Ladanin masallacin Madina ya rasu
Hukumomi a Saudiyya sun ce Sheikh Faisal Nouman ya rasu a birnin Madina ranar Laraba bayan fama da jinya
Allah Ya yi wa Ladanin Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Faisal Nouman rasuwa.
Hukumomi a Saudiyya sun ce Sheikh Faisal Nouman ya rasu a birnin Madina ranar Laraba bayan fama da jinya.
- Kirsimeti: Ina yin kira ga yin ƙauna da haɗin kai — Shugaban CAN
- Zulum ya yi Allah wadai da harin ƙunar baƙin wake a masallaci
An dai naɗa Sheikh Faisal a matsayin ladanin masallacin a shekarar 2002, kuma ya gaji kakansa da mahaifinsa a wannan aiki kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito.