, amma ga mamakinta sai ta ji ya ce: “Wannan kyakkyawar shawara ce, ki sama masa makaranta mafi kusa.” Daga nan bai ce mata komai ba sai ya sa kai ya fita. Hakan ya bakanta mata rai, sannan ta ji wani haushi ya tsikari zuciyarta, bayan mijinta ya fita ne, ta juya ta tambayi yaron sunansa, a nan ya fada mata sunansa Sadik, bayan wadansu tambayoyi ne ta gano makaranta da yake da sunan mahaifiyarsa da kuma yadda mahaifiyarsa ta ce dole sai mahaifinsa ya tafi da shi, domin ta gaji da jira.
Haka ta rika sauraren Sadik har ya kammala ba ta labari, daga na ta yanke hukuncin ba za ta tunkari mijinta kai-tsaye ba.
“Tana kicin sai ta ji ya dawo gida, abin ya ba ta mamaki domin bai taba dawowa daga wurin aiki da wuri kamar a wannan lokacin ba, tana cikin yanka albasa ke nan, sai ’yarta ta shigo kicin din ta ce mahaifinsu na son magana da ita, hakan ya sanya ta ji hankalinta ya kwanta a tsammaninta yanzu ya amince zai yi mata bayanin halin da ake ciki. A lokacin da ta shiga dakinsa sai ta gan shi rike da ambulam a hannunsa, a lokaci guda ya ce:
“Ga wata ’yar karamar kyauta nan, za ki iya sayan sabuwar mota ko kuma ki ajiye a asusun ajiyarki, ko kuma ki yi duk abin da kike so ki yi da kyautar, domin taki ce.” Zahra’u ta karbi ambulam din sannan ta bude ta, a cikin ambulan din cekin kudi na Naira miliyan 5 ne, cikin saurin baki ta ce:
“Wannan kuma na mene ne?” Ya ba ta amsa: “Kyauta na ba ki.” Bayan ta kalle shi sai ta ce: “Na gode.” Abin ne yake ba ta mamaki, domin ba ta taba tsammanin yana da wannan kudin ba. Har ta mike ta fara tafiya za ta fita daga dakin ne sai ta juyo ta tambaye shi,
“Dangane da yaron nan fa, ko zan iya sanin daga ina yake?
Za mu ci gaba in sha Allahu.