Ladubban Warware Husuma Auratayya (8)
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Matsalolin Surukkuta, cigaba…
3. Rashin tsayuwa da adalci ta bangaren Maigida: Karkatar da kulawa ga bangare daya kadai da wasu Magidanta ke yi na daga cikin abubuwan da ke haifar da yawan husuma da fadace-fadace a cikin rayuwar ma’aurata. In magidanci ya karkatar ga iyayensa kadai, ta yadda lokaci, kulawa da soyayyar da yake basu ta wuce ka’ida har baya samun lokaci da kulawar da zai bayar ga matarsa; wannan dole ya haifar da matsala tsakaninsa da matarsa, domin tana da nauyin wadannan hakkokin akansa itama. Haka kuma in maigida ya karkata kacokan ga matarsa ta yadda bai da lokacin kulawa da iyayensa kuma bai sauke hakkokinsa da suka rataya akansa dole wannan ya haifar masa da matsala a cikin rayuwar aurensa koda kuwa iyayen masu hakuri masu kau da kai ne.
Magani: Dole magidanci ya tsayu kuma ya kafu da daidaita adalci a ciki huddudinsa da mu’amularsa da bangarorin biyu. Da farko Ya san cewa hakkin iyaye ya girmama kuma ya daukaka sama da duk wani hakki in ba na Allah SWT da Manzonsa bane, don haka in har iyayensa ba masu hali bane, dole sai ya sauke bukatunsu na rayuwa sannan ya sauke na iyalinsa; kuma ba dai-dai bane ace matar mutum tana zaune a daki mai shafe da siminti mahaifiyarsa kuma tana zaune a daki mai daben kasa; ko gidan magidanci ana cin kayan dadi, iyayenshi kullum daga tuwo sai kunu. Don haka wannan hakki shi magidanci zai fara saukewa kafin ya sauke na matarsa. Duk da haka kuma kar ya zurfafa cikin haka har ya wuce gona da iri ya kasance ya bar matarsa tana tagayyara, dole ita ma ya sauke mata dukkan hakkokinta dai-dai gwargwadon hali; iyaka dai maigida ya sani hakkin matarsa na kasa da na iyayensa, domin yawancin maza a wannan zamani sun fiye karkata ga matansu da ‘ya’yansu kadai su mance da iyayensu, wasu ‘yan kadan kuma na karkata sosai ga iyayen har ya zan suna cutar da matansu da ‘ya’yansu; don haka dole sai maigida ya zama cikakke kuma tsayayyen namiji mai tsayuwa da dai-daita adalci a cikin al’amuransa a koda yaushe.
4. Kishin Uwar miji: Karkataccen kishi da gasa da wasu Uwayen magidanta kan bayyanar ga matayen ‘ya’yansu wata guba ce dake gurbata zaman lafiyan rayuwar aure wata sa’in har ma ta kai ga halakar da ita gabadaya. Irin wannan kishi da gasa wani bakin sinadarine da aka zo aka ajiyesa ba a mazuninsa ba, aka kuma aikatar da shi a wurin da ba ma’aiktarsa ba, don haka dole sakamakon abinda wannan sinadari zai fitar duk lokacin da aka aiktar da shi ya kasance wani abune mummuna kuma abin kyama kuma abin Allah Ya kyauta. Wasu daga cikin alamun kishin uwar miji ga matar dansu shine in ya kasance uwarmiji tana takurawa ga matar danta, ta ki barin wanzuwar zaman lafiya tsakaninta da mijinta, kullum burinta ta haifar da husuma tsakaninsu ta hanyar bakanta da dora mata laifuka na karya da na gaskiya; in Uwar miji tana jin kyashin duk wani abin alherin da danta yayi ga iyalinsa kuma tana bayyanar da wannan jin kyashin nata; in uwar miji ta kanannade dan nata a dan yatsanta, ta yadda itace ke zartas da duk wasu al’amura na iyalansa, misali, kayan abinci da kudin cefane duk suna wurinta da sauransu.
Abubuwan da ke haifar da Kishin Uwar Miji:
· Wasu uwayen magidanta bayyanar da irin wannan kishi lalura ce daga cikin shimfidar ma’aikatar hankalinsu, don haka ba da gangan suke yi ba, su a ganinsu, fahimtarsu da hankalinsu, hakan da suke yi shine dai-dai.
· Yayin da wasu iyayen mijin kuwa da gangan suke yi, saboda mummunar zuciyarsu, mummunan halinsu da kuma mugun nufin dake cikin zuciyarsu.
· Wasu kuwa dole ce take sa su aikata haka; saboda karkatar da wasu magidantan ke yi kacokan a kan matayensu, su mance da iyayensu na iya haifar da irin wannan kishi, musamman in aka yi la’akari da yadda mutane za su yi yada jita-jita na zuga ga iyayen, a rika cewa ga uwar miji ‘kura da shan bugu gardi da amshe kudi!? Don dole sai kin mike tsaye ke ma!’ da kuma zuga da rade-radin shaydan a zuciya, irin wannan yau da gobe na iya sa uwar miji ta fada cikin wannan bala’i na bayyanar da kishi a kan matar danta; a irin wannan, da dan nata ya canza yana sauke mata dukkan hakkokinta da suka rataya a kansa ita ma za ta canza ta bar wannan bakar dabi’a. Da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.
Sai mako na gaba in sha Allah, za kawo karashen bayani a kan hanyoyin da za a bi don magance wannan matsala, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.