Lafiya da ilimi ke da kaso mafi tsoka a kasafin Jigawa na 2016 – Gwamna Badaru

Gwamnatin Jihar Jigawa ta  yi kasafin kudin shekarar 2016 yayin da kaso mafi tsoka ya tafi ga bangaren lafiya da ilimi.Da yake karanta kasafin kudin na bana Gwamnan Jihar, Alhaji Badaru Abubakar ya ce kasafin kudin na bana zai fi mayar da hankali wajen inganta aikin gona da rayuwar matasa.“Gwamnatin Jihar za ta kashe Naira […]

Lafiya da ilimi ke da kaso mafi tsoka a kasafin Jigawa na 2016 – Gwamna Badaru
Lafiya da ilimi ke da kaso mafi tsoka a kasafin Jigawa na 2016 – Gwamna Badaru

Gwamnatin Jihar Jigawa ta  yi kasafin kudin shekarar 2016 yayin da kaso mafi tsoka ya tafi ga bangaren lafiya da ilimi.
Da yake karanta kasafin kudin na bana Gwamnan Jihar, Alhaji Badaru Abubakar ya ce kasafin kudin na bana zai fi mayar da hankali wajen inganta aikin gona da rayuwar matasa.
“Gwamnatin Jihar za ta kashe Naira biliyan 137, domin aiwatar da muhimman ayyuka a jihar,” inji shi. Yayin da kananan hukumomin jihar za su kashe Naira biliyan 18.52 wajen harkokin ilimi, inda za a fi ba da fiffiko wajen gyaran makarantu da sayen kujeru da littattafan karatu da daukar malaman makaranta.
Ya ce, a bangaren kiwon lafiya da ya ja kaso mai yawa, gwamnatin za ta kashe mafi yawan kudin ne wajen kula da lafiyar mata da kananan yara da gyare-gyaren asibitoci, tare da inganta makarantun kiwon lafiya na jihar.
A cewar Gwamna Badaru, gwamnatin jihar ta tanadi hanyoyin samun kudin shiga wadanda da su ne gwamnati za ta samu damar aiwatar da ayyukan da take da bukatar yi wa jama’a. “Gwamnatin jiha za ta amso bashin daga Gwamnatin Tarayya don inganta aikin gona, domin sama wa matasa aikin yi,” inji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin jahar zata dauki dogon lokaci tana biyan ma’aikata albashinsu a hannu a kokarinta na zakulo ma’aikatan bogi daga ma’aikata na hakika saboda magance  aringizo da dukiyar gwamnati
Ya ce gwamnatin jihar a duk wata za ta ba da Naira biliyan daya da miliyan 200, a matsayin kudin hadaka na fansho, don biyan hakkin ma’aikatan da suka bar aiki ko suka rasu, inda ya ce, gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 315 wajen gina sababbin asibitoci da gyaran wadanda take da su.
Ma’aikatar Mata Walwalar Jama’a, an ware mata Naira miliyan 170; sai Ma’aikatar Watsa Labarai Naira miliyan 895; kananan hukumomin jihar 27 an ware musu Naira biliyan 57 da miliyan 200 domin gudanar da ayyuka.
“Gwamnatin jihar za ta rika bayar da kashi 40 cikin 100 na kason da take samu daga Asusun Tarayya a yi  hada-ka tsakaninta da kananan hukumomin jihar. Domin ganin komai ya tafi daidai wajen yi wa jama’a aiki,” inji Gwamna Badaru.
Da yake karbar kasafin kudin na bana Shugaban Majalisar Jihar, Idris Garba Kareka, cewa ya yi, za su sanya ido wajen ganin duk ayyukan da gwamnati ta ce za ta yi an yi su a kan ka’ida, kuma ba za su amince da wargi ba.
“Duk ayyukan da gwamnati ta bayar za mu bi su sau da kafa, wajen ganin an kammala su. Kuma za mu sanya ido a duk kwangilar da aka bayar don ganin an cika sharuddan da suka dace,” inji shugaban.