Ladubban zabar mijin aure (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili. Ga bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yan matanci. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin: Ladabi na 6: Ladubban ’yan matanci: ’Yan matanci wani takaitaccen lokaci ne mai kunshe da wasu dabi’o’i […]

Ladubban zabar mijin aure (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili. Ga bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yan matanci. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin:

Ladabi na 6:

Ladubban ’yan matanci:

’Yan matanci wani takaitaccen lokaci ne mai kunshe da wasu dabi’o’i da halaye na musamman wadanda bayyanarsu ya zama dole ga kowace ’ya mace. Wadannan  halaye da dabi’o’i suna farawa ne tun daga farkon balaga har zuwa tsawon wasu shekaru mabanbanta ga kowace ’ya mace. Wadannan dabi’u suna bayyana tare da canjawar ginuwar jikin ’ya mace daga na yarinya zuwa na cikakkiyar mace. Irin wadannan dabi’u sukan bayyana cikin yanayin magana, tafiya, murmushi kallo da sauransu. Kuma suna bayyana cikin siga mai jan hankali da rudarwa ga namiji. Amfanin bayyanar wadannan halaye masu rudarwa ga namiji shi ne don su zama sinadaran darsa soyayya da motsar da sha’awar mijin da mace ta aura don inganta dadin zamantakewar rayuwar aure. Don haka amfani da su da ’yan mata ke yi wajen jan hankalin samari barnarsu kawai suke yi da wuce ka’idojin addinin Musulunci. Don kauce wa fadawa cikin haramtattun abubuwa, ya kamata ga kowace mace Musulma da ke jiran fitowar mafi dacewar miji gare ta ta san abubuwan da suka dace da wadanda ba su dace ba na daga dabi’un ’yan matanci, kuma ta san yadda za ta iya sarrafa dabi’un ’yan matancinta ya kasance ba su rinjaye ta zuwa ga aikata abubuwan da za su haifar mata da matsala cikin rayuwa ba.

1. Da farko yana da kyau ga mai jiran fitowar miji ta san irin salon ’yan matancinta da kuma irin tasirinsa; domin kowace mace irin salonta daban da na ’yar uwarta; in ta fahimci irin salonta da irin tasirinsa da haka ne za ta iya mulkinsa da sarrafa shi ta hanya mafi dacewa, ta yadda zai zama abin alheri a gare ta ba abin sharri ba.

2. Ladubban Kwalliya: Son yin kwalliya wata babbar dabi’a ce cikin dabi’un ’ya mace, shi ya sa ko yaran da ba su balaga ba suna son yin ado da kwalliya; don haka ne Allah Madaukakin Sarki bai haramta yin kwalliya da ado ba sai dai Ya yi umarnin a boye su daga ganin mazan da ba muharramai ba.

Yana da matukar alfanu ga mace Musulma ta san irin kwalliyar da ta halatta da wacce ba ta halatta ba; kuma ta san irin kwalliyar da ta halatta ta bayyana da wacce ta zama tilas ta boye ta.

’Yar uwa Musulma ta sani cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya umarci dukkan mata Musulmi kada su bayyanar da adonsu face ga mazan da babu aure a tsakaninsu har abada kamar yadda ya zo a Aya ta 31 a  Suratul Nur.

Ga ladubban kwalliya ga ’ya mace kamar haka:

1. Yin kwalliya, da ado cikin salo mafi kyau kuma mafi dacewa ya halatta; kuma bayyanar da ita ga ’yan uwa mata da mazan da babu aure a tsakani har abada; ko mazan da ba su da sha’awa, ko yara kanana, shi ma ya halatta.

2. Bayyana kwalliya ga dukkan namijin da ba muharrami ba haramun ne kamar yadda ya zo a wannan aya da aka ambata a sama. Haka bayyana kwalliya ga mazan da ba muharramai ba, ta hanyar sanya abubuwa masu fitar da sauti in jiki ya motsa kamar awarwaro, sarkar kafa, ko ta hanyar takalmi mai fitar da sauti in ana tafiya, shi ma yin hakan bai halatta ba. Don haka rufe jiki da hijabi bai bada damar sanya irin wadancan kayan kawa masu fitar da sauti matukar mace ta san za ta bayyana a gaban mazan da ba muharramanta ba.

3. Caba ado a fuska, ta hanyar shafa hoda mai canja launin fata, ko ta hanyar rina lebba da jambaki mai launin fau da shafa man lebe mai kyalkyali; yin fenti a fatar saman ido, jan girar ido da jagira har ta wuce asalin inda tsawonta ya tsaya da sauran ire-iren wadannan kwalliya na adon fuska, haramun ne mace Musulma ta bayyanar da su ga mazan da ba muharramanta ba. Wasu daga ire-iren wadannan kwalliya ma bai dace mace mai mutunci ta yi su ba; domin maimakon su fito da kyaun fuskar, wasu sai dai su sanya mata launin fitsara da kekashewar zuciya; wasu kuma irin adon mutanen da ba Musulunci a zuciyarsu ne, wanda haramun ne kwaikwayon dabi’u irin nasu. Don haka caba ado kaca-kaca a fuska bai dace da mace Musulma ba, sai dai in za ta rika rufe fuskarta ce koyaushe ta caba irin wannan ado. Amma yin ado sassauka da kayan kwalliya masu saukin rini, ta yadda za su inganta kyan fuska ba tare da sun canja wani abu daga gare ta ba shi ne ya dace da kowace Musulma.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.