Labarin Zaki da Kurege
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A wannan makon na kawo muku Labarin zaki da kurege. An yi wani zaki ne da ke musguna wa sauran namomin daji don ya fi su karfi. Haka kawai yake kashe su ba tare da wani dalili ba.To sauran namomin daji sai suka rika yin […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A wannan makon na kawo muku Labarin zaki da kurege.
An yi wani zaki ne da ke musguna wa sauran namomin daji don ya fi su karfi. Haka kawai yake kashe su ba tare da wani dalili ba.
To sauran namomin daji sai suka rika yin shawarar yadda za su shawo kan matsalar. Ana cikin haka wata rana kurege na yawon neman abinci sai kawai ya hango zakin nan, yana ganin haka ya san tasa ta kare, amma sai wani tunani ya zo masa na hanyar da zai bi don ya samu tsira.
Da yake ya san zakin na da jarumta fiye da ko wane naman da ji sai ya nufi wani gulbi da ke kusa yayin da shi kuma zakin na biye. Kurege na kai wa kusa da rafin sai ya yi tsaye yana ta magana da kargi kamar yana jayayya da wani.
Da zakin ya ga haka sai abin ya ba shi mamaki sai kawai ya tsaya yana kallonsa da mamakin da wa yake magana? Sai ya yanke shawarar ya yi tambaya kafin ya halaka shi.
Da zaki ya tambayi kurege sai ya juyo, ya ce, ranka ya dade wai wani ne a nan yake ta jayayya da ni wai ya fi ka karfi. Zaki na jin haka sai ya daka tsalle ya nufi inda ruwan ya ke. Da zuwa sai ya ga wani abu kamar a cikin ruwan bai san hoton kansa yake kallo ba. Saboda haushi da tsuma sai ya yi tsalle ya fada cikin ruwan don ya kashe dabbar da aka ce ta fi karfinsa. Fadawarsa cikin ruwan ke da wuya sai ruwa ya yi gaba da shi shi kuma Kuerege da ya ga haka sai ya kama gabansa. Yana isa masauki sai ya fada wa sauran dabbobin cewa daga yau babu sauran Zaki don ruwa ya tafi da shi. Nan fa suka yi ta rawa suna murna a kan abin da ya faru, don tun daga wannan lokaci suka samu ’yanci.
Da fatan Manyan Gobe sun fahimci labarin inda yake nuna babu kyau yin zalunci da kuma sauran fushi.
Sai mako na gaba insha Allah
Taku Gwaggo Halima