Ladubban neman aure (7)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma Ya amfanar da su, […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma Ya amfanar da su, amin:
Ladabi Na 6:
Bincike mai zurfi:
Abu mafi muhimmanci da manemin aure zai fara bincika game da matar da yake da niyyar aura shi ne rikon addininta, domin riko da addini na gadar da kyawawan halaye da dabi’u ga mutum. Bayan an tabbatar da rikon addini, sai kuma a zurfafa bincike a san halayya da dabi’unta da yadda take mu’amala da mutane; wato ba fuskarta kadai za a kalla ba, yana da kyau a san me ke bayan fuskar; me ke cikinta; kuma yaya wannan fuskar take a mu’amulance?
Muhimman abubuwan da suka kamata a bincika sun hada da: bincikar ko tana da iyayen kirki masu dattaku; Wadanne irin abokai take tare da su, na kirki ne ko akasin haka; shin ko tana sallolin farilla cikin lokutansu; tana da tsabta da gyara jikinta; tana taimakawa wajen aikin gida da kula da kannenta; ta iya tattali kuma ba ta da almubazzaranci wajen amfani da kayan bukatun rayuwa; ba ta da rainuwa ko raina mutane; ba ta da yawan yawace-yawace; ba ta da yawan cin bashi, (haka kuma mahaifiyarta); bakinta mai tsabta ne, wato ya kasance tana tauna magana kafin ta fade ta, kuma ta iya jera zance, domin babu dadi zama da mace mai kwaba magana duk yadda ta zo mata; tana da sadaukarwa; tana kyauta kuma ba ta da rowa da sauran kyawawan dabi’u da suka yi daidai da yanayi da bukata. Sai maniyyacin aure ya nemi taimakon magabatansa, ’yan uwa da abokai wajen yin irin wannan bincike.
Sannan a bincika shin tana hira da samari? Wadanne irin samarin take hira da su? Duk wanda ya zo ko kuwa ba kowa take kulawa ba? Tana amsar kudi da kyaututtuka daga samarin? Tana shiga motarsu ko su dauke yawo ko su tafi unguwa tare? Tana yin girki ga samarin? Tabbatar da wannan ko akasin haka zai bayyana yanayin kamun kai da tarbiyya na yarinyar da iyayenta da ma zuriyarsu gaba daya.
Sannan a wannan zamani mutum zai iya zurfafa bincike ta kafofin sadarwar zamani musamman Facebook da sauransu. Sai maniyyaci ya binciki yaya take hulda a wadannan kafafe? Tana baza hotunanta kyauta kowa ya kalla ya more? Su wane ne da wane ne take hulda da su a wadannan kafafe, masu kamun kai ne masu sanin ya kamata ko akasin haka? Tana hirar bata lokaci da rashin abin yi? Tana hira da mazan da ba muharramanta ba? Yaya yanayin hirar take? Wadanne irin guruf take ciki da shafukan da take bibiya, na addini ne, masu ilimantarwa ne, masu alfanu da karuwa ne ko akasin haka? Tana bata lokaci sosai a wadannan kafafe? Za a gane haka ne ta hanyar bin diddigin lokacin hawa da saukarta akalla na mako uku. Da sauran dukkan abubuwan da ya kamata a tantance game da wadannan kafafe.
Ladabi na 7: Neman Izinin Iyaye:
Bayan maniyyacin aure ya gama kammala samun dukkan bayanan da suka wajaba game da ingancin macen da yake da niyyar aure, to sai ya sanar da magabata cewa ya ga wance ’yar wane a unguwa kaza, yana son ya nemi aurenta. Sai ya nemi shawara da izinin magabatansa game da wannan niyya tasa su kuma magabatan maniyyaci ya kamata su dan yi nasu binciken, don tattaunawa a tsakaninsu, in ma ta kama su kira taro na dangi don tattaunawa da tuntubar juna kan hanya mafi kyau ta samun nasarar wannan al’amari mai muhimmanci ta kowace fuska. Bayan sun aminta da tarbiyyar yarinyar da nagartar gidan da ta fito, daga nan sai su yi sallama ga iyayenta su nemi izinin dansu ya zo ya gana da ’yarsu, da nufin in sun aminta da juna a tsayar da maganar aure.
A mako na gaba insha Allah, Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.