Ladubban Warware Husuma Auratayya (2)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, tare da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da ya kunsa. Ga ci gaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance ta; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa […]

Ladubban Warware Husuma Auratayya (2)
Ladubban Warware Husuma Auratayya (2)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, tare da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da ya kunsa. Ga ci gaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance ta; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
2. Bambancin Tunani:
Sinadari na biyu da yake yawan haifar da husuma tsakanin ma’aurata shi ne idan aka samu bambanci mai fadin gaske ga yanayin tunanin ma’aurata musamman a bangaren yanayin zamantakewa da yadda suke cudanyan da junansu. A bayyane yake cewa ba mutum biyun da suke da tunani iri guda a kowane lokaci; kuma akwai bambanci mai fadin gaske tsakanin yanayin tunanin ‘ya mace da da namiji; wannan sai ya haifar da yawan munana zato ga juna tsakanin ma’aurata, mata za ta fadi wata magana, miji sai ya zaci wani abin daban, alhali ita a tunaninta ba haka take nufi ba; ko miji ya yi wani abin, mata ta yi zaton wani abin daban alhali a tunaninsa ba haka yake nufi ba; wannan sai ya haifar da yawan zargin juna da kullatar juna tsakaninsu; wanda inda a ce yanayin tunaninsu iri daya ne, to za su fahimci juna, kuma idan dayansu ya yi wani abu ko ya ce wani abu, zai fahimci maganar a asalinta ba zai yi zargin wani abin na daban ba. Sannan, tunani shi ke taruwa ya gina ra’ayi, don haka da tunani ya bambanta dole a samu bambancin ra’ayi. Bambancin ra’ayi shi ma wani babban sinadari ne da ke saurin ruruta wutar husuma tsakanin ma’aurata.
Magani:
•    Hanya ta farko ita ce ma’aurata su fahimci cewa yanayin tunaninsu ba daya ba ne da na abokin zamansu, kuma duk inda abu biyu mabambantan suka hadu wuri guda dole ne a rika samun akasi; su aje wannan a zuciyarsu ta yadda kodayaushe wata rashin jituwa ta bijiro a tsakaninsu, cikin sauri za su tuno cewa akwai bambancin tunani a tsakaninsu, wannan zai sauya yanayin tunaninsu, su yi kokarin hango abin ta wata mahanga wacce za ta kawo masalaha kuma ta kiyaye aukuwar husuma a cikin auratayyarsu.
•    Hanya ta biyu ita ce ma’aurata su tabbatar da budaddiyar hanyar sadarwa a tsakanin junansu, rashin budaddiyar hanyar sadarwa shi ke haifar da yawan zargi da kullatar juna a tsakanin ma’aurata. Sannan duk lokacin da wata rashin jituwa ta faru, kada a bar ta ta wuce haka nan, ma’aurata su zauna su tattauna su fahimci juna game da wannan matsala, wannan ya ce ni ga yadda na zata, ko ga abin da nake zargi game da kaza, wannan ya ce ni ba haka nake nufi ba, ga yadda nake nufi da sauran makamantan kalamai. Idan ma’aurata suna haka, ba za su rika tara laifin juna cikin zukatansu ba, kuma zai gina kyakykyawar fahimtar juna a tsakaninsu wanda wannan zai zama rigakafin faruwar wata husumar nan gaba a rayuwar aurensu.
•    Duk lokacin da daya daga cikin ma’aurata ya fusata da wani laifi daga abokin aurensa, kafin mayar da martanin wannan laifi, sai ma’aurata su daure, su tsananta tunaninsu kuma su zurfafa shi a kan laifin, su hango abin nan ta wata mahanga daban, su yi wa abokan zamansa uzuri kafin su zarge shi da wannan laifi, wannan zai natsar musu da tunaninsu ya kuma tafiyar da hasalar da ta wanzu cikin zuciyarsu a dalilin wannan laifi.
3. Matsatsin Rayuwa: Sinadari na uku da ke yawan haifar da husuma a tsakanin ma’aurata shi ne halin yau da gobe na rayuwa; wani canji na rayuwa da ya haifar da matsatsi da takurawa ga rayuwar ma’aurata, ko wata mummunar kaddara da ta fado cikin rayuwar aurensu; na iya zama dalilin faruwar hatsaniya wacce idan ma’aurata ba su kiyaye ba sai ta bunkasa ta zama husuma da za a dade a na kai ruwa rana.
Magani:
•    Abin farko shi ne ma’aurata su fara da yin rigakafin kamuwa daga illar da sauyin rayuwa yake kawowa; ta hanyar fahimtar cewa rayuwa ba ta da tabbas, yanayi na iya juyawa kowane lokaci, don haka idan ma’aurata suna cikin jin dadin rayuwa, su sa a ransu cewa Allah na iya jarabtar su da canji a duk lokacin da Ya so; su dage da addu’a Allah Ya dauwamar musu da wannan shafin alherin nan har karshen rayuwarsu; da kuma addu’ar Allah Ya sa duk wata kaddara da za ta fado cikin rayuwar aurensu ta zama sanadiyyar kara kusancinsu ga Allah da kara kusancinsu ga juna ba dalilin nisantarsu da Allah ko nisantarsu da juna ba.
•    Hanya ta biyu ita ce  ma’aurata su tsananta hakuri yayin da suke cikin matsatsin rayuwa, hakuri da juna da kuma hakuri da kaddarar da ta same su. Kada su kasance masu yawan zargin juna ko zargin kawunansu game da wannan kaddara; su fahimci cewa kaddarar nan ba ta isa ta matsanta wa rayuwarsu ba sai sun yi sake; idan sun fuskance ta da kyakykyawar siga da cikakken sakankancewa ga al’amarin Ubangiji; alheri ne zai same su a dalilin wannan kaddara; amma idan suka fuskance ta da siga mara kyau da rashin hakuri. Da fatan Allah Ya tsare mana imaninmu a kowane yanayi na rayuwa, amin.