Ladubban neman aure (8)
Ladabi na 8: Sabunta sanayya In an dace iyayen wadda ake da nufin aure sun aminta, sai maniyyacin aure ya je don su gana. Daga ladubban ganawa shi ne za a zabi wurin zama mafi dacewa a cikin gidan su yarinyar inda za su zauna tare don sabunta sanayya tsakaninsu. Za a yi irin wannan […]
Ladabi na 8:
Sabunta sanayya
In an dace iyayen wadda ake da nufin aure sun aminta, sai maniyyacin aure ya je don su gana. Daga ladubban ganawa shi ne za a zabi wurin zama mafi dacewa a cikin gidan su yarinyar inda za su zauna tare don sabunta sanayya tsakaninsu.
Za a yi irin wannan ganawa ce tare da wani na uku daga cikin muharraman yarinyar, kamar wanta, kanenta, yayarta, kanwarta, kawunta ko gwaggonta su kasance tare da ita kuma su sa ido ga irin hirar da za a yi. Ba wai su juya baya ko su dauke kai daga gare su ba. Maniyyacin aure zai fito cikin shiga ta kamala kuma ya cika zuciyarsa da kyawawan tunani na rokon Allah da fatar Allah Ya tabbatar da alheri a dalilin wannan ganawa mai muhimmanci da za su yi.
Bayan sun yi wa juna sallama, sai su dan yi musayar gaisuwa irin ta al’ada. Sai maniyyacin aure ya gabatar da kansa gare ta sannan ya yi mata bayani game da abin da ya kawo shi; kuma ya nemi jin ra’ayinta. Daga nan in akwai wasu tambayoyi da suke bukatar yi wa juna, don samun karuwar fahimta da kwadaituwa ga auren juna sai su yi wa juna wadannan tambayoyi.
Ana iya maimata wannan ganawa sau biyu zuwa uku in akwai bukatar haka, kamar don warware wasu abubuwa da ba a fahimta ba ko don kara yin kyakkyawan dubi ga ita matar don a tabbatar komai ya yi yadda ake so. Ganawa sau uku ta isa, in mutum na da niyyar aure da gaske sai ya zarce da neman aure, in ita wadda yake nema ta amince; in kuma daya daga cikinsu bai aminta da juna ba; to sai a yanke wannan ganawa kuma take yanke domin amfaninta ya kare; kuma ko da su duka sun aminta da juna to hirar dai karshenta ya zo, sai dai a je ga batun neman aure kuma.
Ba ya daga cikin koyarwar addinin Musulunci yin hira da mace ba tare da neman izinin iyayenta ba; haka ma zuwa hira wajen mace ba da niyyar aure ba, kawai hakan nan kawai don shan bati. Haramun ne kebancewa da mace ana hira ba tare da wani muharraminta a wajen ba. Haka kuma ya saba wa koyarwar Musulunci tsawaita lokaci ana hira har shakuwa ta kullu tsankanin mace da namijin da ba muharraman juna ba. Wannan haramtacciyar shakuwa ita ke bude hanyoyin alfasha da sabon Allah a tsakanin mace da namijin da ba muharraman juna ba. Mu tuna Allah Ya yi kakkausar kira ga Musulmi da “Kada su kusanci zina” da fatar Allah Ya ba mu ikon kiyayewa, amin. Wadannan ayyukan gabatar da haram kafin halal da ke kudundune cikin al’adar neman auren Hausawa shi ke rage albarkar da ke cikin mafi yawan aurarraki saboda an bi son zuciya, an sabi Allah kuma an juya baya ga koyarwar Musulunci to ta ina albarka za ta shiga har ta samu wurin tsayawa? Sai ga ma’auratan da Allah Ya ba su dacewa suka tuba hakikatan daga kura-kuransu na lokacin neman aure da sha’anin biki.
Ladabi na 9: Tsai da magana
In maniyyacin aure ya gana da wadda yake nema, kuma ya gamsu da ganinta, ita kuma ta amince masa da nemanta, to sai ya sanar da magabata su kuma sai su je su gana da magabatanta a tsaida maganar aure. In magabatan yarinyar sun amsa cewa za su aurar da ’yarsu gare shi, sai a sanar da sadaki da kuma ranar da za a taru don daurin aure.
Ba ya daga cikin Sunnar Annabi (SAW) sa ranar daurin aure ta yi nesa da tsayar da magana. Amma ya halatta daura aure a daga ranar tarewa sai can gaba, shi ma kasa a sanya tarewar ta yi nisa sosai sama da shekara biyu. Kuma ya halatta a daura aure take yanke a zaman farko na magabata ba sai an yi ta jan magana ba.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.