Labarin wata mata da jimina
Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya? A yau na kawo muku labarin wata mata da jimina. Labarin yana koyar da bai kamata a rika zargi kan abin da babu tabbas. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin wata mata da jimina A wani lokaci da ya wuce akwai wata mata […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Ina fata kuna cikin koshin lafiya? A yau na kawo muku labarin wata mata da jimina. Labarin yana koyar da bai kamata a rika zargi kan abin da babu tabbas.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin wata mata da jimina
A wani lokaci da ya wuce akwai wata mata da ta dauki akwatin duwatsun gwal da lu’u-lu’u da sauransu don ta kai wa wani makeri, don ya kera mata abin wuya. A kan hanyarta, bayan ta kusa zuwa gidan makerin, sai akwatin ya fadi kayan ciki suka zube.
Bayan makerin ya ga abin da ya faru ne, sai ya tura dansa don ya taya ta kwashe wadannan duwatsun.
Suna cikin kwashe duwatsun, sai ga wata jimina ta zo, kan a ce wani abu tuni ta hadiye babban dutsen lu’u-lu’un. Matar da dan makerin suka shiga neman babban dutsen, amma ba su samu ba.
A gefensu akwai wani mutum da ke zaune, sai suka zargi shi ne ya dauke dutsen lu’u-lu’un, sai suka tara masa mutane har aka fara dukansa. Yana cewa ba shi ya dauka ba, amma suka ki yarda.
Mutumin ya gaya musu cewa ya ga wata jimina ta hadiye dutsen, amma suka ci gaba da dukansa, har sai da wata tsohuwa ta dakatar da su. Ta ce a kamo jimina, bayan an kamo jiminar ne, sai aka ba mai jimina kudinta, daga nan aka farke cikinta. Bayan an fyede ta ne sai aka ga babban dutsen lu’u-lu’un a cikinta.
Sai mutumin da ake zargi da sata ya ce a biya shi, ko ya rama dukan da aka yi masa. Haka matar ta ba shi kudi mai yawa.