Ladubban Neman Matar Aure (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. da fata. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin. Abubuwan Dubawa Wajen Nazarin Rikon Addinin Macen Da Ake Neman Aurenta: Don samun dacewa ta kowace fuska, yana […]

Ladubban Neman Matar Aure (4)
Ladubban Neman Matar Aure (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. da fata. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.

Abubuwan Dubawa Wajen Nazarin Rikon Addinin Macen Da Ake Neman Aurenta:

Don samun dacewa ta kowace fuska, yana da matukar alfanu ga mai neman aure ya yi nazarin wadansu muhimman abubuwa kamar haka:
• Da farko sai maniyyacin aure ya duba kansa: Shin shi din ya kasance mai riko da addini? Idan har ya tabbatar da shi ba mai riko da addini ba ne, to sai ya ajiye neman aure gefe daya ya koma ga kokarin inganta addininsa. Domin duk wata mai riko da addinin da zai nema ita ma mai riko da addini take nema, idan kuwa ta fahimci bai siffantu da wannan siffa ta riko da addini ba, to zai yi wuya ta amince da shi. Idan kuwa har ya yi nasarar auren mace mai riko da addini, akwai yiwuwar wata rana ya ga ta canza ta koma kamarsa, watau marar riko da addini, don mace kasa take ga mijinta, irin shafin rayuwar da ya so budewa, to a cikinsa za ta rayu. Irin matsayin da ya kai, ta kowace fuska a rayuwa, ita ma irin matsayin za ta bi.
• Maniyyacin aure ya sani: Mawuyacin abu ne samun mace mai riko da addini dari bisa dari, dole ne idan tana da karfi a wani wajen, ya kasance tana da rauni a wani bangaren. Misali za a iya samun mace mai kokarin ibada, mai riko da addini ta kowace fuska, amma kuma ya kasance ba ta da hakuri ko tana da saurin fushi. Ana kuma iya samun mace mai kyakkyawan Tauhidi amma kuma a samu rauninta wajen sanya hijabi ko a wani bangaren daban. Don haka dai maniyyacin aure sai ya yi amfani da kaifin hankali da basirarsa ta da namiji ya auna da kyau- ya zabi wacce inda take da karfi ta fuskar riko da addininta ya dara inda take da rauni; kamar a ce rikonta ya zama kashi 70 cikin 100 rauninta kuma kashi 30 cikin 100, ko wani abu makamancin haka.
• Mace marar tarbiyya na iya rikidewa ta zamo nagartacciyar mace mai tarbiyya bayan aure. Wannan na iya faruwa ne kadai idan ta kasance mai kyakkyawar zuciya, ta kasance marar tarbiyya kadai, don ba ta samu tarbiyyar ba a gidansu, amma idan ta samu tarbiyya a gidan miji, sai wannan ya sa ta zama nagartacciya. Domin akan samu wasu mata marasa kamun kai, amma aure ya sanya su natsu.
• Kasancewar mace ta fito daga babban gida, ba shi ke nuna tana da tarbiyya ko riko da addini ba, ba kuma shi ke nuna za ta zamo nagartacciyar matar aure ba. Sai dai maniyyacin aure ya auna ya yi nazari ta kowace fuska, ya yi aiki da umarnin Annabi SAW na cewa a nemi mace mai riko da addini, in har ta cika dukkan sharuddan riko da addini, kasancewar ta ’yar babban gida sai ya zama karin ni’ima ke nan, in kuma ba ta cika sharuddan ba, to kasantuwarta ’yar babban gida ba zai yi kyakkyawan tasiri ba.
• Yawan ilmin addini ba shi ke nuna cewa mace mai rikon addini ba ce, da yawa akwai mata masu ilmin addini amma kuma ba su aiki da ilminsu. Wasu ilmin nasu ma shi ke sa su zama masu takama da ji da kai, wanda hakan ke kai su ga aikata kura-kurai da yawa wadanda suka ci karo da siffar riko da addini.
• Kamun kai, natsuwa da yawan jin kunya ba su ke tabbatar da mace mai riko da addini ba ce, domin akan samu mata masu irin wannan siffar, amma can a boye suna aikata wata tabargazar da ta ci karo da siffar riko da addini.
• Hanya mafi sauki ta gane yanayin zamantakewar macen da ake nema da aure shi ne ta hanyar yin bincike da nazarin zamantakewar mahaifiyarta a gidan mahaifinta, ko kuma duk wata macen da ta tashi ta girma a gabanta. Matan da ta girma a gare su, irin yadda suka yi zaman aurensu, ita ma haka za ta yi, sai dai ikon Allah ne kadai na iya sa wa a samu akasin haka. Wannan saboda la’akari da cewa kowane yaro yana dubi ne ga al’adar gidansu ya koyi yadda zai yi tasa rayuwar. Kamar yadda Hausawa kan ce: ‘kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi,’ kuma masana zamantakewa sun tabbatar da hakan cewa, mafi akasarin mutane, yadda iyayensu suka yi rayuwar aure to haka su ma za su yi.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.