Labarin Yaro da Kunama
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon na kawo muku labarin ‘Wani Yaro da Kunama’. Labarin na kunshe da darasin duk wanda bai ji bari ba, to kuwa zai ji hoho.A sha karatu lafiya Labarin Yaro da Kunama An yi wani lokaci akwai wani yaro marar ji, duk […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon na kawo muku labarin ‘Wani Yaro da Kunama’. Labarin na kunshe da darasin duk wanda bai ji bari ba, to kuwa zai ji hoho.
A sha karatu lafiya
Labarin Yaro da Kunama
An yi wani lokaci akwai wani yaro marar ji, duk abin da aka fada masa ba ya saurarar mutane. Ya cika rigima, komai ya gani sai ya taba, ko kuma ya lalata. Mahaifiyarsa babu irin nasihar da ba ta yi masa amma ya ki ji, wani lokaci har ta lakata masa duka amma hakan ba zai hana ya ci gaba da rashin jinsa ba.
“Idan ba ka daina rashin ji ba, wata rana za ka hadu da gabanka, a lokacin za ka dandana kudarka, za ka kuma fahimci lallai rashin ji ba shi da amfani.” Inji mahaifiyarsa wata rana tana yi masa nasiha. Amma bai saurare ta ba, ya fita waje yana guna-gunin ana takura masa.
Wata rana ya zo zai sanya takalminsa, sai mahaifiyarsa ta ce masa ya zazzage takalminsa, sannan ya share kafarsa kafin ya sanya takalmin, amma ya yi kamar bai ji ta ba, zai sanya takalmin ke nan ta sake fada masa, amma ya ki bin umarnin da ta yi masa.
Ashe abin da bai sani ba shi ne, akwai kunama a cikin takalmin, bayan ya sanya ne ta harbe shi, a nan ya rika kuka, hankalin mahaifiyarsa ya tashi bayan kunamar da ta harbe shi ta fito daga cikin takalmin. Daga nan ta dauke shi zuwa wurin mai magani. Bayan an yi masa magani sun dawo gida ne, sai ya rika tunanin abin da ya yi bai kyauta ba, duk da haka mahaifiyarsa ba ta guje shi ba, ta taimake shi duk rashin bin umarninta, ya yi nadama, sannan ya roki gafara a wurin mahaifiyarsa. Ta yafe masa, tun daga ranar bai kara ketare umarnin da mahaifiyarsa ba.