Lafiya uwar jiki
Babu mai fushi da ke, tabbas wannan haka yake, lafiya ta fi komai muhimmanci a rayuwar bil-Adama. Da lafiya ne muke da damar cimma burinmu na yau da gobe walau tafiya makaranta, aikin yi, takara da kowace mu’amala ta rayuwa. Hakan ke tabbatar mana da cewa, duk kasar da ta samu lafiya, ta samu arziki, […]
Babu mai fushi da ke, tabbas wannan haka yake, lafiya ta fi komai muhimmanci a rayuwar bil-Adama. Da lafiya ne muke da damar cimma burinmu na yau da gobe walau tafiya makaranta, aikin yi, takara da kowace mu’amala ta rayuwa.
Hakan ke tabbatar mana da cewa, duk kasar da ta samu lafiya, ta samu arziki, don haka zarar zaman lafiya ya tabbata, za a samu ci gaba, kuma tattalin arziki ya bunkasa. Saboda haka idan ba lafiyar jiki, babu wanda zai je makaranta, ya jure wahalar karatu, kakarewar kasuwa, aiki da inji a masana’antu.
Kuma idan za a yi zabe akan yi kamfen da zamanantar da harkokin kiwon lafiya! Sai dai ma’aikatar lafiya da asibitoci sun tsinci kansu a wani yanayi na kayata gine-gine daga waje, amma da shigarka ciki, wani wari za ka ji. Kuma ka iske ba kayan aiki! Kana ji, kana gani za a karya hakorinka.
Kwananan gwamnatocin jihohi na neman bashi, don su gina sababbin asibitoci domin inganta lafiyar al’umma, akan haka wasu suka yi kira da kar a kara gina sababbin asibitoci, a yi tunanin abin da ake bukata, kamar kara likitoci da ma’aikata kiwon lafiya a tsofaffin tare da wadatasu da magani da kayan aikin zamani. Sai a yi gyaran fuska! Wai shin asibitoci za mu ci, ko shi asibitin zai yi aiki a kashin kansa? Tabbas ta hanyar kwangiloli ake satar kudi!
Maimakon daukar shawara da isar da sakon ga gwamnati, sai a samu wasu ‘yan kanzagi da za su rika zagin mutane a matsayin kare mahukunta don su burge masu zartarwa. ba tare da la’akari da muhimmancin nasihar mutanen da ke zuwa asibitocin ba.
Halin da aka bar asibitocin gwamnati ya sa kusan kowa ya fi dogara da asibitoci masu zaman kansu, wadanda ake biyan kudi, sai ba kudin ake maneji a na gwamnati. Su kansu asibitocin gwamnati wani lokaci su suke tura mutane zuwa asibitoci masu zaman kansu don karancin gadaje, babu kayan aiki ko kwararre ko wasu kayan gwaje-gwaje! Duk da cewa wannan gurguwar fahimta ce, kwararrun ma’aikata sune mai’aikatan gwamnati, kuma ita gwamnati uwa ce, a haka komai na gwamnati ya kamata ya fi kyau da inganci.
Wani mataki wajen kawo ci gaba ga asibitocin gwamnati shi ne a kara haraji a kan asibitoci masu zaman kansu, ta yadda kwararrun na gwamnati da saukin kudi zai jawo a ingantasu. Domin a yau sai ka iske duk likitan da yake aiki a asibitin gwamnati yana da asibitinsa, wasu ma kayan na gwamnaticn suke sacewa su kai asibitocinsu!
Wajen neman mafita wasu na ganin gwamnati ta fi kowa wayo da dubara, kuma mahukuntan su suka san yadda talaka zai more romon dimokuradiyya.
A nan a lura kowa zai iya samun sa’a da hikima a rayuwa, kuma duk wanda aka wadata shi da hikima an ba shi komai! Kuma abin da yake mayar da shugabanni masu hikima shi ne saukin kai da sauraren kukan talakawa, wanda ya hada da share masa hawaye! Ba neman gulma ba daga annamimai, ita hikima ba digiri ko difloma ba ce, ko yawan mabiya.
Ana bakin cikin ma’aikatan kiwon lafiya domin albashinsu, abin lura shi ne ko ba alawus, likitoci na da lada a wajen Ubangiji. Kuma ya kamata a rika karfafa musu wajen yin kwas a nan cikin gida da waje don zamanantar da iliminsu, domin wasu cuttutukan na kama da juna, su samu horon zamanantar da maganin gargajiya, musamman domin wani lokaci kwayoyin cututtuka na bijire wa magani, ga hadarin magungunan jabu a kasuwa, su kansu jami’an lafiyar kan zama kamar wasu mahauta, a rika tsoronsu!
Da ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati za su rika zuwa asibitoci gwamnati ko a kwantar da su da danginsu da an gyara wani abin. Ta yadda ba sai an gina sababbi ba, kuma ta yadda masu zartarwa za su zo, da an tabbatar akwai magungunan da mabukata za su sha, su shafa a yi musu allura.
Sai dai mun wayi gari da gwamnatin da ke yawan kuka, kukan rashin kudi, idan aka yi maganar abubuwa masu muhimmanci, amma a harkokin masu zartarwa suna cin karensu ba babbaka. Gwamnatin da ba ta ga muhimancin tsarin kara wa ma’aikata alawus a bisa dalilan hadari, cin lokaci da rashin tsaro ba, wa zai yi musu aikin? Mutane suke yin aikin, ko mutum-mutumi ko ‘yar tsana za su yi aiki ko kuma a kyauta za a rika yin aikin don an sami canji! A guji barkonon tsohuwar likitoci don sai kowa ya ji a jikinsa!
Idan gwamnati ta ci gaba da yin kullen kashi game da bukatun talakawa, lokaci na zuwa inda su ma talakwa za su jefa kuri’unsu a shara. Dole a yaki alfarma game da lafiya, domin sai ka iske ana bai wa ‘yan mata takardar shiga makarantun koyon kiwon lafiya don alfarma, su gama ba su san komai ba. Tabbas zamanantar da asibitocinmu zai sa a bar zuwa kasashen ketare don neman lafiya.
Buhari Daure [email protected]
+2347035986444 Muryar Talaka Modoji, Katsina.