Ranar Lahadi ce 1 ga watan Rabi’ul Auwal – Sarkin Musulmai

Mai alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana Lahadi 18 ga watan Okotoba 2020 a matsayin 1 ga watan Rabi’ul Auwal, 1442 bayan Hijira. Sarkin, wanda kuma shine shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Sakkwato. Halin […]

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Rabi’ul Auwal – Sarkin Musulmai

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana Lahadi 18 ga watan Okotoba 2020 a matsayin 1 ga watan Rabi’ul Auwal, 1442 bayan Hijira.

Sarkin, wanda kuma shine shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Sakkwato.

Takardar sanarwar da shugaban Kwamitin Ganin Wata na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai ya ce kwamitin cikin gida dana kasa sun samu labarin ganin wata kuma Sarkin musulmi ya aminta da sahihancin ganin.

Rabi’ul Auwal dai shine wata na uku a tsarin kalandar Musulunci zai soma Lahadi bisa ga sahihancin fitar watan da aka samu.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram