Ladubban Warware Husuma Auratayya 7
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za bcsu zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance su; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za bcsu zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance su; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Matsalolin Surukkuta, cigaba:
2. Rashin girmama iyayen miji ko na mata ta bangaren Ma’aurata: Duk lokacin da maigida ya raina iyayen matarsa, bai ba su girmamawa da darajtawar da yakamata, wannan dole ya haifar da matsala tsakninsa da uwargidansa, zai haifar da wani bakin sofane akan kaunar da take masa kuma zai sa kimarsa ta rage a idanuwanta; wata ma ba za ta iya daurewa ba har sai hakan ya zama dalilin fadace-fadacen da zai iya kai wa ga mutuwar aure. Haka nan raini ga iyayen miji da rashin girmamasu, darajtasu da yi masu cikakken ladabi da biyayya na haifar da babbar matsala tsakanin ma’aurata wacce in har bata haifar da mutuwar auren ba za ai ta zaman tsami da yawan cece-kuce tsakanin ma’aurata.
Magani: Tabbas yana daga cikin hakkokin aure ga ma’aurata da su girmama iyayen junansu, bai halatta ga daya ya wulakanta iyayen daya a bisa kowane irin dalili ne ma. Don haka dole maigida ya kasance mai girmawa da darajtawa ga iyayen matarsa kamar yadda zai so ita ma ta girmama nasa iyayen. Kulawa da su ta hanyar sada zumunci da yi masu jaje da taya su murna in sun kama da duk wani kyawawan ayyukan da zsu sadar da karamci da kyautatawa ga surukkai. Wannan zai habaka kaunar maigida a zuciyar matarsa zai kuma daga darajarsa da kimarsa a kwayar idonta.
Yana daga cikin alamar kaunar uwargida ga maigidanta ta kaunaci iyayensa; yana kuma daga cikin alamar girmamawarta gareshi ta girmama iyayenshi; sannan yana da cikin siffofin salihar mace darajjatawa, karramawa da kuma kyautatawa ga iyayen mijinta a cikin dukkan al’amura. Uwargida tayi tuni da girman ladar da ke cikin girmama iyaye da girman zunubin saba masu, tabbas duk wanda yayi rayuwa yana girmama iyayensa ya dace duniya da lahira kuma duk wanda ya rayu yana saba ma iyayensa ya tabe duniya da lahira, don haka sai uwargida ta dage kuma ta daure wajen taya maigida girmama iyayensa da karramasu; ta hanyar ita kanta ta runka yawan girmamasu da karramasu da yin hakuri da duk wata mishkila da ta bullo daga garesu, da kara ma maigida kwarin gwiywa da goyon baya wajen yin ladabi da biyayya garesu, da sauke dukkanin hakkokinsu da ya rataya akansa, da karramasu, jiji dasu da kokarin faranta masu a koda yaushe. In kika yi ma maigidanki haka, tabbas kamar kin saka shi a cikin wani jirgine wanda ba inda zai dire da shi sai gidan aljanna; wannan kuwa itace sahihiya, mafi kololuwar kaunar da zaki nuna ma mijinki. Da fatan Allah Yasa mu dace da rahamarsa, amin.
3. Yawan yada jita jita: Yada jita-jita tsakanin uwargida da surukanta na daga manyan abubuwan da ke haifar da yawan rikice-rikice tsakanin uwargida da surukanta. Domin yawan maganganun, ko abubuwan da ke zama musabbabin faruwar husumar ba a ganin idon surukkan ko uwargidan suka faru, ‘yan gulma da ‘yan jita-jita ne suka yada maganar har ta iso kunnen daya daga cikinsu.
Magani: domin tabbatar zaman lafiyar iyali duka, ya zama dole ga suruka da surukkai, miji da mata, duka kowa ya toshe kunnensa daga sauraren irin wadannan maganganun, musamman in ba masu muhimmanci bane, in kuma masu muhimmanci, a fara da danne fushi tukunna, sannan a nemi jin ba’asin abin cikin kyakykyawar siga ta yadda bin ba’asin ba zai dagular da al’amura ba kuma. Duk Musulmin kirki kamata yayi in yaji wani mummunan zance game da dan’uwansa ya kyautata masa zatto, ya karyata abin take yanke har sai hujja bayyananniya ta tabbatar masa da gaskiyar al’amarin. Kuma kullum mutum ya kasance mai zabar hanyar sulhu da maslaha sama da hanyar rikici da fadace-fadace. Su kuma masu yada jita-jita su gane cewa abinda suke aikatawa suna cutas da kawunansu ne sama da kowa da al’amarin ya shafa, domin nauyin zunubin nan yana nan akansu, duhun zunubin yana nan ya launace zuciyarsu, sannan alhakin wadanda suka zalunta da gulmarsu yana nan yana jiran sakayya; don haka ko domin kawunansu ba domin kowa ba sai su dage suyi yaki da wannan muguwar dabi’a ta yada jita-jita musammam wacce ke haifar da rashin zaman lafiya tsakanin mace da mijinta ko tsakanin mutum da iyayensa.
Da fatan Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.