Labarin wasan buya a rayuwar aure (4)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Muna fata kuna biye da mu a danganen da labarin wasan buya a rayuwar aure da muke kawo muku. A wannan makon za mu tashi daga wurin da muka tsaya a makon jiya, wato wurin da Tahir yake ba matarsa labarin halin da Usman ya samu […]

Labarin wasan buya a rayuwar aure (4)
Labarin wasan buya a rayuwar aure (4)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Muna fata kuna biye da mu a danganen da labarin wasan buya a rayuwar aure da muke kawo muku. A wannan makon za mu tashi daga wurin da muka tsaya a makon jiya, wato wurin da Tahir yake ba matarsa labarin halin da Usman ya samu kansa.

Daga Al-Bint’s Diary
Fassara: Bashir Musa Liman

“Ai wannan nata mai sauki ne, idan kika ji labarin tashin hankali da ya faru da kanwar Isma’il.” Ya ce mini bayan ya kalli agogonsa.
“Da gaske? Me ya faru da ita?” Na tambaya da sauri cikin zumudi. “Wane Isma’il ke nan?” Na sake tambaya cikin zumudi.
“Mataimakina a wurin aiki mana. Wata rana ya zo aiki a makare, kodayake ya aiko da sakon cewa wani abu ya tsayar da shi, don haka zai zo aiki a makare saboda wani abu na gida da ya shafe shi, bayan ya shigo ofis ne na ji yana ta guna-gunin a kan halin matasa maza na yanzu, hakan ya ba ni dariya, domin shi ma matashin ne, sai na danne dariyata, sannan na tambaye shi me ya faru yake wannan guna-gunin?”
“kanina Usman ne ya bata rayuwarsa.” Isma’il ya ba wa Tahir amsa.
“Ban gane ya lalata rayuwarsa ba? Me ya faru ne?”
“Shekarun da suka gabata ashe yana rayuwa da mata biyu, ma’ana matansa biyu kowa da gidanta da kuma ’ya’yanta. Ka san haka ya ci gaba da rayuwa kamar babu abin da ya yi? Hankalinsa kwance yake yawo a gari. Ban taba tsammanin zai iya haka ba.” Isma’il ya fada wa Tahir bayan ya zauna a kan kujera.
“Da yaya hakan ya faru? Yaushe ya auri mata biyu? Na san dai kan gayyace ni daurin aurensa na farko, amma ban da na biyu.” Tahir ya ce bayan ya gyara zama a kan kujera.
“Mu kanmu mun dauka matarsa daya, sai yau da safe ne nake jin labarin ashe matansa biyu, amarya ma tana da da, gare mu ‘yan uwansa daurin auren da na gayyace ka shi ne auren da muka san ya yi, kodayake abokin tagwaitakarsa Isa ya san da amaryarsa din. Isa ne ya tabbatar mini da batun auren Usman din, ya ce mini ya halarci daurin auren nan, har ma ya fito da hotunan da ke nuna cewa tabbas an yi auren.”Isma’il ya tsahirta bayan ya ja dogon numfashi.
“Wannan abin da mamaki da kuma daure kai, me ya sa ya zabi yin auren sirri?” Tahir ya tambaya, bayan muskuda don gyaran zamansa.
“Mun tuna lokacin da ya ce mana yana so ya auri wata kabila bayan ya kammala jami’a, ya ce mana ajinsu daya. Mun gargade shi illar da ke cikin yin hakan, mun fada masa iyayenmu ba za su taba yarda da haka ba, muka ce masa bai kamata ya yi aure yanzu ba, tun da bai dade da kammala jami’a ba, saboda babu wani aikin da yake yi da har zai ba shi damar iya rike aure, don haka ya ma daina batun aure, ya sanya wadansu abubuwa a gaba da za su taimake shi a rayuwa, sai ya yi kamar ya dauki shawarata, a lokacin ya ce zai yi hidimar kasa a lokacin kuma zai rika neman aiki.
Za mu ci gaba in sha Allahu.