Ladubban zabar mijin aure (4)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.Barkanmu da sake haduwa a wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yan matanci; da fata Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin: Ladubban Kwalliya, ci gaba… 4. Sanya turare mai karfi, irin wanda duk a mace ta wuce […]

Ladubban zabar mijin aure (4)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.Barkanmu da sake haduwa a wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yan matanci; da fata Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin:

Ladubban Kwalliya, ci gaba…

4. Sanya turare mai karfi, irin wanda duk a mace ta wuce sai an ji kanshinsa, yin haka bai halatta ba; sai dai mace ta sa turare mai sanyin kanshi ta yadda ita kadai ke jin abinta sai kuma wanda ya matso kusa da ita sosai.

  1. Amfani da man shafawa mai karfin kanshi, ko mai canja launin fatar jiki, ko mai haifar da wata tangarda ga fatar jiki; shi ma bai halatta ba.
  2. Ladubban sanya tufafi: Kamar yadda ya gabata, mace Musulma za ta rufe jikinta gaba daya da hijabi koyaushe bukatar bayyana gaban mazan da ba muharramai ba ta kamata; kamar yadda Allah (SWT) Ya yi umarni a Aya ta 59, cikin Suratul Ahzab:

“Ya kai Annabi! Ka ce wa matan aurenka da ’ya’yanka da matan muminai su kusantar kasa daga manyan tufafin da ke kansu. Wancan ya fi sauki da a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara Mai jinkai.”

Wannan Aya mai abarka ta bayyana mana cewa wannan umarni na Allah Madaukakin Sarki, Ya shafi dukkan matan Musulmi: masu aure, zawarawa, masu takaba da ’yan mata. Don haka babban kuskure ne, kuma ketare iyakokin Ubangiji ne irin shigar nuna kawa da bayyana siffofin jiki da yawancin ’yan matan wannan zamani suke yi da sunan ’yan matanci ko da sunan tallata kai don a samu mijin aure. Manzon Allah (SAW) ya bayyana irin wadannan mata da cewa su tsinannu ne don haka in an gan su a tsine musu, kuma ya ce ba za su ji kanshin Aljanna ba balle su shige  ta. Don haka ya ke ’yar uwa! Ki sani, duk wani farin jini, duk wani arziki, duk wani matsayi da daukakar da za ki samu dalilin yin shigar da ta saba addininki, za ki ji dadinsu ne na dan kankanen lokaci kadai, azabar Lahira kuwa madawwamiya ce. Don haka kada ki bari Shaidan ya yi amfani da zafin kan ’yan matanci ya hallakar da ke ya hana ki dacewa da Aljanna, ya tabbatar miki kasancewa cikin azaba. In kunne ya ji, jiki ya tsira!

  1. Ladubban yanga da yatsina: Zafin kai irin na ’yan matanci na sa har macen da ba ta da dabi’un yatsina, yanga da kwarkwarsa ta ji tana son yin wadannan dabi’u a wasu lokuta. Wadannan dabi’u suna shagaltar da namiji wani sa’in har su tsundumar da shi cikin begen sha’awa. Haram ne ga ’yan mata yin wadannan dabi’u ga samarinsu ko ga mazan da ba muharramansu ba. Wadannan dabi’u sun halatta ne kadai mace ta yi su ga mijinta. Wadannan sun hada da: salon magana, tsara kalami cikin siga mai jan hankali, kashewa ko sanyaya murya wajen magana; yin wani salon furuci marar ma’ana illa ma’anar saka fitina a zuciyar mai saurare; yin fari da ido, harara irin ta wasa, kallon hadarin kaji cikin tsiwa; gatsine da murguda baki cikin salon jan hankali; salon murmushi iri-iri cikin siga mai kayatarwa, salon tafiya da murgude-murgude; warwatsa hannaye cikin yanga da sauran ire-iren wadannan dabi’u duk haram ne mace mai jiran aure ta yi su ga wani mutum wanda ba mijinta ba. Sai dai wacce yana daga cikin ainihin dabi’arta yin daya daga cikin wadannan dabi’u; to ita ma sai ta sa kula sosai wajen yadda take mu’amala da mazan da ba muharramanta ba don tsaron mutuncinta da imaninta.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.