Ladubban mahajjaci kafin barin kasarsa

Idan Musulmi ya yi nufin tafiya zuwa Hajji ko Umra anso da ya yi wa iyalansa da abokansa nasiha da tsoron Allah, ma’ana ya yi musu nasiha da aikata abin da Allah ya umurce su da aikatawa, Ya kuma hanesu da kauce wa abin da Allah Ya yi hani akansa. Kuma mutum ya rubuta duk […]

Ladubban mahajjaci kafin barin kasarsa
Ladubban mahajjaci kafin barin kasarsa

Idan Musulmi ya yi nufin tafiya zuwa Hajji ko Umra anso da ya yi wa iyalansa da abokansa nasiha da tsoron Allah, ma’ana ya yi musu nasiha da aikata abin da Allah ya umurce su da aikatawa, Ya kuma hanesu da kauce wa abin da Allah Ya yi hani akansa. Kuma mutum ya rubuta duk abin da yake bin bashi, da wanda ake binsa, kuma mutum ya nemi shaidu akan hakan. Dole ya gaggauta tuba daga dukkan zunubi. Wadannan su ne ladubban da maniyyaci, mahajjaci ya kamata ya lizumta kafin tafiyarsa zuwa kasa mai tsarki don sauke farali.
Kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce. “Kutuba zuwa ga Allah baki daya yaku muminai domin ku samu rabo.”                 
Sharuddan tuba kuwa su ne: yin da na sani (nadama) a bisa abin da ya gabata na Zunubi, da niyyar rashin komawa ga zunubin. Kuma in ya zamana akwai hakkin mutane a kansa, kamar zalunce-zalunce na dukiya ko mutunci, to sai ya mai dawa mai hakki hakkinsa, ko ya Nemi su da su  hallata masa hakkin su.
 Manzon Allah (S.A.W) ya fada a cikin wani hadisi mai tsawo cewa:-
Idan mutum ya fita da niyar Hajji da guzuri na halal yana sanya kafarsa cikin likkafa, idan ya yi kira ya ce ubangiji na amsa kiran ka ka amsa mini, wani mai kira zai yi kiransa daga sama ya ce, ‘an amsa maka,’ guzurin ka na halal ne, abar hawanka na halal ne don haka Hajjin ka karbabbe ne, ba a bin ki ba ne.  Idan mutum ya tafi da kudi wadanda ba na halal ba idan ya sanya kafarsa cikin likafa Idan ya yi kira ya ce, Ubangiji na amsa kiranka ka amsa mini, sai mai kira ya yi kira daga sama ya ce, ba a amsa maka ba, guzurin ka na haramun ne kuma abincin ka na haramun ne kuma hajjinka ba karbabbe ba ne.
Kuma wanda ya yi niyyar hajji, ya kamata ya abbokanta da mutanen kirki na kwarai kuma ya zauna da masu tsoron Allah masana shari’ar Allah, ya ki ya yi tafiya da jahilai ko fasikai, kuma ya nemi sani game da abin da ya shafi Hajji da Umra, kuma ya rika tambaya akan abin da ya riki ce masa, domin ya samu basira.
Idan mutum ya dauki harama, ya kamata ya yawaita ambaton Allah da salati ga manzon Allah (S.A.W) kuma ya kame bakinsa daga karya da zumde da rada da anamimanci da cin zarafin ‘yan uwansa musulmai.
Bayan aikin hajji me ya rage? Kasani ya kai Alhaji dan uwana a Musulunci wanda ya yi Hajji da Umra, yana mai nufin Allah da su; ya kamata ka bude wani sabon shafi a rayuwar ka tsakanin ka da Allah akan tsoronsa. Wannan shi ke nuni da cewa Allah ya karbi Hajjin ka da Umrar ka, don haka ba a tsammanin zunuban ka da aka shafe a ka karkare saboda alfarmar Hajji da umra, ka koma ga abin da ka aikata a baya na sabo, a’a ya kamata ka tsarkake zuciyar ka da raya ta a bisa tauhidi, da tsarkake bautar Allah da tuba zuwa gareshi daga kowane zunubi da sabo, kada ka koma zuwa ga zaluntar mutane ko keta dokokin Allah (S.W.T).
[email protected] 08063673656

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50