Ladubban neman aure
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Wannan fili ya samu karin tambayoyi game hanyoyin da ya kamata mai niyyar yin aure ya bi don samun dacewa da nasara cikin neman auren da kuma bayansa. […]
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Wannan fili ya samu karin tambayoyi game hanyoyin da ya kamata mai niyyar yin aure ya bi don samun dacewa da nasara cikin neman auren da kuma bayansa. To ga sabunta bayani kan ladubban neman aure ga maza da mata da kuma iyaye; sannan daga baya za mu amsa sababbin tambayoyin da masu karatu suka aiko:
Ladabi na 1: Kulla Niyya:
Kamar yadda muka sani daga koyarwar Manzon Allah (SAW), cewa dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, kuma mutum yana samun abin da ya yi niyya dominsa; don haka don samun alheri, sai mutum ya kudurta alheri yayin kulla niyyarsa ta yin aure. Sai ya kudurta a zuciyarsa cewa zai yi aure ne musamman saboda Allah da kuma more ni’imar da Allah Ya sa cikin aure da raya Sunnar Annabinmu (SAW) da fatar samun zuriyya dayyiba. Da sauran niyyoyi na alheri da suka dace da yanayin rayuwar mutum da bukatunsa.
Ladabi na Biyu: Tsananta Addu’a:
Bayan kulla kyakykyawar niyyar yin aure cikin zuciyar mutum, to sai ya bi bayan wannan niyya tasa da tsananta addu’a da kara dagewa wajen tsayar da addininsa da yin abubuwan karuwar imani a zuciya, kamar yawan yin azumin nafila a-kai-a kai, sallolin nafila a sulusin karshe na dare, yawan yin sadaka, karin kyautatawa ga iyaye da ’yan uwa makusanta da makwabta. Yawan yin Sallar Neman Zabin Allah (Sallar Istikhara) da dagewa wajen guje wa aikata ayyukan sabo, manya da kuma kanana irin wadanda aka raina da guje wa cin haram da yawaita tasbihi da istigifari da raya zuciya da yawan tunanin Allah Madaukakin Sarki da yawan gode maSa. Sannan a sanar da iyaye da ’yan uwa makusanta cewa su taya mutum da addu’a kan wata matsananciyar bukata wajen Allah. Haka abokin arziki ko wani mutumin kirki da aka sani, ana iya neman taimakonsa, don dai a dace da nasara ta kowace fuska cikin yardar Allah.
Ladabi na 3: Neman Zabin Allah Madaukaki: Yana da matukar alfanu ga Musulmi ya kasance idan ya tashi zartar da wani abu sabo a cikin harkokin rayuwarsa, ya sanar da Ubangijinsa, ya nemi zabi da shiriyar yadda zai gabatar da abin daga wajen Allah Mabuwayi Mai Hikima.
Aure babban al’amari ne mai bukatar tanadi da shiri mai kyau don tabbatuwar nasararsa. Don haka ba tanadin da ya kai neman taimakon Allah Azza Wa Jalla a kowane bangare na nema da zabar mata ko mijin aure. Don haka sai mutum mai niyyar aure ya jibanci yin Istikhara a duk lokacin da wani abu ya taso da ya shafi yunkurinsa na samun mata ko mijin aure. Wato lokacin kulla niyya a yi Istikhara, lokacin da aka ga wata da ta cancanta a nema da aure a yi Istikhara, zuwa neman izini a yi Istikhara, zuwa hirar farko a yi Istikhara, da haka dai har a kai ga daurin aure.
Ladabi na 4: Fahimtar bukatun rai yayin neman abokin aure: Yana da kyau ga mai niyyar yin aure ya binciki kansa a wannan lokaci, ya san bukatun ransa da abubuwan da ya fi bai wa muhimmanci a rayuwarsa; ya kuma san inda yake da rauni da inda yake da karfi, ya san abubuwan da ransa zai iya dauka da wadanda ba zai iya dauka ba. Sanin wadannan abubuwa za su taimaka masa sosai wajen zabar abokiyar zamar da ta dace da halayyarsa da dabi’unsa da kuma yanayin bukatun ransa. Domin aure abu ne mai matukar muhimmanci kuma mai cike da sammatsi da yawa; abu ne da ya kamata a tattara dukkan hankali da natsuwa kafin yin sa, don a tabbatar da cewa an yi kokarin kawar da duk wani abu da ka iya haifar da matsala bayan an yi auren.
Ladabi Na 5: Neman wacce za a nema da sure: Bin ’yan matan unguwa da kallo yayin da suke wucewa ba ita ce ingantacciyar hanyar neman wadda za a aura ba, shi irin wannan kallo ma in ya wuce kallo daya ya zama sabon Allah. Hakan nan yawan zuwa hira wajen ’yan mata daban-daban, sannan daga karshe a zabi wata a nema da aure shi ma gurbatacciyar hanya ce ta neman matar aure. Haka nan tara samari wani sa’in har suna layi a kofar gida, ko hirar zamani da ake yi har cikin motar saurayi ko kuma a tafi yawo da shi, cin ado da sa matsattsun kaya da fesa turare don maza su gani su dasa wadannan duk gurbatattun hanyoyin zabin abokin aure ne. Ingantacciyar hanya da ta dace da koyarwar Musulunci sai a biyo mu mako mai zuwa insha Allah.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin