Ladubban Warware Husumar Auratayya (1)
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. A yau cikin yardar Allah za mu fara ne da gabatar da bayanai akan husuma a cikin rayuwar aure, abubuwan da ke haifar da ita, da hanyoyin kauce […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. A yau cikin yardar Allah za mu fara ne da gabatar da bayanai akan husuma a cikin rayuwar aure, abubuwan da ke haifar da ita, da hanyoyin kauce wa faruwarta, da kuma sinadaran wanzar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin ma’aurata, don kara wa ganuwar auratayya karfi da inganci; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Ma’anar Husuma: Husuma na nufin lokacin da aka samu bambancin fahimta da bambancin ra’ayi tsakanin mutum biyu ko sama da haka wanda wannan bambanci ya yi kamari har ya haifar da bacin rai, jin haushin juna ko rashin jituwa tsakaninsu. Husuma irin ta zamantakewar auratayya na faruwa ne lokacin da faruwar wani abu ya haifar da sabawa da jin haushin juna tsakanin ma’aurata wanda hakan na iya zarcewa har ya haifar da jayayya, fadace-fadace da kullatar juna a tsakanin ma’aurata. Duk inda mutum biyu mabanbantan juna suka hadu yau da gobe dolene a samu sabawa tsakaninsu, kamar yadda Hausawa kance ko tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa. Husuma irin ta rayuwar aure tana da fuskoki daban daban, mafi yawan lokaci ba ta cika yin tsanani ba, wata sa’in kuma ta kan zarce ta zama gagarumar husumar da kan iya haddasa wasu manyan matsalolin daban. Husuma ba koda yaushe take zama barna ko laifi ba, babban abin dubin shi ne ta yadda ma’aurata suka tunkare ta. In ma’aurata suka tunkari husuma ko wani sabanin da ya shiga tsakaninsu ta kyakykyawar hanya, wannan zai iya zama sanadiyyar samun karin fahimtar juna da karuwar zaman lafiya a cikin rayuwara aurensu. Husumar da aka warwareta ta kyakykyawar hanya na iya kara dankon soyayya da kuma zakaka zamantakewar auratayya. Amma husumar ta aka tunkareta da hanyar da ba ta dace da ita ba, na iya zama sanadiyyar tashen-tashen hankula, wata sa’in har abin ya kai ga uwar aure tsakanin ma’aurata.
Sinadaran Husumar Auratayya: Kowace husuma da ta faru tsakanin ma’aurata dole akwai abinda ya haddasa ta, wata husumar sinadarinta dan karami ne amma in wasu matsaloli suka shigo cikin kamar son kai, karancin fahimtar juna, kin daukar laifi, rashin hakuri da rashin kau da kai, sai su bunkasa ta, ta yi kamari har ta wuce misali; wata husumar kuma sinadarin da ya hada ta zai iya kasancewa mai girma ne ainun, amma a dalilin ma’aurata sun tunkare ta ta siga mai kyau, sai su yi maganinta tun kafin ta bunkasa ta yi kamari. Don haka sinadarin da ya hada husuma tsakanin ma’aurata ba shi ne matsala ba, haka nan husumar ita ma ba matsala ba ce, amma yadda ma’aurata suka tunkari warware husumar a nan babbar matsalar take. Ga bayani kan muhimman abubuwan da suke yawan haddasa husuma tsakanin ma’aurata:
1. Banbancin halayya: Hausawa na cewa sai hali ya zo daya ake abota; wannan kam haka yake musamman a zamantakewa irin ta rayuwar aure wacce ta sha bamban da kowace irin zamantakewa, kuma tana dauke da sarke-sarke sama da kowace irin zamantakewa. In aka samu bambanci mai girman gaske a cikin gundarin halayyar ma’aurata, to wannan dalili ne da zai iya zama sanadiyyar yawan zargin juna da yawan fadace-fadace a tsakaninsu. Musamman in ya kasance fahimtar juna ta yi rauni sosai, kuma babu budaddiyar hanyar sadarwa a tsakaninsu. Misalin haka shi ne Maigidan da yake da son girma da tsare gida, in ya auri mace mai jiji da kai da rashin iya bin umarni dole za su yi ta samun yawan ka-ce-na-ce da ka iya haddasa husuma a tsakaninsu.
Magani:
In ma’aurata suka fahimci bambanci gundarin halayya ne sinadarin da yake yawan haifar da rashin zaman lafiya a tsakaninsu, to sai su bi wannan hanyoyin don ganin sun warware wannan matsala don samun cigaban zaman lafiya da wanzuwar kyakykyawar zamantakewar aure a tsakaninsu:
·Ma’aurata su yi kokarin samar da kyakykyawar fahimtar juna a tsakaninsu; domin komin irin nisan bambancin da ke cikin halayyar ma’aurata, in akwai kyakykyawar fahimtar juna a tsakaninsu, wannan zai zama kamar wata ganuwa ne da za ta karesu daga afkawa cikin tafkin husuma, in kuma yanayin yau da gobe ya sa suka afka din, to fahimtar juna ita ce kamar gugar da za ta tsamo su daga ciki, da Yardar Allah. Ana samun fahimtar juna ne ta hanyar yawan tattaunawa tsakanin ma’aurata, kowa ya fadi ra’ayinsa akan mabanbantan abubuwa na rayuwa, a cikin haka kowanne sai ya yi kokari ya fahimci yanayin halayyar dan’uwansa, abinda yake so da wanda bai so, da mafi kyawon hanyar da ya kamata a yi hulda da shi don kauce wa bacin ransa; sannan da yawan sadar da zumunta tsakanin juna, da yin abubuwa tare, musamman ayyukan gida, cin abinci, zuwa unguwa, da sauransu, da haka ma’aurata za su kusanci juna sosai su zama kamar shakikan abokan juna, kowannensu ya fahimci halin dan’uwansa, ya san abinda ke bata masa rai da abinda yake faranta masa rai, to in aka samu irin wannan fahimtar juna, da wuya a rika samun yawan husuma a tsakanin ma’aurata sai dai na bacin rana. Sannan wasu kyawawan dabi’u da za su taimaka ga warware irin wannan matsala shi ne hakuri, yawan kau da kai ga kurakuran juna, da kuma yawan yi wa juna uzuri.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.