Labarin wasu yara biyu
Wata rana wasu yara biyu masu suna Chindum da Kundum sun tashi daga makaranta, kan hanyar dawowar su sai Chindum ya hango wani icen mangwaro. Ya’yan mangwaron sun yi jajir, sai kwadayin shan mangwaron ya kama su. Nan take ya ce wa abokinsa Kundum, kai! Ga mangwaro, mu shiga lambun nan mu tsinko mana, sai […]
Wata rana wasu yara biyu masu suna Chindum da Kundum sun tashi daga makaranta, kan hanyar dawowar su sai Chindum ya hango wani icen mangwaro. Ya’yan mangwaron sun yi jajir, sai kwadayin shan mangwaron ya kama su. Nan take ya ce wa abokinsa Kundum, kai! Ga mangwaro, mu shiga lambun nan mu tsinko mana, sai Chindum ya hau kan bishiyar mangwaro yayin da Chindum yake tara wa a jakar makarantarsu.
Suna cikin haka sai mai lambu ya ji su. Ya nufo su yana fadin wa ya ce ku hau kan mangwaro nan ba tare da izini ba? Yau sai na yi muku dukan da ba za ku taba mancewa ba.
Kundum da jin haka sai ya runtuma da gudu ya bar jakukunan makarantarsu shi kuma Chindum da ke kan iccen mangoron, ya kasa sauka, yana ta wayyo Baba don Allah ka gafarce mu, ba za mu kara ba, ka cece ni na tuba!
Tsohon na jin irin rokon da wannan karamin yaron ke yi sai ya ce na ce ka sauko. Chindum ya sauko jikinsa na kakkarwa da saukarsa sai tsohon ya ja masa kunne ya ce da shi ya tafi ya yafe musu amma kada su kara. Chindum na jin haka sai ya kwashe jakarsu ya ruga a guje, tsoho yayi murmushi, ya ce Allah sarki yaro man kaza.
To manyan gobe, da fatan kun lura da darasin wannan labarin da ke nuna kada ku taba abinda ba na ku ba, sai da izinin mai shi.
Taku Gwaggo Halima