Labarin wasan buya a rayuwar aure (5)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Muna fata kuna biye da mu dangane da labarin da muke kawo muku. A wannan makon ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a makon jiya. A sha karatu lafiya Daga Al-Bint DiaryFassara: Bashir Musa Liman “Don haka bayan ya ji cewa ya tsaya […]

Labarin wasan buya a rayuwar aure (5)
Labarin wasan buya a rayuwar aure (5)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Muna fata kuna biye da mu dangane da labarin da muke kawo muku. A wannan makon ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a makon jiya. A sha karatu lafiya

Daga Al-Bint Diary
Fassara: Bashir Musa Liman

“Don haka bayan ya ji cewa ya tsaya da kafafunsa sai ya auri wata yarinya da ke kauyen da yake hidimar kasa, babu wanda ya sani a cikinmu, sai dan uwansa. Abin da daure mini kai a ce iyaye su ba wani aure ba tare da sun gana da iyayen surakansu ba. Babu abin da ya dame su, suka daura wa ’yarsu aure da shi. A wurinsu dan uwansa ya wadatar
“Haka aka daura aure Usman ya ci gaba da zama da matarsa cikin sirri. Bayan shekara biyu ne ya sake aurar matarsa ta biyu, wadda muke tsammanin ita ce ta farko, kuma shi ma haka ya rika nuna wa mutane. Kasancewar matar tasa wadda a yanzu muka gane ta biyu ce, ya zabo ta daga gidan mutunci, hakan kuma ya burge jama’a da dama. A yanzu ne muke mamakin me ya fada wa matarsa ta farko har ta yarda ta rike auren a matsayin na sirri, duk da cewa sun haihu, haka ya rika lura da su cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba har tsawon shekara bakwai, sai abin da ya faru a jiya da daddare, da misalin karfe 7 na safe na gan shi cikin tashin hankali a gidana, ya ce mini matarsa ta tattara kayanta, don haka in taimaka in ceto masa aurensa.
“Ya ce mana al’amarin ya faru ne shekaranjiya bayan sun ci abincin dare, suna zaune suna hira sai suka ji kararrawa ta amsa, hakan ya sanya Hajara (matarsa) ta je ta duba ko wane ne, bayan ta bude kofa sai ya ji shiru saboda ta ga wata mata a tsaye a kofar gidan namu da yara uku ba tare da ta ce wani abu ba. Amma duk da haka sai da Hajara ta ce mata: “Sannu da zuwa. Wa kike nema?” Sai ta amsa mata da mijinki, hakan ya sanya ta ba ta hanya bayan ta ce shigo daga ciki. Bayan ta shigo har sun hada idanu da Usman ne sai ya kidime sakamakon girgizar da ya yi, cikin saurin baki ya ce mata: “Me kike yi a nan kuma, me kike so?”
“Bayan ta kalle shi, sannan ta kalli Hajara sai ta ce “Ina so ’ya’yana su ga ’yan uwansu.” Saura kadan Hajara ta suma sakamakon girgizar da ta yi, duk da cewa ta ga ’ya’yan suna kama da mijinta. Duk da haka ba ta ce komai ba, bayan kallon Usman da take yi don jin me zai fada mata, abin da ya kara girgiza ta shi ne, ya kasa cewa komai, idan ban da guna-gunin da yake yi, wanda kuma ba a jin me yake cewa. Daga baya ne ya fara magana:
“Wannan matata ce, sunanta Wasilah” Hajara ta ce: “Ina tsammanin wadannan ’ya’yanka ne?” Sai ya ce mata eh. Hakan ya sanya Hajara ta kwashi ’ya’yanta, ta dauki makullin mota, sannan ta fice daga gidan. Daga nan Usman ya fara surutu a kan me ya sa za ta kashe masa aure, sai ta masa ko kadan ba ta yi nadamar abin da ta aikata ba, saboda ta gaji boye-boye, bayan haka ita matarsa ta sunna ce, ba wai zaman dadiro suke yi ba. Ita ma daga nan ta fice daga gidan, inda Usman mai mata biyu ya yi biyu babu.
“Haka ya rika kaiwa da komowa har gari ya waye, inda da sassafe ya zo wurina yana rokon in taimaka masa a shawo kan aurensa, don matansa biyu kowa ta koma gidanta. Na ba shi shawarwari kafin na amince in je bikon Hajara.”
Za mu ci gaba in sha Allahu.