Ladubban Neman Matar Aure

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A yau za mu fara bayani kan ladubban neman aure ga maza da mata da kuma iyaye. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga […]

Ladubban Neman Matar Aure
Ladubban Neman Matar Aure

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A yau za mu fara bayani kan ladubban neman aure ga maza da mata da kuma iyaye. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Ladabi Na 1: kulla Niyya:
Kamar yadda muka sani daga koyarwar Manzon Allah SAW cewa, dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, kuma mutum yana samun abin da ya yi niyya dominsa, don haka don samun alheri, sai mutum ya kudurta alheri yayin kulla niyyarsa ta yin aure. Sai ya kudurta a zuciyarsa cewa zai yi aure ne musamman saboda Allah da kuma more ni’imar da Allah Ya sa cikin aure, da raya Sunnar Annabinmu SAW, da niyyar fatan samun zuri’a dayyiba. Da sauran niyyoyi na alheri da suka dace da yanayin rayuwar mutum da bukatunsa.
Ladabi Na Biyu: Tsananta Addu’a
Bayan kulla kyakkyawar niyyar yin aure cikin zuciyar mutum, to sai ya bi bayan niyyarsa da tsananta addu’a da kara dagewa wajen tsayar da addininsa, da yin abubuwan karuwar imani a zuciya, kamar su yawan yin azumin nafila a-kai-a-kai da sallolin nafila a sulusin karshe na dare da yawan yin sadaka da kuma karin kyautata wa iyaye da ’yan uwa da makwabta. Yawan yin sallar neman zabin Allah (watau Sallar Istikhara) da dagewa wajen guje wa aikata ayyukan sabon Allah, musamman kanana irin wadanda aka raina da guje wa cin haram da yawan yin tasbihi da istigfari da raya zuciya da yawan tunanin Allah da Yawan gode masa. Sannan a sanar da iyaye da ’yan uwa makusanta cewa su taya mutum addu’a kan wata matsananciyar bukata wajen Allah. Haka nan ma abokin arziki ko wani mutumin kirki da aka sani, ana iya neman taimakonsa, don a dace da nasara ta kowace fuska cikin yardar Allah SWT.
Ladabi Na 3: Neman Shawarar Allah Madaukaki: Yana da matukar alfanu ga Musulmi ya kasance ko yaushe ya tashi zartar da wani abu sabo a cikin harkokin rayuwarsa, to ya sanar da Ubangijinsa, ya nemi shawarar zabi da shiriyar yadda zai gabatar da abun nan daga wajen Allah. Aure babban al’amari ne mai bukatar tanadi da shiri mai kyau don tabbatuwar nasararsa. Don haka ba tanadin da ya kai neman taimakon Allah a kowane bangare na nema da zabar matar aure. Don haka sai mutum mai niyyar aure ya mu’amulanci yin istikhara a duk lokacin da wani abu ya taso masa da ya shafi yunkurinsa na samun matar aure. Watau lokacin kulla niyya a yi istikhara, lokacin da aka ga wata da ta cancanta a nema da aure a yi istikhara, zuwa neman izini a yi istikhara, zuwa hirar farko a yi istikhara, da haka dai har a kai ga daurin aure.
Ladabi Na 4: Neman Wacce Za a Nema Da Aure: Bin ’yan matan unguwa da kallo yayin da suke wucewa ba ita ce ingantacciyar hanyar neman wadda za a aura ba, shi irin wannan kallo ma in ya wuce kallo daya ya zama sabon Allah. Haka yawan zuwa hira wajen ’yan mata daban-daban, sannan daga karshe a zabi wata a nema da aure shi ma gurbatacciyar hanya ce ta neman matar aure. Ingantacciyar hanya da ta dace da koyarwa addini ita ce ta wadannan hanyoyin:
1. Ganin Ido: Shi ne lokacin da maniyyacin neman matar aure ya ga wata baiwar Allah, har wani abu daga gare ta ya burge shi ya ji ya dace ya neme ta da aure.
2. Sanayya: Ko ya kasance maniyyacin aure ya san wata baiwar Allah a dalilin zumunci, makwabtaka ko wani dalili makamancin haka, sannan kuma ya yaba da hankali da siffarta.
3. Ko maniyyacin aure ya ji labarin wata baiwar Allah kuma abubuwan da ya ji suka burge shi har ya ji ya kamata ya nemi aurenta.
4. Ko kuma maniyyacin aure ya sa a bincika masa irin matar da yake ganin ya dace ya aura, ta hanyar iyaye, ’yan uwa da abokan arziki.
Ladabi na 5: Fahimtar Bukatun Rai yayin neman wacce za a nema da aure: Yana da kyau ga mai niyyar yin aure ya binciki kansa a wannan lokaci, ya san bukatun ransa da abubuwan da ya fi ba muhimmanci a rayuwarsa; ya kuma san inda yake da rauni da kuma inda yake da karfi, ya san abubuwan da ransa zai iya dauka da wadanda ba zai iya dauka ba! Sanin wadannan abubuwan za su taimaka masa sosai wajen zabar abokiyar zamar da ta dace da halayyarsa da dabi’unsa da kuma yanayin bukatuwar ransa. Domin aure abu ne mai matukar muhimmanci kuma mai cike da sammatsi da yawa; abu ne da ya kamata a tattara dukkan hankali da natsuwa kafin yinsa, don a tabbatar da cewa an yi kokarin kawar da duk wani abu da ka iya haifar da matsala bayan an yi auren nan.
Sai mako na gaba sauran bayani na zuwa in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.