Lafiyar Kwakwalwa: WHO ta ba wa ’yan jarida horo na musamman

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a karqashin Majalisar Dinkin Duniya ta ba wa ’yan jarida horo na musamman kan kula da lafiyar kwakwalwa.

Lafiyar Kwakwalwa: WHO ta ba wa ’yan jarida horo na musamman

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a karqashin Majalisar Dinkin Duniya ta ba wa ’yan jarida horo na musamman kan kula da lafiyar kwakwalwa.

Taron na yini biyu, ya gudana ne a hedikwatar majalisar a Najeria da ke Abuja inda wakilan wasu zababbun kafofin yada labarai na gida da ketare da ke birnin, ciki har da Media Trust Group, masu Aminiya da Daily Trust, Trust TV da Trust Radio, suka samu gayyata.

Masana a bangaren lafiyar kwakwalwa sun gabatar da kasidu tun daga yinin farko na taron a ranar Litinin, sai kuma ranar Talata da ya zo daidai da 10 ga watan Oktoba da ke matsayin Ranar Lafiyar Kwaqwalwar na Duniya.

Daya daga cikin masu bada horon, Mista Michael Onotu wanda babban jami’in lafiyar kwakwalwa ne ofishin, ya ce ’yan jarida na fuskantar abubuwan fargaba a yayin gudanar da aikinsu, a saboda haka suna bukatar sanin yadda za su kula da lafiyar kwakwalwarsu da kuma yadda za su tinkari jama’a cikin tsanaki.

Moji Makanjuola wadda tsohuwar shugabar shirye-shiryen kiwon lafiya ce a gidan talabijin na kasa (NTA), ta shwarci ’yan jarida da su fifita daukar labarai kan matsaloli da al’umma ke fuskanta a cibioyin kiwon lafiya musamman a yankunan karkara, mainakon zama ’yan amshin shatan gwamnati a bangaren.

“Za ku iya amfani da alkalaminku wajen zaburar da gwamnati kan inganta kiwon lafiyar al’umma, ku kuma fadakar da su a kan yadda za su kula da lafiyarsu ta hanyar jin ta bakin masana bangaren,” in ji gogaggiyar ’yar jaridar.

Babban kodineta na ma’aikatar lafiya ta tarayya a kan inganta lafiyar kwakwalwa, Dokta Tunde Ojo ya gabatar da lacca kan kan rage matsalar damuwa ta kai da ta iyali, don magance kauce wa matsalar hawan jini mai muni da ke kaiwa ga shanyewar barayin jiki.