Labarin Zakara Da Giwa

Barka da warhaka Manyan Gobe Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon gwaggwonku A’isha Kabir Jos ce ta yi muku guzurin ‘Labarin Zakara da Giwa’. Ina fata Manyan Gobe za su nazarci labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa.A sha karatu lafiya.Gwaggonku: Amina Abdullahi Labarin Zakara Da Giwa Wata rana zakara zai […]

Labarin Zakara Da Giwa
Labarin Zakara Da Giwa

Barka da warhaka Manyan Gobe

Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon gwaggwonku A’isha Kabir Jos ce ta yi muku guzurin ‘Labarin Zakara da Giwa’. Ina fata Manyan Gobe za su nazarci labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa.
A sha karatu lafiya.
Gwaggonku: Amina Abdullahi

Labarin Zakara Da Giwa

Wata rana zakara zai fita kiwo sai ya kira ‘ya’yansa ya ce musu kada su fita waje, saboda gidansu na kan hanyar da giwa ke wucewa. Bugu da kari kuma, sun yi kanana za ta iya taka su ta wuce ba tare da ta gan su ba. Bayan ya sallame su ne ya fita. Ya fita ke nan sai babban cikinsu ya ce da sauran ku zo mu fita wasa kafin baba ya dawo, ba su yi gardama ba suka bi shi. Suka yi ta wasa har lokacin wucewar giwa ya yi, inda kuma har ta take su ba ta sani ba.
Bayan zakara ya dawo ne sai bai ga ‘ya’yaansa ba, hankalinsa ya tashi, daga nan ya fita nemansu har ya tarar da inda giwa ta take su. Ya yi bakin ciki sosai. A kan hanyarsa ta koma wa gida sai ya hadu da giwa, sai ya ce mata kin kasance mai girma, ga karfi, amma kuma marar tausayi. Giwa ta fusata ta yunkuro kamar za ta hadiye shi. Zakara  ya ja gefe sannan ya ce zan kai kararki wajen alkali sai an hukunta ki. Ya tafi gidan alkali. Alkali ya sanya aka kira giwa. Daga nan zakara ya yi jawabi. A nan giwa ta ce ranka ya dade wallahi ban gan su ba, amma ka tambayi zakara me ya sa bai hana ‘ya’yansa fita ba tun da ya san kanana ne, kuma ya san ba zan iya ganin su ba. Kafin giwa ta rufe baki caf zakara ya ce na gargade su kada su fita. Alkali ya ce, to ai giwa ba ta da laifi kuma zakara ma ba shi da laifi. Laifi na ‘ya’yansa ne, tun sun ki bin umarninsa. Yanzu hakuri ya kamata ya yi, giwa kuma ta sani ba ita kadai ba ce a wannan dajin. Manyan Gobe a rika bin umarnin  iyaye.
A’isha Kabir Jos, 08180210250