Labarin yaro mai karya

Barka da warhaka Manyan Gobe Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya shirye-shiryen sallah? Allah Ya sa a yi da mu cikin koshin lafiya, amin. A yau na kawo muku labarin yaro mai karya. Labarin na nuna illar yin karya da kuma abin da take haifar wa mutum. Da fatan za ku nazarci labarin. A sha karatu […]

Labarin yaro mai karya
Labarin yaro mai karya

Barka da warhaka Manyan Gobe

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya shirye-shiryen sallah? Allah Ya sa a yi da mu cikin koshin lafiya, amin. A yau na kawo muku labarin yaro mai karya. Labarin na nuna illar yin karya da kuma abin da take haifar wa mutum. Da fatan za ku nazarci labarin.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin yaro mai karya

Akwai wani yaro, babu abin da ya iya sai karya. Rannan sai aka kai shi makarantar kwana; shi kuma ba ya son makarantar, hakan ta sanya ya fara kage-kagen karya daban-daban. A cikin karyar da ya fi yi ita ce yana ciwon ciki.
Idan ya yi karyar ciwon ciki, sai a dawo da shi gida. Daga dawowarsa gida sai ya debo kayan wasa ya fara wasa. Ganin hakan, sai iyayensa suka ce wa malamin da ya kawo shi, ya mayar da shi, sannan ko ya sake cewa cikinsa na ciwo, to kada a dawo da shi gida domin karya yake yi.
Bayan an mayar da yaron makaranta da sati daya, sai ya kamu da ciwon ciki mai tsanani. Nan take sai ya gaya wa malamansa cikinsa na masa ciwo. Malaman suka ki yarda da shi, a zatonsu karya yake yi.
A hakan ya yi ta fama da ciwon cikin har sai da aka ga ya suma, sannan aka kai shi asibiti, har aka yi masa  karin ruwa. Bayan ya samu lafiya ne ya roki iyayensa da malamansa da sauran dalibai afuwar karyar da ya yi musu, sannan ya dauki alkawarin ba zai sake ba.
Da fatan Manyan Gobe za su kasance masu fadin gaskiya a duk halin da suka tsinci kansu. Kun ga da yaron ya saba fadin gaskiya ne bayan ya fara ciwon ciki sai a mayar da shi gida. Amma da yake karya ya sa a gaba, kun ga ko ya wahala. Allah Ya sa mu dace amin