Ladubban Warware Husuma Auratayya 9

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya […]

Ladubban Warware Husuma Auratayya 9
Ladubban Warware Husuma Auratayya 9

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.

Abubuwan da ke haifar da kishin Uwar Miji, Cigaba:
• Bankaurar Suruka: Wasu matan su kan tsinci kansu ne cikin halin kishi da matar dan da suka haifa a dalilin matar dan nasu wata bankaura ce da ba ta da wayau kuma ba ta da dabarar gane abu mafi kyau kuma mafi alfanu daga abu mafi muni kuma maras alfanu daga cikin al’amuran rayuwa. Bankaurar suruka ita ce wacce take jin tafi uwa iko da danta da kayan danta; ita ce wacce take wulakanci da izgilanci ga uwar mijinta; tana jin ba ragi ba ragowa, in uwar miji ta yi mata daya sai tay mata goma; ita ce wacce ba ta taimakon mijinta wajen karfafa masa gwiwa a kan ya girmama mahaifiyarsa; ita ce wacce take tsara makirce-makirce ta yadda mijinta ba zai kula da mahaifiyarsa ba balle har ya ba ta hakkokinta; da sauran miyagun dabi’o’i makamantan wadannan. Idan matar da ta kasance haka, halin bakin ciki da kuncin da miyagun ayyukanta suka haifar na iya jefa uwar miji ta tsinci kanta cikin bayyanar da karkataccen kishi ga matar danta. Ma’aurata ku sani, auren bankaurar mace bai halatta ba a Musulunce, domin duk mace mai irin wadannan dabi’un to ba Salihar mace ba ce; kuma cigaba da zaman aure da ita a haka yana da hadari ga sakamakon lahirar Magidanci; don haka sai a dage da neman maganin haka ta hanyar rokon Allah da yi mata nasihohi har Allah ya ganar da ita ta tuba ta daina.
Maganin Kishin Uwar Miji:
1. Riga Kafi: Akwai yadda ma’aurata za su bi su yi rigakafin kishin uwar miji tun kafin ya kai ga faruwa har ya zama barazana ga zaman lafiyar auratayyarsu. Yin wannan rigakafi yana daga cikin manyan shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su fi bai wa muhimmanci sama da shirye-shiryen shagalin buki; domin shagalin buki kusan za a iya cewa bai da wani alfanu ga tabbatar da dorewar rayuwar aure. Amma yin rigakafin kishin uwar miji da makamantan shirye-shirye sune masu tabbatar da dorewar zaman lafiyar auratayya. Don haka shawara ga ma’aurata, in har suna da burin kasancewa tare har abada, in har suna son Allah Ya ba su zaman lafiyar nan da kowa yake yawan yi masu addu’arsa, dole sai sun bai wa shirya yadda za su kula da sabuwar shukar auratayyarsu muhimmanci sama da shirya kayataccen buki na gani na fada da ya zama ruwan dare a wannan zamani. Ga hanyoyin yin rigakafin kishin uwar miji:
• Maigida, a matsayinsa na da ga mahaifiyarsa, ya san halayen mahaifiyarsa da yadda take mu’amalantar mutane daban-daban; don haka yana da kyau mai niyyar aure, sabon ango ko sabon magidanci ya zauna yayi nazarin halayyar mahaifiyarsa da yadda take hulda da mutane, sannan yayi amfani da karfin hangen nesansa na da namiji, ya hango ya zata mu’amulanci surukarta, shin zata zama mai saukin hali da saukaka halayya gareta ko zata zama mai takurawa gareta ta hanyar kokarin juya ta, maida ita kamar baiwa da hana ta wali a cikin gidan aurenta? Sannan ana kyautata zatton mutum mai niyyar aure, sabon ango ko magidanci ya kasance ko yaya ne ya san wasu daga cikin halayen matar da zai aura ko ya riga ya aura, don haka sai yayi tunanin shin ya mu’amalarta zata kasance da surakarta, shin zata zama mai ladabi da biyayya, mai juriya ga wasu halaye maras dadi daga surukarta? Zata zama mai bin ta sannu-sannu, mai gudun bacin ranta, mai boye duk wani abu ko wata magana da ta san zata bata mata rai ko zata zama marar wayau mai yin abubuwan da zai sa surukarta ta runka jin haushinta har hakan ya kai ga ta tsakulo baki kuma karkataccen kishinta gareta? Duk abinda tunanin mutum ya hango masa, sai yayi amfani da wannan wajen fitar da wani kyakykyawan tsari da zai zama mai tsare mutunci da kare hakkin matar, uwar da shi kan shi magidancin.
• Haka kuma duk wata uwar da danta yake gab da yin aure ko yayi sabon aure, ya kamata ta zauna tayi ma kanta karatun ta natsu, tayi nazarin cewa tunda ta haife danta yake a matsayin nata ita kadai, ba wanda ya kaita girman iko da tinkaho da shi da rayuwarsa ma gabadaya; amma daga ranar da yayi aure, to wannan dan nata kuma ya zama mijin wata mata, don haka dole yanzu ta dan jinginar da wasu mukamai da a da ita akadai take da iko dasu a rayuwarsa. Duk wata uwa ta sani, daga lokacin da danta ya mallaki hankalin kansa, ya kamata ta rage yawan tsoma baki cikin harkokinsa da takura masa sai yabi ra’ayinta, sai yayi abinda take so a koda yaushe; irin wanan yawan tsoma bakin na haifar kaushi, kauje da kuraje ga soyayyar da ga uwarsa; maimakon ta cigaba da ginuwa da girma, sai ya kasance ta tsaya cak sai dai abubuwan kulawa da na sadaukarwa na bayane in an tunosu suke rike da soyayyar, amma yanzu saboda tsananin takurawa daga wajen uwa, sai ya kasance sabbin sinadaran kauna basu shiga balle har su kara raya soayyar ta cigaba da girma. Ko don guje ma wannan, sai uwa tayi dauri aniyar yin iyakar kokarinta don ganin cewa ta zama dattijuwar suruka ta gari abin yabo abin kwantance.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.