Ladubban Neman Matar Aure (6)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin. Ladabi Na 6: Bincike Mai ZurfiAbu mafi muhimmanci da manemin aure zai fara bincike game da matar da yake da […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Ladabi Na 6: Bincike Mai Zurfi
Abu mafi muhimmanci da manemin aure zai fara bincike game da matar da yake da niyyar aure shi ne, rikon addininta, domin riko da addini na gadar da kyawawan halaye da dabi’u ga mutum. Bayan an tabbatar da rikon addini, to sai a zurfafa bincike, a san halayya da dabi’unta da kuma yadda take mu’amula da mutane, wato ba fuskarta kadai za a kalla ba, yana da kyau a san me ke bayan fuskar, me ke cikinta, kuma yaya wannan fuskar take a mu’amulance?
Muhimman abubuwan da ya kamata a bincika sun hada da: bincikar ko tana da iyayen kirki masu dattako, wadanne irin abokai take tare da su, na kirki ne akasin haka, shin tana sallolin farilla cikin lokutansu, tana da tsabta da gyara jikinta, tana taimakawa wajen aikin gida da kula da kannenta, ta iya tattali kuma ba ta da almubazzaranci wajen amfani kayan bukatun rayuwa, ba ta da raina mutane, ba ta da yawan yawace-yawace; ba ta da yawan cin bashi, (haka kuma mahaifiyarta); bakinta mai tsabta ne, wato ya kasance tana tauna magana kafin ta fade ta, kuma ta iya jera zance, domin babu dadi zama da mace mai kwaba magana duk yadda ta zo mata, tana da sadaukarwa, tana da kyauta, kuma ba ta da rowa da sauran kyawawan dabi’u da suka yi dai dai da yanayi da bukatar. Sai maniyyacin aure ya nemi taimakon magabata da ’yan uwa da abokai wajen yin irin wannan binciken.
Ladabi Na 7: Neman Izinin Iyaye:
Bayan maniyyacin aure ya gama kammala samun dukkan bayanan da suka wajaba game da ingancin macen da yake da niyyar aure, to sai ya sanar da magabatansa cewa ya ga wance ’yar wane a unguwa kaza, yana son ya nemi aurenta. Sai ya nemi shawara da izinin magabatansa game da wannan niyya tasa, su kuma magabatan maniyyaci ya kamata su dan yi nasu binciken, bayan sun aminta da tarbiyyar yarinyar da kuma nagartar gidan da ta fito, daga nan sai su yi sallama da iyayenta, su nemi izinin dansu ya zo ya gana da diyarsu, da nufin idan sun aminta da juna a tsayar da maganar aure.
Ladabi Na 8: Sabunta Sanayya
Idan an dace iyayen wacce ake da nufin aure sun aminta, sai maniyyacin aure ya je don su gana, daga ladubban ganawa shi ne, za a zabi wurin zama mafi dacewa a cikin gidansu macen da za a nemi aurenta, inda za su zauna tare don sabunta sanayya tsakaninsu.
Za a yi irin wannan ganawa ne tare da wani na uku daga cikin muharramanta, kamar wanta, kaninta, yayarta, kanwarta, kawunta ko gwaggonta su kasance tare da ida, kuma su sa ido ga irin hirar da za a yi, ba wai su juya baya ko su dauke kai daga gare su ba. Maniyyacin aure zai fito cikin shiga ta kamala, kuma ya cika zuciyarsa da kyawawan tunani na rokon Allah da fatan Allah Ya tabbatar da alheri a dalilin wannan ganawa mai muhimmancin da za su yi.
Bayan sun yi wa juna sallama, sannan sai su dan yi musayar gaisuwa irin ta al’ada. Sai maniyyacin aure ya gabatar da kansa gare ta, sannan ya yi mata bayani game da abin da ya kawo shi; kuma ya nemi jin ra’ayinta. Daga nan in akwai wasu tambayoyi da suke bukatar yi wa juna, don samun karuwar fahimta da kwadaituwa ga auren juna sai su yi wa juna wadannan tambayoyi.
Ana iya maimata wannan ganawa sau biyu zuwa uku idan akwai bukatar hakan, kamar don warware wasu abubuwa da ba a fahimta ba, ko don kara yin kyakkyawan dubi ga ita matar don a tabbatar komai ya yi yadda ake so. Ganawa sau uku ta isa, in mutum na da niyyar aure da gaske sai ya zarce da neman aure idan ita wacce yake nema ta amince; in kuma daya daga cikinsu bai aminta da juna ba, to sai a yanke wannan ganawa, domin amfaninta ya kare, ko da su duka sun aminta da juna to hirar dai karshenta ya zo, sai dai a je ga batun neman aure kuma.
Ba ya daga cikin koyarwa addinin yin hira da mace ba tare da neman izinin iyayenta ba, haka nan ma zuwa hira wajen mace ba da niyyar aure ba, sannan haramun ne kebancewa da mace ana hira ba tare da wani muharraminta a wajen ba. Haka kuma ya saba wa koyarwar Musulunci tsawaita lokaci ana hira har shakuwa ta kullu a tsankanin mace da namijin da ba muharraman juna ba, wannan haramtacciyar shakuwa ita ke bude hanyoyin alfasha da sabo. Da fatan Allah Ya ba mu ikon kiyayewa, amin.
Ladabi Na 9: Tsayar da Magana
Idan maniyyacin aure ya gana da wacce yake nema, kuma ya gamsu da ganin ta, ita kuma ta amince masa, to sai ya sanar da magabatansa, su kuma su je su gana da magabatanta a tsayar da maganar aure. Idan magabatanta sun amince za su aurar da ’yarsu gare shi, sai a yanka sadaki da ranar da za a daura auren. Ba ya daga cikin Sunnar Annabi SAW sa ranar daurin aure ta yi nesa da tsayar da magana. Amma ya halatta daura aure a daga ranar tarewa sai nan gaba, shi ma kada a sanya tarewar ta yi nisa sosai sama da shekara biyu. Kuma ya halatta a daura aure a take a zaman farko na magabata ba sai an yi ta jan magana ba.