Labarin Zamantakewar Aure: Martanonin masu karatu
Gaisuwa mai yawa ga masu bibiyar dandalin FDK (Filfilon Dausayin Kauna). FDK na taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadan, tare da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan albarkokin da ke cikinsa, amin. A wannan mako, za mu yi tariya ne dangane da labarin Zamantakewar Aure da muka kawo a makon jiya, inda […]
Gaisuwa mai yawa ga masu bibiyar dandalin FDK (Filfilon Dausayin Kauna). FDK na taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadan, tare da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan albarkokin da ke cikinsa, amin.
A wannan mako, za mu yi tariya ne dangane da labarin Zamantakewar Aure da muka kawo a makon jiya, inda masu bibiyar filin nan suka tofa albarkacin bakunansu. Don haka bari mu bibiyi wasu daga cikin sakonnin da suka samu damar shigowa a sahun farko. Kafin sannan, muna kara ba da hakuri ga wadanda ba su ga sakonsu ba, wanda haka ya faru ne saboda yawan sakonnin da muka samu.
***
Bari mu fara da sakon Muhammad Hassan Danbaza, Rediyon Zamfara, Gusau (07068040761), wanda ya ce: “FDK, wannan ai ko ba a fada ba kowa ya san cewa rayuwarta ta lalace ta hanyar haduwa da samarin banza kuma hakan yana faruwa da yawan gaske, sai dai Allah Ya sa mu gane gaskiya gaskiya ce kuma Ya ba mu ikon bin ta.”
Shi kuwa Y. Y. Dantsoho, Kaduna (08979901259) cewa ya yi: “FDK, lamarin nan akwai takaici, tsanani da tausayi. Mahaifin yaran nan ya yi asara kwarai. Matar ma barin shi za ta yi wata rana, ya yi da na sani. Ga yarinya mai bilicin, kawaye da kuma ganin masu yi ya sa ta yin hakan, kudin saye na iya fitowa daga samari da hanyoyi na daban-daban. Dan da ba naka ba, da wuya ka kula da shi kamar naka. Zai yiwu matar da ke tare da ita ta saka ta yin shafe-shafen don wasu bukatunta. Allah dai Ya kara tsare mu, amin.”
Sai kuma Zainab M. Bello Kano, wacce ta ce: “FDK amma don Allah kada a sa lambata, assalama alaikum. Gaskiya mun ji dadin dawowar wannan shafi. To a gaskiya wannan yara ya dace a sanar da mahukunta da wadanda abin ya shafa. Na gode.”
FDK ya samu sako daga Muhammad M. Sakkwato (08127402963), yana cewa: “Da fatan an yi Jumu’a lafiya. Gaskiya ba ni da abin da zan ce sai in yi muku fatan alheri.”
Daga Suleiman Maidoya Sabon Gari Zariya (07039135470), yana cewa: “FDK, ai wannan a fili yake, kadangarun bariki ne suke saya mata; Allah Ya tsare mu, amin.”
Daga Ikra Isah ’Yantakori, Katsina (08036141059), sakonsa na cewa: “Hmm! Yaran abin tausayi. Ni shawarar da zan bayar a kanmu ne mu maza, idan matanmu sun rasu ko mun rabu da su mun auro wadansu, ba komai za su fada mana game da ’ya’yan wacce muka rabu da ita ba; sai mun yi bincike tukunna. Domin ai da ma tsammanin da ake, su fadi ba daidai ba a kansu.”
A sakonta, Hauwa’u Ahmad (08104188656), ta dora laifin bilicin da yarinyar take yi a kan samarin banza, inda take cewa: “Ni dai a ganina, samarin banza gare ta.”
Sai kuma Amina Muhammad Kaduna (07031626257), wacce ta nuna takaicinta da kuma tausayin yanayin da yaran suka shiga. Ga abin da take cewa: “FDK, gaskiya rayuwar yaran na cikin garari, musamman budurwar, tun da har ta fara bilicin.”
Shi kuwa Anas Nuhu Rijiyar Lemo (07034312244) yana cewa: “Assalamu alaikum FDK, barka da warhaka. Gaskiya FDK, zaluncin matar uba bai yi ba. Ya kamata uban ya duba lamuran ’ya’yansa, ganin yadda ya fifita matarsa a kan ’ya’yansa, sakamakon zalunci na sabuwar matarsa, musamman yadda rayuwa ta lalace kuma kowa nasa ya sani. Allah Ya ganar da ubansu ya dawo ga ’ya’yansa.”
Sai kuma sakon Nasiba A. Mato (08149023190), wacce ta bayyana cewa: “Muna jin dadin rubutunku. Allah Ya taimake ku, da fatan za a ci gaba da labarin da aka fara.”
***
Malama Nasiba, ai labarin ya kare a nan, sai dai za mu ci gaba da bibiyar mataki na gaba, domin jin yadda ta kaya a gaba. – FDK.
***
Ita kuwa Nusaiba Abubakar Sakkwato (0810 290 5542), hasashe ta yi dangane da inda wannan yarinya mai bilicin take samo kudi. Ta ce: “Watakila samari ne suke ba ta kudin sayen man bilicin.”
Zaharaddin Isa Abdullahi (08036986928) ya aiko da nasa sakon, yana cewa: “Ta hadu da kawayen banza, sun hada ta da mutanen banza. Allah Ya kyauta.”
Daga Bashir Salisu Dansadau (08075707272), yana cewa: FDK, ni dai a ganina wurin da yarinyar nan ta samu kudin shafe-shafe ba wurin kwarai ba ne. Sannan mai yi mata jagoranhin yin hakan yana iya yiyuwa matar da take wurinta ce. Allah Ya sawake, da fatan mu iyaye za mu kiyaye hakan a gidajenmu.”
Daga Nura Mai Apple Gusau (08133376020), ya ambata cewa: “Muna lale marhabin da dawowar dandalin FDK na Dausayin Kauna. Muna yi wa dinbin al’ummar da ke biyar wannan shafin barka da watan Ramadan, da fatan matan da ba su iya abinci ba za su koya su iya kafin wucewar Ramadan.”
***
Madalla da wadannan sakonni kuma da fatan za ku ci gaba da bibiyar wannan shafi domin fantamawa a lambun FDK.