Ladubban Warware Husumar Aure (12)

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance su.  Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu […]

Ladubban Warware Husumar Aure (12)
Ladubban Warware Husumar Aure (12)

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance su.  Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Hanyoyin Magance Karkataccen Kishin Uwar Miji, Cigaba…
Abinda ’yan uwa, kawaye, da abokai za su iya yi:
’Yan uwa, kawaye, da abokan maigida da na uwargida har ma da uwar miji na da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya da kauce wa faruwar rigingimu tsakanin uwargida da surukarta. Duk wani labarin da suka san in uwargida ko suruka suka ji zai haifar masu da jin haushin juna dole su yi dukkan kokarinsu don ganin maganar na ba ta isa ga kunnen dayansu ba.
· Kar ’yan uwan maigida, musamman kannensa su saurari wani mummunan kalami daga bakin mahaifiyarsu game da matar dan uwansu, su fitar da maganar nan har ta je ga kunnen wanda zai iya sanar da matar dan uwansu; haka kuma duk wani labari game da yanayin zamantakewar auren dan uwansu da suka san zai sosa ran mahaifiyarsu, sai su yi dukkan kokarinsu don ganin cewa labarin bai isa ga kunnenta ba. Su kasance masu yawan tausar zuciyar mahaifiyarsu cikin lalla shi da kwantar da kai game da fushinta akan matar dan uwansu; su zama jakadun jaddada zaman lafiya; kar su zama mataimakan shaidan ta hanyar haddasa fadace fadace da rashin zaman lafiya tsakanin matar dansu da mahaifiyarsu.
· ’Yan uwa da kawayen uwargida ma sai su dage da ba ta kyawawan shawarwari game da yadda za ta huldanci surukarta; in ma ta yi masu mita game da wasu halayen uwar mijinta da suke ba ta haushi, ko wasu abubuwan takura wa da surukarta ke mata, su yi kokari su taushi zuciyarta da kyawawan kalaman ban hakuri da dauriya don ta kara dagewa ta cigaba da kyautata hulda da uwar mijinta; kar su zama mataimakan shaidan ta yadda za su rika gaya mata kalaman da za su tunzurata har ta rika yin rashin kunya da rashin kyautatawa ga uwar mijinta.
10. Tasirin Shau’uka Da Sinadaran Rai wajen haddasa husuma tsakanin ma’aurataa:
Matsala ta goma daga cikin matsalolin da suke yawan haddasa faruwar husuma tsakanin ma’aurata shi ne tasirin shau’uka da sinadaran rai ke da shi ga dabi’u da kyautuwar ko munana zamantakewa tsakanin ma’aurata. Da farko ya kamata ma’aurata su san mene ne sinadaran rai don su samu saukin fahimtar tasirinsu a cikin rayuwar aurensu: Sinadaran rai dai wasu sinadarai ne kala daban daban wadanda sun kasance kamar mazauni ko ’yan aikin ma’aikatar hankali da suke aikin yada bayanai tsakanin bangarorin jikin dan adam da kwakwalwa; kowane abu yake faruwa a cikin jikin dan adam, akwai wani sinadari da yake da alhakin zartas da wannan aikin; tun daga tunani, motsi,  jin haushi, tace abinci; gudanar jini, numfashi ; zufa; fitar da najasa; jima’i; bayyana da tafiyar jinin haila, daukar ciki da sauransu kowanne akwai wani sinadari ko taron sinadarai da suke da alhakin tabbatar da faruwarsa, Kuma in aka samu kasawa a daya daga cikin bangarorin zartaswa na jiki za ka ga yana da nasaba da sinadarin dake da alhakin zartas da wannan al’amari. Don haka sinadaran rai na da nasaba ga shau’ukan dake kai kawo cikin zuciya da ma’aikatar hankali; shau’uka kuma na da nasaba da dabi’un yau da kullum na dan adam; dabi’u kuma na da nasaba da yanayin zamantakewar auratayya. Don haka daidaituwar sinadaran rai na samar da wanzuwar kyawawan shau’uka cikin zuciya da ma’aikatar hankali, wannan shi zai haifar da kyawawan dabi’un da za su haifar da kyakykyawar zamantakewa tsakanin ma’aurata. Rikirkicewar sinadaran rai na haifar da wanzuwar munanan shau’uka cikin zuciya da ma’aikatar hankali; wadannan za su haifar da munanan dabi’un da za su zama shimfidar yawan fadace-fadace da rigingimu tsakanin ma’aurata.
Rigakafi Da Magani:
Ma’aurata za su yi rigakafin da kuma maganin wannan matsala ta hanyar tabbatar da daidaituwar sinadaran rai a koda yaushe a cikin zuciya da ma’aikatar hankalinsu; domin in sinadaran rai suka daidaita, suke haifar da kyawawan sha’uka cikin zuciya, in kuma suka yawaita ko suka rikirkice sai su haifar da munanan shau’uka cikin zuciya; shau’uka kuma suke yin babban tasirin ga kyautuwa ko rashin kyautuwar zamantakewa; domin maganar da mutum zai fada lokacin da yake cikin fushi ta sha bamban da wacce zai fada lokacin da ba ya cikin fushi; shau’kin fushi bai taba bayyana sai tare da yawaitar sinadarin dake haifar da shi cikin jini(cortisol); don haka hanyar yin rigakafin wannan matsala ita ce kauce wa duk wani abu da zai haifar da yawaita ko rikirkicewar sinadaran rai masu nasaba da shau’uka da dabi’a. Ma’aurata zasu yi haka ne ta hanyar danne duk wani bakin shauki da ya bayyana a zuciyarsu kamar fushi, jin haushi, tsana, da sauransu tun farkon bayyanarsa cikin zuciyarsa, kada su bar shi ya yi tasiri cikin magana da ayyukansu, wannana zai sa sinadarin da ke da alhakin zartas da wannan shau’ki ya yi kasa ya rage yawa cikin jini har ya daidaita; in yin haka ya zama dabi’a ga ma’aurata, shine rigakafi da kuma maganin faruwar husuma tsakaninsu ta hanyar rikircewar sinadaran rai da bayyanar bakaken shau’uka masu lahani ga dorewar kyakykyawar zamantakewa. Kamar Yadda Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wa Sallam Ya umarce mu da yi lokacin bayyanar shaukin fushi cikin zukatanmu, shi ne mutum ya kulle bakinsa kar ya ce komai; kuma in yana tsaye ne ya zauna, ko ya kwanta har sai fushin nan ya sauka. In danne fushi ya zama dabi’ar ma’aurata, a hankali fushin zai rage bayyana sai dai kadan, wannan shi ne daidai, domin fushi mai yawa bai da amfanin komai; haka dukkan wani bakin shaukin da ya yawaita bai da amfani sai dai ya cutar da mamallakinsa.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodasyaushe, amin.