Ladubban Idda

A yau zamu yi amfani da Labarin Uwargida Najiya don bayyanar da ladubban idda, watau yadda ya kamata matar da aka saki ta yi zaman kwanakin iddarta; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.Bayan Shehun Malami Ragib Ya saki matarsa Najiya, sai yace da […]

Ladubban Idda
Ladubban Idda

A yau zamu yi amfani da Labarin Uwargida Najiya don bayyanar da ladubban idda, watau yadda ya kamata matar da aka saki ta yi zaman kwanakin iddarta; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.
Bayan Shehun Malami Ragib Ya saki matarsa Najiya, sai yace da ita “tafi gidan iyayenki.” Sai tace “ba zan tafi gidan iyayena ba kuma ba zan bar gidan nan ba sai dai in an tursasa ni ne.” Yace da ita “na sake ki kuma bani da bukata dake don haka ki bar min gidana. “Ta ce da shi “ba zan tafi ba, kuma bai halatta ka sani in tafi ba har sai na gama idda kuma sai ka biyani kyautar sakina.”   “Ai wannan karfin hali ne da rashin kunya da sakarci!”
Ta ce da shi ai ban kai Allah ba shi da ya ce: “Ya kai Annabi! Idan kun saki mata, sai ku sake su ga iddarsu kuma ku kididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da takwa, kada ku fitar da su daga gidajensu kuma kada su fita face idan suna zuwa da wata alfasha bayyananna. Kuma wadancan iyakokin Allah ne. Kuma wanda ya ketare iyakokin Allah, to lallai ya zalunci kansa. Baka sani ba, tsammanin Allah zai fitar da wani al’amari a bayan haka.(Suratul Talak Aya ta 1).  Sai ya sabi rigarsa ya barta yana gunaguni.
Ita kuwa sai dai ta yi lallausan murmushi ta cigaba da harkokin gabanta kamar ba abinda ya faru.
Kullum za ta kunna turaren wuta gidan ya yi ta kamshi, ta ci kwalliya ta fesa turare mai tsananin kamshi sannan ta zauna a wurin da zai ganta lokacin shigowa da fitarsa daga gidan. Bai iya dauriyar da ta wuce kwana biyar ba ya mayar da ita a aikace ba a magance ba.
Wata rana ta makara wajen hada masa kayan karin kumallon safe, sai ya ce da ita a harzuke: “Wannan daya daga cikin nakasunki ke nan game da hakkokina, kuma wannan ba dabi’ar matan kirki ba ne!”
Sai ta ce da shi “Ka yi wa dan uwanka Musulmi kyakykyawan zato sau saba’in. Kuma yin kyakykyawan zato ga mutane yana daga cikin kyawawan dabi’u; kuma yana sa sanyin zuciya kuma yana inganta addinin mutum. Kuma duk mutumin da yake wa mutane kyakykyawan zato to zai mallaki soyayyarsu.”
Ya ce da ita “abinda kika fada ba zai kawar da sakacinki ba! Yanzu dadinki ne in fita ban karya ba?”
Ta ce da shi “daga cikin kyawawan dabi’un Musulmi nagari shi ne samun kwanciyar hankali ga abinda Allah Ya ba shi komin kankantarshi. Kuma Annabi Sallallahu Alayhi wa Sallam ya fada cewa ‘lallai mafi nasarar mutane shi ne wanda ya riki Musulunci a matsayin arzikinsa kuma Allah Ya ba shi wadatar zuci game da abinda ya mallaka masa.’” Sai yace “ba zan ci abincin ba!”  Sai tade da shi “baka fahimci darasin ba ke nan.”
Shehun Malami Ragib bai kara fuskantarta ba, kuma ya fita ya bar gidan a fusace. Kuma ya ki cewa da ita komi bayan ya dawo. Da dare ya kaurace wa gadonta ya kwanta a kasa. Wannan ya cigaba har kwana goma.
Uwargida Najiya ta kasance za ta dafa masa abinci da abin sha kuma ta yi dukkan ayyukanta na kula da gida kamar yadda ta saba a yini. Da daddare sai ta cire rigar kunya, ta ci kwalliya ta sa turare ta kwanta a gadonta sai dai kawai ba ta ce masa komai sai in maganar ta dole ce.
A rana ta 11, har ya kwanta a kasa sai ya koma bisa gadon. Ta yi dariya ta ce “Me ya sa kaz o?” Ya ce “Faduwa na yi!”
Tace da shi “ai faduwa daga sama zuwa kasa ne ba daga kasa zuwa sama ba.”
“Ai akwai wani maganadisu mai karfi a saman gadon nan da ya fi karfin maganadisun duniyar duka!” Ya fada cikin murmushi.
Cike da jin dadi ya cigaba da cewa “Inda a ce duk mata kamarki suke da ba namijin da zai saki matarsa kuma dukkan matsalolin auratayya za su kau. Kuma Manzon Allah Sallallahu alayhi wa sallam Ya yi gaskiya inda ya ce: Duk macen da ta yi hakuri da cutarwar mijinta, Allah Zai ba ta lada kwatankwacin ladar Asiyah diyar Mazahim. Lallai kin taimake ni wajen yin biyayya ga dokokin Allah Yake Najiya, Allah Ya biyaki, kuma Allah Ya sa ba za mu taba rabuwa ba!
Wannan shi ne yadda hakuri ya ci nasara akan fushi. Ko kun san cewa Najiya na nan a cikin kowace mace? Duk matar da take maida kaimi ga bauta wa Ubangijinta ita ce Najiya. Tana kokarin tsere wa kaskantacciyar duniya don ta samu kololuwar Aljannah mafi daraja. Allah Ya tserar da mu daga wuta.
dan uwa Ridwan Ibrahim ne Ya fassara daga Larabci zuwa turanci; Duniyar Ma’aurata ne suka fassara zuwa harshen Hausa. Mun samo wannan labari daga yanar gizo.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe amin.