Ladubban neman aure (4)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaven macen da ta dace; da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu […]

Ladubban neman aure (4)
Ladubban neman aure (4)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaven macen da ta dace; da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Siffofin mai rikon addini, ci gaba…

  1. Kiyaye Dokokin Allah Madaukaki: Mace mai riko da addini za ta kasance ta siffantu da riko da addini ta hanyar kiyaye dokokin Allah (SWT) gaba daya, kananansu da manyansu. Duk wani hani na Allah Mabuwayi Mai hikma, tana kokarin kauce masa a cikin dukkan yanayi, na dadi ko na tsanani; kuma duk wani umarni tana kokarin aiki da shi sau-da- kafa gwargwadon iyawarta. Don haka mace mai riko da addini ta kasance mai yin dukkan ayyukan ibada; mai tsarewa ce wajen yin sallolin farilla a lokutansu, mai yawan azumi, mai sadaka, mai kyauta da kyautatawa kuma mai yin shiga irin ta kamala ta hanyar rufe jikinta kamar yadda Allah Ya umarce ta da sauran kyawawan ibadu da suka wajaba a kan dukkan Musulmi.
  2. Kamun Kai: Mace mai riko da addini ta siffantu da yawan jin kunya da kamun kai, ba ta cakuduwa ta saki jiki da maza ko yin abota da su. Sannan ba ta da yawan yawace-yawace da zuwa wuraren da ba su dace ba.
  3. Hakuri: Wannan wani babban sinadari ne da ake bukatar kowace macen aure ya kasance tana da shi ta yadda bai taba kare mata har karshen rayuwarta. Mace mai riko da addini ta kasance mai yawan hakuri kuma ba ta gajiya a cikin halin yin hakuri domin ta san Allah (SWT) Yana tare da mai hakuri don haka duk wanda ya yi hakuri ba zai tabe ba duniya da Lahira.
  4. Kankan da Kai: Mace mai riko da addini ta kasance mai yawan tawali’u ce kuma ba ta da girman kai; domin ta san cewa matsayi, kyau, dukiya ko ilimi ba su ke nuna daraja da daukakar dan Adam ba. Daraja da daukaka a zuciya suke domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada cikin LittafinsSa Mai girma cewa:

“Mafi darajar cikinku a wajen Allah shi ne wanda ya fi takawa…” Suratul Hujurat, Aya ta 13.

Kuma mace mai riko da addini ta san cewa Annabi (SAW) ya tabbatar mana cewa mai girman kai ba zai shiga Aljanna ba, don haka ba ta siffantuwa da girman kai, takama da nuna isa, kuma ba ta nuna ta fi kowa ta kowace fuska a cikin al’amuran rayuwarta.

  1. Kyakykyawar tarbiyya: Riko da addini bai tabbatuwa ya kafu har ya zama dabi’a dole sai da kyakykyawar tarbiyya. Don haka mace mai riko da addini ita ce wadda aka kawata da kyakkyawar tarbiyya da ke haskaka ta da kara mata daraja a koyaushe.

Abubuwan dubawa wajen nazarin rikon addinin macen da ake neman aurenta

Don samun dacewa ta kowace fuska, yana da matukar alfanu ga mai neman matar aure ya yi nazarin wasu muhimman abubuwa kamar haka:

  1. Da farko sai mai niyyar aure ya yi dubi zuwa ga kansa: Shin shi din ya kasance mai riko da addini? In har ya tabbatar da shi ba mai riko da addini ba ne, to sai ya ajiye neman aure gefe daya ya koma ga kokarin inganta addininsa. Domin duk wata mai riko da addini da zai nema ita ma mai riko da addini take nema, in kuwa ta fahimci bai siffantu da wannan siffa ta riko da addini ba, to zai yi wuya ta amince da aurensa. In kuwa har ya yi nasarar auren mace mai riko da addini, akwai yiwuwar wata rana ya ga ta canja ta koma kamarsa, wato marar riko da addini, don mace kasa take ga mijinta, irin shafin rayuwar da ya son budewa a cikin irinsa za ta rayu. Irin matsayin da ya kai, ta kowace fuska a rayuwa, ita ma irin matsayin za ta bi.
  2. Maniyyacin aure ya sani; mawuyacin abu ne samun mace mai riko da addini dari bisa dari, dole ne in tana da karfi a wani wajen, ya kasance tana da rauni a wani bangaren. Misali za a iya samun mace mai kokarin ibada, mai riko da addini ta kowace fuska, amma kuma ya kasance ba ta da hakuri ko tana da saurin fushi. Ana kuma iya samun mace mai kyakkyawan tauhidi amma kuma a samu rauninta wajen sanya hijabi ko a wani bangare daban. Don haka maniyyacin aure ya yi amfani da kaifin hankali da basirarsa ta da namiji ya auna da kyau; ya zabi wacce inda take da karfi ta fuskar riko da addininta ya dara inda take da rauni; kamar a ce rikonta ya zama kashi 70 cikin 100 rauninta kuma kashi 30 cikin 100 ko wani abu makamancin haka.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.