Ladubban Neman Matar Aure (3)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaben macen da ta dace. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin. Siffofin Mace Mai Riko Da Addini: 1. Tauhidi: Abu na farko, kuma mafi muhimmanci […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaben macen da ta dace. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Siffofin Mace Mai Riko Da Addini:
1. Tauhidi: Abu na farko, kuma mafi muhimmanci da dukkan wata mace mai riko da addini ya kamata ta siffantu da shi shi ne, kyakkyawan Tauhidi, wanda ya kunshi kadaita Allah wajen bauta da kadaita shi a cikin dukkan harkokin rayuwa na yau da kullum. Da kuma yin addini kamar yadda Annabi SAW tare da Sahabbansa managarta suka yi shi ba tare da yin kari ko ragi ba.
Lallai Tauhidi babban al’amari ne, abin dubawa da yi wa kyakkyawan nazari wajen zabar matar aure. Domin in Tauhidi ya samu rauni, to dukkan bangarorin addini gaba daya za su raunana. In Kuma Tauhidi ya kafu da kyau a cikin zuciya, to zai tabbatar da kafuwar dukkan sauran bangarorin Addini.
Mu fahimci saboda yanayin rauni da ke tattare da halittar ’ya mace, tana saurin samun rauni ta bangaren Tauhidi musamman ta hanyar amince wa wasu ayyuka masu raunata Tauhidi don samun saurin wata matsala ko damuwa da ta taso mata gaba. Don haka sai a binciki yanayin halayya, nisan hankali da juriyar matar da za a nema da aure, da haka ne za a iya fahimtar ko za ta iya riko da tauhidinta komai tsanani, ko kuwa irin wacce da ta ji wata ’yar matsala irin ta halin rayuwa ta matso ta, za ta garzaya wajen boka ko malamin tsibbu da nufin samun warkuwar matsalarta.
Don haka akwai hadari sosai a cikin auren macen da Tauhidinta bai inganta ba, hasalima, Allah SWT Ya fada cikin littafinsa mai tsarki cewa yin hakan haramun ne ga Mu’uminai:
“Mazinaci ba ya aure face mazinaciya ko mushirika, mazinaciya ba mai auren ta face mazinaci ko mushiriki; kuma an haramta wannan a kan Mu’uminai.” Suratun Nur; Aya ta 3.
Don haka dole maniyyacin aure ya dage ga neman mace mai Tauhidi domin wannan alama ce gare shi cewa shi din mai Tauhidi ne kuma ba mushiriki ba ne ba mazinaci ba ne.
2. Kiyaye Dokokin Allah Madaukaki: Mace mai riko da addini za ta kasance ta siffantu da riko da addinin ta hanyar kiyaye Dokokin Allah SWT gaba daya, kananansu da manyansu. Duk wani hani na Allah Mabuwayi mai Hikima, tana kokarin kauce masa a cikin dukkan yanayi: na dadi ko na tsanani; kuma duk wani umarni tana kokarin aiki da shi sau da kafa gwargwadon iyawarta.
Don haka mace mai riko da addini ta kasance mai yin dukkan ayyaukan ibada; mai tsarewa ce wajen yin sallolin farilla cikin lokutansu, mai yawan azumi, mai sadaka mai kyauta da kyautatawa, kuma mai shiga ta kamala ta hanyar rufe jikinta kamar yadda Allah Ya umarce ta, da sauran kyawawan ibadodi da suka wajaba a kan dukkan Musulmi.
3. Kamun Kai: Mace mai riko da addini ta siffantu da yawan jin kunya da kamun kai, ba ta cakuduwa ta saki jiki da maza ko yin abota da su. Sannan ba ta da yawace-yawace da zuwa wuraren da ba su dace ba.
4. Hakuri: Wannan wani babban sinadari ne da ake bukatar kowace macen aure ya kasance tana da shi da yawan gaske, ta yadda bai taba kare mata har karshen rayuwarta ba. Mace mai riko da addini ta kasance mai yawan hakuri kuma bata gajiyawa a cikin halin yin hakuri. Domin ta san cewa Allah SWT yana tare da mai hakuri don haka duk wanda yayi hakuri ba zai tabe ba duniya da lahira.
5. kan-kan da Kai: Mace mai riko da addini ta kasance mai yawan tawali’u ce kuma ba ta da girman kai; domin ta san cewa matsayi, kyau, dukiya ko ilmi ba su ne ke nuna daraja da daukakar dan Adam ba. Daraja da daukaka a zuciya suke domin Allah Ya fada cikin littafinSa mai tsarki cewa:
“Mafi darajar cikinku a wajen Allah shi ne wanda ya fi takawa…” Suratul Hujurat, Aya ta 13.
Kuma mace mai riko da addini ta san cewa Annabi SAW ya tabbatar mana cewa mai girman kai ba zai shiga Aljanna ba. Don haka ba ta siffantuwa da girman kai, takama, nusa isa da kuma nuna ni na fi kowa ta kowace fuska a cikin al’amuran rayuwarta.
6. Kyakkyawar Tarbiyya: Riko da addini bai tabbatuwa ya kafu har ya zama dabi’a, dole sai tare da kyakkyawar tarbiyya. Don haka mace mai riko da addini ita ce wacce aka kawata da kyakkyawar tarbiyya, wacce ke haskaka ta da kara mata daraja a kodayaushe.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.