Labarin Zomo da Kunkuru

Manyan Gobe barka da warhaka Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon Kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku labarin Zomo da Kunkuru. Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa.A sha karatu lafiya.Labarin Zomo da Kunkuru A baya an taba yin wani […]

Labarin Zomo da Kunkuru
Labarin Zomo da Kunkuru

Manyan Gobe barka da warhaka

Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon Kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku labarin Zomo da Kunkuru. Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa.
A sha karatu lafiya.
Labarin Zomo da Kunkuru

A baya an taba yin wani zomo mai gudu har ta kai yana ikirarin duk cikin namun daji babu mai iya tsere masa. Ganin abun nasa yana neman wuce gona da iri, sai kunkuru ya fito domin a bambance tsakanin aya da tsakuwa. Duk namun daji suka taru domin ba da shaida.
Fara tseren ke da wuya zomo ya shiga gudun fanfalaki na wani dan lokaci, sannan ya juya hangi kunkuru can nesa yana tafiya hankalinsa kwance kamar ba da shi ake tseren ba. Ganin haka, sai Zomo ya daga murya: “Kai yau ka cika shashasha. Ta yaya kake tsammani za ka iya tsere mini alhali kana irin tafiyar da ka saba?”  Zomo yana fadin haka, sai ya kwanta a gefen hanya har barci ya dauke shi, a tunaninsa akwai ishasshen lokacin hutawa kafin kunkuru ya karaso.
Shi kuma kunkuru yana ta tafiya ba tare da nuna gajiyawa ba har Allah Ya sa ya wuce zomo yana barci. Ko da namun daji suka ga Kunkuru ya kai karshe, sai suka hau shewa suna taya Kunkuru murna.
Firgigit! Zomo ya farka daga barci yana ganin abin da ke faruwa ba tare da ya jira komai ba ya fara gudu amma duk a banza.
Ya kamata Manyan Gobe su fahimci mai alfahari ba ya tare da nasara.