LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi

Shin akwai matsala ce idan fatar bakin jariri ta yi baki? Daga Ilyasu Wakili Akuyam Amsa: Eh, duhun fatar lebba a jariri zai iya nuni da abubuwa da dama, musamman ma abubuwan da kan iya hana iskar odygen zagayawa a jiki, kamar ciwon zuciya, ciwon hakarkari ko nimoniya, ciwon shawara da sauransu. Zai kuma iya […]

LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi
LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi

Shin akwai matsala ce idan fatar bakin jariri ta yi baki?

Daga Ilyasu Wakili Akuyam

Amsa: Eh, duhun fatar lebba a jariri zai iya nuni da abubuwa da dama, musamman ma abubuwan da kan iya hana iskar odygen zagayawa a jiki, kamar ciwon zuciya, ciwon hakarkari ko nimoniya, ciwon shawara da sauransu. Zai kuma iya kasancewa haka kamanninsa suke, canjawa yake. Don haka dai idan aka ga irin wannan a jikin jariri yana da kyau likitan yara ya duba ya tabbatar ba komai

 

Yarinya ce tunda ta fara girma kirjinta bai kara girma ba, shekarunta kusan 20. Shin hakan matsala ce ko kuwa? Muna bukatar shawara

Daga Ummi HIB

Amsa: Eh, matsala ce, yana da kyau likitar mata ta duba ta, a bincika a ga ko daga ina ne matsalar. Yawanci daga sinadaran jiki ne wato hormones, watakila akwai wadanda suka yi karanci a jikinta. Idan haka ne za a iya magance matsalar ta hanyar dawo da wadannan sinadarai. A wasu lokuta kuma daga kwayoyin halittu na gado ne, wanda wannan shi ne mai wahalar magani

 

Ina da yaro dan shekara biyar mai ciwon sikila. Wane mataki za mu dauka domin kiyaye tashin ciwon?

Daga Nasir A. Kano

Amsa: Da alama kai bako ne a filin. Domin mun sha magana a nan yadda ake bi a kiyaye yara daga yawan tashin ciwon sikila. Mafi muhimmanci a ciki su ne cewa ya kamata a ce yana da magungunan kariya daga ciwon zazzabin maleriya da na nimoniya da na karin jini, wadanda yake zuwa asibiti jefi-jefi ana ba shi. Wato yaro mai sikila ko tana tashi ko ba ta tashi sai an yi masa rajista a asibitin ciwon sikila domin karbar irin wadannan magunguna. Dole ya kasance a kan wadannan magunguna da’iman.

Sa’annan sai ka tabbatar yana samun ci-maka mai kyau, yana yawan shan ruwa ko abu mai ruwa-ruwa, yana kuma kwana a gidan sauro a kullum. Idan ka yi haka, to, za a samu dacewa sosai, da wuya ciwon ya rika tashi sosai.

 

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50