Labarin ’ya’yan Sarki su biyu

Barkanmu da warhaka Manyan gobe.  A yau kuma na kawo muku wani labari ne mai kunshe da darasi, ina fata za ku natsu wajen karanta labarin don ku fahimci inda ya dosa.  Da fatan za ku amfana da wannan labari. A wani lokaci an yi wani sarki yana da ya’ya maza biyu. Wannan Sarkin yana […]

Labarin ’ya’yan Sarki su biyu
Labarin ’ya’yan Sarki su biyu

Barkanmu da warhaka Manyan gobe.  A yau kuma na kawo muku wani labari ne mai kunshe da darasi, ina fata za ku natsu wajen karanta labarin don ku fahimci inda ya dosa.  Da fatan za ku amfana da wannan labari.

A wani lokaci an yi wani sarki yana da ya’ya maza biyu. Wannan Sarkin yana matukar ji da su. Har ta kai baya barin su fita su kadai ba tare da ya sa dogarai sun bi su ba. Kai hatta in suna bacci ana kula da su. Yaran gwanin ban sha’awa don sun kasance suna da ladabi da biyayya ga iyayensu da kuma daukacin mutanen gari. Har mutanen kauyen suna musu kirari da farin wata hasken kowa.
Ana nan, wata rana su biyu wa da kane sun fita yawon shakatawa, sai babban wan ya ga wani naman daji, sai ya sulale yana ta bin naman dajin har ya bata. dan uwan da masu gadi suka yi ta neman sa, ba su gano shi ba. Dole ta sa suka koma fada aka sanar da Sarki abin da ya faru. Nan da nan Sarki ya sa aka baza masu nema ko’ina amma babu labari sa. Hakan ta sa Sarki ya kamu da bugun zuciya har ya mutu.
Baya ’yan kawanaki, aka yanke shawara na kanen ya zama Sarki, tunda ba a samu labarin yayansa ba. Har an gama komai, yaro ya gaji mahaifinsa, kwatsam! wata rana sai wansa ya dawo. Daga nan mutane suka shiga zullumin ko me zai faru da dawowar yayansa. Ko zai yi rikici akan hakan, kafin ka ce kwabo kanin ya yanke shawarar ya sauka daga kan kujerar don ya ba yayansa dama ya cigaba daga inda mahaifinsu ya bari. Shi kuma yayan ya ce ai hakan ba za ta taba faruwa ba, tun da ana riga an nada masa rawani, babu dalilin da zai sa ya ce zai ajiye sarauta don kurum shi ya dawo daga bacewar da ya yi. Haka dai aka cigaba da dambarwa har mutanen gari suka sanya baki kuma aka shawo kansu, yayan ya amince ya karbi ragamar sarautar shi kuma kanin ya ja da baya ya cigaba da yin biyayya. Hakan ta sa mutanen hari suka yaba da dabi’un wadannan yara kuma sun tabbatar lallai soyayyar da ke tsakaninsu ta gaskiya ce.
To Manya Gobe ku zama masu ladabi da yin biyayya don samun albarka.
Taku Gwaggo Halima