Ladubban neman aure (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman aure daga inda muka kwana a makon jiya: Hanyoyin kulla saduwar farko: A al’adance ta wadannan hanyoyi ne ake […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman aure daga inda muka kwana a makon jiya:
Hanyoyin kulla saduwar farko:
A al’adance ta wadannan hanyoyi ne ake kulla saduwar farko tsakanin maniyyata aure:
- Ganin ido: Shi ne lokacin da maniyyacin aure ya ga wata baiwar Allah, har wani abu daga gare ta ya burge shi ya ji ya dace ya neme ta da aure. Mafi yawan saduwar farko na a cikin al’ummar Hausawa na faruwa ne ta wannan kafa amma kuma cike take da hadari ga Musulmin kwarai musamman wanda ya ba da muhimmanci ga abin da za a rubuta masa a littafin ayyukansa na lada ko zunubi, da kuma mai kai-kawo da Ranar Hisabi. Allah Madaukakin Sarki Ya yi kira da su runtse idanunsu daga kallon matan da ba muharramansu ba sannan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana kallo na farko ba laifi a ciki amma na biyu za a tuhumi bawa game da shi. Don haka sai a kiyaye lallai kallon nan kada ya wuce na farkon, da an gani dole a yi aiki da umarnin Allah Madaukakin Sarki a kawar da kai kada a yi na biyu ko a yi kallo ba kakkautawa.
- Sanayya: Ko ya kasance maniyyacin aure ya san wata baiwar Allah a dalilin zumunci, makwabtaka ko wani dalili makamancin haka, sannan ya yaba da hankali da tarbiyyarta.
- Ko maniyyacin aure ya ji labarin wata baiwar Allah kuma abubuwan da ya ji suka burge shi har ya ji ya kamata ya nemi aurenta.
- Ko kuma maniyyacin aure ya sa a bincika masa irin matar da yake ganin ya dace ya aura, ta hanyar iyaye, ’yan uwa da abokan arziki.
Ladabi na 5: Zabar macen da ta dace: Aure wani abu ne da ake kulla shi don samun natsuwa, farin ciki da annashuwar zuciya ga ma’aurata da kuma samar da kyakykyawar zuriyya wacce za ta samar da ingantacciyar al’umma. Kamar yadda Allah (SWT) Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma: “Kuma akwai daga cikin ayoyinSa Ya halitta muku matan aure daga kawunanku, domin ku natsu zuwa gare su, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani.’ (Suratu Rum aya ta 21).
Don samun dacewa da irin wannan natsuwar zuciyar, dole sai ma’aurata sun zabi miji ko matar da ta fi dacewa da su ta kowane fannin rayuwar duniya. Kuma Manzon Allah (SAW) ya yi umarni ga maniyyacin aure cewa ya sa kula sosai wajen zabar mace domin irinsa (zuriyyarsa), kuma ya ce mutum ya auri mafi dacewa (daga mata) kuma ya aurar (da ’ya’yansa) ga mafi dacewa.
Maniyyacin aure zai dubi dacewar matar da zai aura ta fuskoki uku: Ta fuskar addini, ta fuskar yanayin bukatar ransa da kuma dacewarta da yanayin zamantakewar danginsa. Ga bayaninsu daya bayan daya:
Dacewa ta fuskar addini: In muka bibiyi koyarwar Addinin Musulunci Madaukaki, za mu ga cewa siffofi uku ne suka dace maniyyacin aure ya yi la’akari da su lokacin zabar matar da zai aura. Na farkonsu, kuma mafi muhimmancinsu shi ne riko da addini, sai iya mu’amalar soyayyar aure, na ukunsu shi ne macen ta kasance mai haihuwa ce.
Riko da addini: A cikin wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya yi kyakykyawan bayani kan irin macen da ta dace a nema da aure; inda ya ce:
“Ana auren mace saboda abubuwa hudu: arzikinta, asalinta (dangantakarta), kyawunta ko addininta. Na hore ku da auren mai addini, in ba haka ba kuwa za ku tabe.”
A wani kaulin kuma ya ce “Na hore ku da auren mai addini sai ku samu natsuwa…”
Daga wannan umarni na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), za mu fahimci cewa, mace mai riko da addini, ita kadai ce macen da ta fi dacewa a nema da aure, ita kadai kuma ya halatta a aura! Musamman in muka yi la’akari da kalaman karshe na cikin wannan Hadisi wanda gargadi ne da fadakarwa mai karfi da hadarin da ke tattare da auren mace mara riko da addini.
Sannan a wani Hadisi daban Annabi (SAW) ya siffanta salihar mace da cewa ita ce mafi kyawun abin da dan Adam zai mallaka a duniya. Don haka duk wanda ya nemi auren mace mara riko da addini, to ya juya baya ne ga wannan umarni na Annabinmu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Kuma wannan ya nuna shi ma yana da nakasu wajen riko da addini, kuma ba ya kishin addini kuma ba ya kwadayin a haifa masa zuriyya masu riko da addini. Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma:
“Miyagun mata domin miyagun maza suke. Kuma miyagun maza domin miyagun mata suke. Kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke, kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke…” (Suratun Nur, aya ta 26).
Wani abu kuma mai kyau game da wannan ingantaccen Hadisi shi ne da a ce dukkan Musulmi za su yi aiki da shi, su wanzar da shi cikin rayuwarsu, to da ya gyara da kuma tsarkake al’umma gaba daya; domin in duk namijin da ya tashi aure zai nemi mai riko da addini ya aura, to da kowace mace ta dage da rikon addininta don samun mijin aure. Wannan shi zai sa yaran da za a rika haifa a cikin al’umma su zama nagartattu masu tarbiyya domin iyayensu sun kasance masu riko da addini.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.