Lafiyar Suntai: Ruwa na neman kare wa dan kada
Bisa dukkan alamu ruwa ya kare wa dan kada dangane da gaskiyar lafiyar Gwamnan Jihar Taraba Mista danbaba Suntai da ya hadu da hadarin jirgin sama kusan shekara biyu da suka gabata, kuma wasu na kusa da shi suke yaudaran ’yan Najeriya kan gaskiyarsa.Domin kuwa wata Babbar Kotu da ke Jalingo ta ki yarda da […]
Bisa dukkan alamu ruwa ya kare wa dan kada dangane da gaskiyar lafiyar Gwamnan Jihar Taraba Mista danbaba Suntai da ya hadu da hadarin jirgin sama kusan shekara biyu da suka gabata, kuma wasu na kusa da shi suke yaudaran ’yan Najeriya kan gaskiyarsa.
Domin kuwa wata Babbar Kotu da ke Jalingo ta ki yarda da bukatar da wasu na kusa da Gwaman danbbaba Suntai suka yi ta a hana bincike kan lafiyar Gwamnan.
Na kusa da Gwamna Suntai sun garzaya zuwa kotu ne a Jalingo suna neman kotu ta hana a binciki lafiyarsa, bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta kafa kwamitin kwararrun likitoci ya binciki lafiyarsa sakamakon da’awar da na kusa da shi suka yi cewa yana da lafiyar da zai iya ci gaba da mulkin jihar.
A lokacin da alkalin kotun Mai shari’a Silas Haruna yake yanke hukunci kan wannan karar, ya ce kotun ba ta da hurumin dakartar da binciken lafiyar Gwamnan.
Ana zargi na kusa da Gwamnan a karkashin Janar T.Y. danjuma mai ritaya da suka dauki kansu cewa su ne suka fi zama ’yan asalin Jihar Taraba na gaskiya da yaudarar ’yan Najeriya kan lafiyar Gwamnan, sai dai dawowa da shi a bayan nan na neman tona musu asiri.
Jama’a da dama a ciki da wajen Jihar Taraba na zargi Fadar Shugaban kasa da masaniya tare da daure gindin ga magoya bayan Suntai wajen yaudarar ’yan Najeriya a kan lamarin lafiyarsa.
Wani dan asalin jihar mai suna Mista John Bulus ya ce sanya bambanci addini da kabilanci a lamarin ba zai taimaki jihar ba.
Ya ce ya kamata wadanda suka dauki kansu sun suka fi zama na kusa da Gwamna su rungumi kaddara dangane da wannan lamari. “Wadanda ke kusa da Suntai duk abin da suke yi suna yi domin cimma burin kansu, ba don ci gaban Jihar Taraba ba,” inji shi.
Mista John Bulus ya ce dattijo T.Y. danjuma ya kamata ya kasance mai ba da shawara nagari ga daukacin ’ya’yan Jihar Taraba ba kawai ya ware wasu ya ce sune nasa ba.
Ya ce abin da ya kamata a yi shi ne a maida hankali wajen nema wa Suntai lafiya ta hanyar maida shi wurin jinya.
A cewarsa karya da yaudara kan wannan lamarin kamar yadda yaran Janar T.Y. danjuma ke yi kan lafiyar Gwamna Suntai ba zai taimaki shi kansa Suntai ko Jihar Taraba ba.
Wani dan siyasa a Jalingo Alhaji Nura Abdullahi ya ce rashin gaskiya da sanin ya kamata daga wasu da suka dauki kansu na kusa da Suntai suka kai jihar inda take a yanzu. Ya ce ya kamata ya yi a yi amfani da abin da tsarin mulki ya tanada ba nuna son kai ba.
Nura Abdullahi ya ce duk mai hankali ya san cewa danbaba bai da cikakken lafiyar da zai iya gudanar da aikin Gwamna.Ya kara da cewa amma an cusa addini da kabilanci kan maganar mulkin jihar.
Alhaji Abdullahi ya ce in wadannan mutane da suka dauki kansu na kusa da Suntai suka garzaya kotu don ta hana kwamitin likitoci da majalisar jihar ta kafa su binciki lafiyar Suntai ya nuna rashin gaskiyarsu.