Ladubban Warware Husumar Aure (10)
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1. Rigakafin Kishin Uwar Miji, cigaba…
· Ita kuma mace mai niyyar aure, amarya ko sabuwar uwargida ya kamata ta yi wa kanta karatun ta- natsu game surukarta tun kafin hulda ta yi nisa har ta kai ga baci tsakaninsu. Ta sa kanta a matsayin ita ce ta haifi yaro, ta rene shi ta sha wahalar fadi tashin kula da shi, har ya girma ya yi aure, shin da wane irin halaye da dabi’u za ta so matar dan nan nata ta huldanceta da su, amsar da zuciyarta ta ba ta a wannan lokaci shi ne kamar wata dabara (formula) da za ta rika amfani da shi a cikin huldarta da surakarta a kowane hali a cikin zamantakewarta da ita; ko wanin abu marar kyau surukarta ta yi mata sai ta yi tunani ta ce “in ni ce na yi wa matar dana irin wannan mummunan abin ya zan so ta yi mani? Ta yi hakuri ta kyale ni ko kuwa ta yi min rashin kunya ta nuna min ban kyauta ba? Duk amsar da zuciyarta ta ba ta haka zat a rika yi; in dai har ya kasance ta sa kyakykyawar niyya cikin zuciyarta, insha Allahu wannan zai taimaketa, ya kasance yanayin huldarta da surukarta bai zama sanadiyyar tsakulo karkatacen kishin uwar miji ba.
1. Hanyoyin Magance Matsalar Kishin Uwar Miji:
Abinda Magidanci zai yi: In maigida ya fahimci bayyanar karkataccen kishi daga wajen mahaifiyarsa ga matar da yake aure, ya kamata ya dauki kwakwaran mataki tun kafin abin ya yi nisa, domin in ya riga ya yi nisa duk matakin da zai dauka kuma sai ya haifar da wata matsalar ta wani wurin.
· Abu na farko da magidanci zai fara yi shi ne ya sanya tsananin taka tsan-tsan wajen hulda da mahaifiyarsa a irin wannan yanayi, kar ya rika bayyana jin haushinsa gareta; ko ya rika tsanarta ya rika ganin ta takura wa rayuwarsa da sauransu; koma wane irin hali ta bayyanar, tana nan dai a matsayinta na mahaifiyarsa kuma ba wanda zai masa irin kauna da kulawar da ta yi masa. Sannan komin tsanantar da al’amari ya yi, kar ya ce zai mata fada ko ya yi mata magana cikin hassala, wannan haramun ne, sai dai ya yi mata magana cikin rarrashi, kwantar da kai da ban hakuri. In ma fadan har ya zama dole, to sai dai ya nemi taimakon magbatanta ko wasu manyan gari su yi mata amma ba dai shi ba.
· Abu na biyu shi ne kar ya sake ya daukaka matarsa sama da mahaifiyarsa ta kowace fuska, ko dai ya daidaita, ko ya daga mahaifiyarsa koda da taku daya ne wajen nuna kulawa da wadatawa.
· Abu na uku shi ne ya fahimci cewa akwai bambanci tsakanin kaunar da zai wa matarsa da wacce zai yi wa mahaifiyarsa; bai kamata kauna da kulawar daya ta dakusar da ta daya ba, dole ya san hanyar da zai daidaita ya kasance kowacce ya ba ta kulawarta daidai da yanayin dangantakar dake tsakaninsu; domin da yawa magidanta sukan bari soyayya da kulawar da suke wa matayensu ya dakushe na mahaifiyarsu a zuci da kuma a aikace, har ya kasance suna dai kula su ne akan dole ba akan son ransu ba. Ba su kewarsu, ba su marmarinsu ba su zakwadin son kasancewa tare da su; wannan babban dalili ne da ke tsaksulo karkataccen kishin uwar miji, sai wasu mahaifan su rika ganin kamar matar dansu ta sace masu dan ne gaba daya, sun gama wahala yanzu ita kadai take shan dadin, ta sa dan nasu ya mance da su. Don haka nuna kauna da soyayya ta gaskiya ga mahaifa na maganin karkataccen kishin uwar mij.
· A yayin da karkataccen kishin uwar miji ya riga ya tsananta, magidanci zai magance wannan ta hanyar yin nazari, wane abu ne cikin yanayin zamantakewarsa da iyalinsa ke sa mahaifiyarsa bayyanar da karkataccen kishi? In ya fahimci abin, sai a yi dukkan kokari na kauce masa ko boye shi daga ganin idonta don dai a samar da zaman lafiya. Sannan in ya kasance a muhalli daya suke zaune, to a yi kokarin raba masu muhalli don wanzar da zaman lafiya, haka ma in ciyarwarsu a hade ne sai a yi kokarin rabawa don samun kwanciyar hankalin iyali duka; duk da cewa hakan karin dawainiya ne ga maigida amma kwanciyar hankalin iyalansa, musamman mahaifiyarsa wasu muhimman hanyoyi ne na samun albarka a cikin harkokin rayuwar magidanci.
· Sannan magidanci ya nemi goyon bayan uwargidansa; ya aza mata dokoki da sharudda kan yadda za ta huldanci mahaifiyarsa amma ba wadanda za su zama cutarwa a gareta ba. Ya nuna mata muhimmanci kyautatawa ga mahaifiyarsa a duniyarsa da lahirarsa; sannan ya ja kunnenta sosai game da yi wa mahaifiyarsa rashin kunya akan kowane irin dalili ne, kuma in har ta yi to ya hukunta daidai gwargwado ta yadda ba za ta yi marmarin kara yi ba.
Sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.