Labarina ya sauya tunanin iyayen da ke hana ’ya’yansu aikin dan sanda —DPO da ya lashe musabaka
SP Mahi ya ce duk mako yakan sauke Alkur’ani, amma bai yi zaton zai zo na daya ba
A watan jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta shirya musabakar Alkur’ani a karo na farko, inda Baturen ’Yan Sanda (DPO) na Takai a Jihar, SP Mahi Ahmed Ali ya zama zakara.
A tattaunawar da Aminiya, ya bayyana gwagwarmayar rayuwarsa har zuwa samun nasarar da yadda labarinsa ya sauya tunanin mutane da dama kai aikin dan sanda.
- DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano
- An kama bindigogi 35 da masu muggan laifi 245 a Kano
Mene ne tarihinka a takaice?
To an haife ni a ranar 17 ga watan Maris, 1980 a Unguwar Gyaranya Takalmawa da ke Karamar Hukumar Gwale yanzu.
An haife ni a zuri’ar Sheikh Malam Ahmad Modibbo, Khalifa ne na Sheikh Sani Likoro, kuma na taso a nan unguwar.
Na fara makaranta a tsari irin na tsangaya a makarantar Malam Mahmud Barnoma da ke Unguwar Sanka a Karamar Hukumar Dala.
A nan na fara koyon bakake da wasali, zuwa fara karatu sosai har na yi sauka ta farko.
Bayan sauka ta farko na juyo na yi gyara rub’i-rub’i bayan haka na zo na fara Satu.
Na yi saukar Satu sau hudu a makarantar kafin in koma Tsangayar Sheikh Malam Rabi’u Gwale da ke Ja’en, inda na yi sauka ta daya na juyo a ta biyun kuma abubuwa suka dauke ni na karatun zamani, sai ban ci gaba ba.
A tsarin karatun zamani kuma wannan makaranta tamu ta rikide ta koma ta zamani inda a nan muka yi firamare.
Sannan Aliya ta Shahuci ita ce sakandaren da na yi sai na yi Diploma a Kwalejin Shari’a (Legal) da ta ke nan birnin Kano, na karanta Kimiyyar Alkur’ani, bayan haka na samu gurbin karatu zuwa kasar Sudan, inda na yi digiri a fannin Larabci, wato Lugga Ajnabiyya.
Yaya aka yi ka shiga aikin dan sanda?
Bayan dawowa ta daga Sudan, na yi hidimar kasa a Jihar Kebbi, bayan kammalawa na dan yi koyarwa a wani gari da ke Karamar Hukumar Bunkure, ana kiran sa Barkum na kusan wata takwas.
A shekarar 2009 ce lokacin da na nemi aikin dan sanda wanda aka kira mu a farkon 2010, bayan mun kammala komai sunana ya fito aka dauke mu aka yi mana horo a 2010.
To a 2010 ne na fara aikin dan sanda.
A kwanakin baya Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta shirya Musabaka ga jami’anta, a karon farko a tarihi kuma cikin ikon Allah ka zama zakara a gasar. Yaya aka yi kuka shiga gasar?
Eh, gaskiya ce a watan jiya an gabatar da Musabaka.
Yanayin yadda labarin ya riske ni shi ne cewa ga shi an turo da sanarwa cewa duk mai sha’awa a Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano a karkashin Kwamishina Sama’ila Shu’aibu Dikko, Allah Ya kara masa jagora ta shirya Musabaka ga ’yan sanda domin karfafa musu gwiwa da sanya musu ruhi na addini.
To a wannan lokaci mutane da yawa sun nuna sha’awarsu ni ma na nuna sha’awar cewa zan shiga.
Daga nan sai aka turo mana cewa ranar 17 da 18 za a yi wanda kuma na shirya na zo.
To kasancewar aikin dan sanda aiki ne da yake bukatar lokaci sosai sannan haddar Alkur’ani ma tana bukatar lokaci, yaya ka iya hada wadannan abubuwa biyu?
Wato karatun Alkur’ani tun da kananun shekaru aka fara don na yi haddar farko ina da shekara 13, saboda haka ya zama jiki.
Wani lokacin ma idan ba a yi ba sai ka ga an shiga cikin damuwa da takura, ni dai haka nake.
To ya kasance a duk yanayin da nake babu wani yanayi ko tafiya da ke hana ni karatu.
Na ma fi jin dadin yin karatu in zan yi tafiya, to ina yin tilawata a hanya saboda akasarin karatuna tilawa ce.
Kuma ko lokacin da muka samu aiki muka tafi Legas za mu karbi horo na farko na shiga aikin dan sanda, to na ci gaba da karatuna tare da karbar horon kafin ma a zo fagen aiki ke nan.
Saboda za ka ga wasu aikace-aikace na horon duk guje-guje ne da tsayuwa.
Duk a tsakanin nan, duk gabar da na samu to zan yi tilawa tunda in ka saba da tilawa duk inda ka yi minti 11 zuwa 12 za ka yi Izu.
To ka ga duk inda ka samu cikakken awa daya za ka samu Izu biyar.
Yanzu haka tunda na yi aiki a bangarori daban-daban, na yi DCO na yi ATO na zauna kuma a Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (CID) da sauransu, to, duk a wadannan aikace-aikacen da na yi babu wanda ya hana ni karatu.
Duk damar da na samu ta shiru, to, zan samu in rage.
A tsarina, mafi yawanci ina son yin karatu bayan Sallar Asuba in kuma abin ya ta’azzara to duk sa’ar da na samu lokaci zan yi. Da na samu wata ’yar gabar shiru ta minti 30 ko 40, to zan yi tilawata.
A tsaka-tsaki, ka kan yi tilawar Izu nawa a rana?
An dauki shekaru da dama duk mako nakan yi sauka.
Tsari ne na yi, wanda duk mako nake sauka to an dauki shekaru da dama ana yi, sai idan abubuwa sun taso sun yi yawa wani lokacin akan dan samu ya wuce haka.
Ranar da aka ayyana ka a matsayin zakaran gasar yaya ka ji a ranka?
Wato abin ya zo min ba-zata tsakani da Allah, tunda ni na je a matsayin in yi musharaka ce in ba da tawa gudunmawar tunda abu ne na addini, shi ya sa ma da na zo ban ma shiga rumfar da aka saka ta ’yan takara ba, cikin ’yan kallo na je na zauna.
Da aka kira ni na je na yi karatu, da aka sanar ni ne na zo na daya abin ya zo min da ba-zata kwarai da gaske.
Ba ka yi tunanin za ka lashe ba ma ke nan?
A’a, ban yi tunani ba gaskiya saboda akwai wadanda suka shiga kuma suna da karatu kwarai da gaske.
Wace shawara kake da ita ga matasa da abokan aikinka a bangaren karatun Alkur’ani da suke yi suna bari aikinsu na dauke musu hankali?
Duk Musulmi ba sai dan sanda ba, duk aikin da mutum yake yi a duk inda ka tsinci kansa, ya zamo cewa abubuwa guda biyu bai rabu da su ba.
Na farko koyon karatun. Yaya za ka yi ibada yaya za ka yi Sallah da azumi da sauransu? Yaya za ka sauke hakkin Allah, yaya za ka sauke hakkin ’yan uwanka, makwabta da sauransu.
Gefe guda kuma shi Alkur’ani shi ne littafin da Musulmi ke tinkaho da shi, wanda kuma babu wata ibada da ke da tarin lada irin karatun Alkur’ani.
Don Hadisi ya zo wanda Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya karanta harafi daya yana da lada 10, to ko da mutum bai haddace ba, ya zamo ya samar wa kansa wani lokacin da zai rika nazarin iya abin da ya sani kada ya bari ya kubce masa tunda da wuya ka samu wanda bai iya wani adadi na Alkur’ani ba.
Mutum ya lizimta wa kansa cewa sai ya yi karatun Alkur’ani sannan ya rika kwadayin sauraron Tafsiri na malamai don ya rika gane abin da yake karantawa.
Domin Alkur’anin ya yi wa mutum tasiri ya zamo a gan shi a aiki kuma a gan shi a mu’amularsa, kamar yadda za a gan shi kuma yana karanta shi.
Mece ce babbar ribarka daga wannan musabakar?
Babbar ribata a zahirin gaskiya ba ma ta lashe gasar kawai ba ce, ko ta samun kyauta.
Sai ta yadda labarina ya taka rawa wajen sauya tunanin mutane da dama cewa akwai mutanen kirki, masu ilimin addini a cikin ’yan sanda.
Don akwai wasu labarai har na mutum uku da na samu na wadansu da iyayensu suka hana shiga aikin dan sanda, wai don kada su lalace.
Akwai wata mata ma da ta sha alwashin in dai tana da rai, wani a zuriyarta ba zai yi aikin dan sanda ko alkalanci ba.
Amma cikin ikon Allah jin cewa ga shi har an samu mahaddata a ciki, ya sauya tunaninta sosai.
Yanzu haka maganar da ake har ta amince danta ya tafi. Wannan ni a wurina ita ce babbar ribar.