LAFIYAR MATA DA YARA – Mace ba ta sakin kwai idan ba ta da isasshen jini

Idan mace ba ta da isasshen jini a jiki an ce ba za ta iya al’ada ba, wannan na nufin ba ta da kwai ke nan ba za ta iya saki ba ke nan? Daga A.A. Danfuloti Amsa: Lallai Mallam Danfuloti ka yi tunani sosai domin da ma shi jinin al’ada na bin bayan sakin […]

LAFIYAR MATA DA YARA – Mace ba ta sakin kwai idan ba ta da isasshen jini
LAFIYAR MATA DA YARA – Mace ba ta sakin kwai idan ba ta da isasshen jini

Idan mace ba ta da isasshen jini a jiki an ce ba za ta iya al’ada ba, wannan na nufin ba ta da kwai ke nan ba za ta iya saki ba ke nan?

Daga A.A. Danfuloti

Amsa: Lallai Mallam Danfuloti ka yi tunani sosai domin da ma shi jinin al’ada na bin bayan sakin kwai ne, idan ba a samu juna biyu ba kenan. Wato idan mace ta saki kwai ko dai a samu juna biyu ko kuma idan ba a samu ba, a samu al’ada.

To duk da cewa kowace mace na da kwayaye miliyoyi a ajiye a cikinta kusa da mahaifa gefen dama da hagu, wadanda ta ke saki duk wata, to idan mace ta samu karancin jini sosai har ya kasance ma jikinta ba zai iya zubar da ko na al’ada ba, to kwayayen ma ana kin sakinsu ne kwata-kwata, ta yadda zai kasance tun da ba a sake su ba, babu maganar daukar ciki ballantana jinin al’ada. Har sai ranar da aka yi maganin matsalar, jiki ya ji alamar akwai isasshen jini sa’annan zai sa a saki kwai.

Ka ga kenan karancin jini ba rashin al’ada zai iya sa wa ba, har rashin haihuwa zai iya jawowa.

 

Likita me ke kawo ciwon farfadiya a mace bayan haihuwar fari?

Daga Goni Ari, Yobe

Amsa: Ai ya ma fi faruwa a haihuwar fari. Amma dai zai iya faruwa a kowace haihuwa. Mata wadanda suka gaji ciwon hawan jini ko suna da shi ciwon hawan jinin, ko ba su da shi, su ne suka fi shiga hadarin samun wannan jijjiga. Amma idan mace mai juna biyu ta fara awo da wuri, ko da tana cikin hadarin masu wannan matsala za a iya ganowa a kare aukuwarsa.

 

Me ke kawo zubewar gashin ido?

Daga Murja M.B

Amsa: Abubuwan da ke kawo zubewar gashin ka su ne dai za su iya kawo zubewar gashin gira kamar kora, amosani da makero da ma sauran kwayoyin cuta masu cin gashi irinsu kwayar fungus. Akwai ma yawan shafe-shafe, kamar wasu kayan kwalliya da akan shafa a gira, watakila suna iya zubar da gashin gira. Haka ma rashin samun isassun wasu sinadarai na abinci kamar sinadaran protein su ma za su iya kawo wannan. Haka nan akwai wasu cutukan jiki da ba su shafi suma ba, kamar ciwon makoko da zai iya sa zubewar gashin gira. Haka ma wasu magunguna, idan akwai wasu magunguna da kike sha ki tambaya ko   za su iya sa haka. Idan ki ka kasa gano dalili za ki iya ganin likitan fata wanda zai duba ya gano dalili.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna