LAFIYAR MATA DA YARA Amsoshin Tambayoyi
Yaro ne dan shekara shida a wasu lokuta yakan samu idanunsa su rika kafewa kamar mai farfadiya. An je asibiti an ce ba rashin jini ba ne, to mene ne? Daga Malam Bala Katako, Jos Amsa: A’a to yaya za a yi na sani, likitan bai ce maka ga abin da yake tunani na damun […]
Yaro ne dan shekara shida a wasu lokuta yakan samu idanunsa su rika kafewa kamar mai farfadiya. An je asibiti an ce ba rashin jini ba ne, to mene ne?
Daga Malam Bala Katako, Jos
Amsa: A’a to yaya za a yi na sani, likitan bai ce maka ga abin da yake tunani na damun yaron ba? Kamar yadda ka ce abin na kama da farfadiya, haka ma a likitance mun san akwai nau’in farfadiya mai sa kakkafewar ido ko wani sashe daya kadai na jiki kamar hannu guda, amma babu suma ko mimmikewa. Wannan mukan kira shi da sunan farfadiya mai sauki, wato ba ta kai babbar farfadiya mai sa suma da fitar da hankali ba. Ku nemi likitan kwakwalwa wato neurologist a babban asibiti (Janaral) ko JUTH a kai shi a duba shi sosai.
Mene ne illar cin kasa a yara ne?
Daga A.B., Gombe
Amsa: Za su iya cin kwayoyin cuta da kwayayen macizan ciki a cikin kasar. Don haka idan aka ga yara na cin kasa a hana su. Kuma a rika sama musu abinci mai gina jiki kamar kifi nama da hanta, yana hana cin kasa. Ai za ka ga ma ko mai ciki takan ce tana kwadayin cin kasa, wadansu ma har su sa a sayo musu farar kasa su ci, duk karanci ne na sinadarai irinsu iron a jiki ke sa wannan kwadayin.
Ni kuma yarona ne dan shekara biyu wani abu a gabansa ya kumburo kamar maruru, daga baya sai ya baje. Ban san wane ciwo ba ne.
Daga Kabiru Mai Shayi, Maraba
Amsa: Wannan yana kama da ciwon kaba Malam Kabiru, idan ka sake ganin ya kumburo ka kai shi likitan tiyata ya duba shi, watakila sai an yi tiyata an gyara ta. Da fatan ana tsabtace kofunan shayi sosai.
Shin mutum mai ciwon hanta na hepatitis B ko A, zai iya aurar wadda ba ta da ciwon?
Daga Bilkisu M.
Amsa: A’a Malama ana kai ki gabas kina yamma. Me zai hada wata lafiyayya da mai ciwon hepatitis idan ba kaddara ba? Yadda ake daukarsa ai kamar ciwon kanjamau ne. Kafin a yi aure ma a yanzu a wasu jihohin sai an gwada ma’auratan an ga ba mai wannan ciwo an tabbatar ba dayansu mai shi, don ma kada a yi yaudara, kamar dai yadda ake auna ciwon kanjamau da na sikila da sauransu. Idan mace lafiyarta kalau kada ta auri mai ciwon hepatitis ko wane iri ne.