LAFIYAR MATA DA YARA … Makon Allurar Rigakafi

Wannan mako mai shigowa ne hukumomin lafiya na duniya suka ware domin tunatar da iyaye muhimmancin allurai da magungunan rigakafi ga ’ya’yansu ’yan kasa da shekara biyar. Kai ba ma yara ba, har manya suna iya karbar wasu alluran rigakafi kamar na kiyaye ciwon hanta na hepatitis da na kiyaye ciwon dajin bakin mahaifa. An […]

LAFIYAR MATA DA YARA … Makon Allurar Rigakafi
LAFIYAR MATA DA YARA … Makon Allurar Rigakafi

Wannan mako mai shigowa ne hukumomin lafiya na duniya suka ware domin tunatar da iyaye muhimmancin allurai da magungunan rigakafi ga ’ya’yansu ’yan kasa da shekara biyar. Kai ba ma yara ba, har manya suna iya karbar wasu alluran rigakafi kamar na kiyaye ciwon hanta na hepatitis da na kiyaye ciwon dajin bakin mahaifa.

An tabbatar da cewa duk da akasin da za a iya samu jefi-jefi idan an yi wa wadansu yaran allurar rigakafi, alluran da magunguna su ne kan gaba a jerin abubuwan da mutum zai yi ya kare ’ya’yansa daga cututtuka masu nakasarwa da salwantar da rayuka.

Sai dai har yanzu an yi kiyasin cewa kusan yara miliyan 20 ne a duniya ba su taba karbar allurar rigakafi ba, mafi yawancinsu a irin kasashenmu. Kai a wani rahoto ma na wata kafar labarai ta kasar Turkiya (TRT), kasar nan ce ta fi kowace kasa a duniya rashin kai yara alluran rigakafi. Wannan zai iya zama gaskiya idan aka yi la’akari da cewa kusan fa duk yawan miliyoyin yara almajirai da muke da su ba ma jin sun taba karbar allurar rigakafi. Wato ke nan har yanzu akwai jan aiki wajen shawo kan al’umma su yarda da magunguna da allurar rigakafi. Ko don saboda alluran kyauta ake karbar su? Wadansu suna ganin da za a ce a sa wa alluran nan kudi da sai an fi yarda da su. Amma masana na ganin hakan zai iya hana marasa galihu kai ’ya’yansu allurai. Dalilan suna da yawa.

Wadansu sukan yi karfin halin tambayar likitoci da ma’aikantan lafiya sirrin lafiyar da ’ya’yansu suke morewa, domin kusan za a iya ganin ’ya’yan masu aikin lafiya lafiyayyu in ban da ’yan abubuwa da ka-je-su-zo. Akan ba su amsa da cewa ba magani ba ne sirrin, tunda ana ganin kamar ma’aikatan lafiya sun fi kowa sanin magani. A’a sirrin a kariya ne daga su kansu cututtukan. Babbar kariya kuwa ga ta nan muna magana a kanta. Daga ita sai cimaka mai kyau, sai tsabta, kamar yawan wanka, da tsabtace gida da yawan wanke hannaye. Ko mutum ba mai yawan abin hannu ba ne idan ya rungumi wadannan ’ya’yansa za su rika zama cikin koshin lafiya. Ko da ciwo ya zo, to zai zo da sauki sosai.

Me za mu iya yi a wannan mako mai shigowa? Za mu iya sauraron kafafen watsa labarai domin dakon shirye-shiryen hukumomi domin wannan mako. Idan ma ba a ji ba, yana da kyau a kai yara wadanda ba a gama musu allurar rigakafi ba cibiyoyin allurai domin a karasa musu. Wadanda ba a fara musu ba ma ya kamata a wannan mako a je a samu a fara yi musu, ba a makara ba in dai har yaran ba su wuce shekara shida ba, ba dole sai jirirai ba. Akwai jadawali na musamman na makararru. Daga shekara bakwai sama ne ake ganin an makara, amma dai za a iya bayarwa musamman alluran da za a iya bayarwa na loto-loto irin su na sankarau, ko na sarke-hakora, ba na yarinta ba.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50