Lai Mohammed ya gaza a ma’aikatarsa —Majalisa

Kwamatin Majalisar Dattawa mai kula da Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu ta Kasa, ya tuhumi Ministan ma’aikatar, Lai Mohammed da gaza karasa ayyuka a ma’aikatar. Kwamantin ya kalubalanci Lai Mohammed kan gazawarsa ya karasa ayyukan da ke cikin kasafin ma’aikatarsa na bara a lokacin da ya je kare kasafin ma’aikatar na 2021. A tarihin Najeriya […]

Lai Mohammed ya gaza a ma’aikatarsa —Majalisa

Majalisar Wakilai

Kwamatin Majalisar Dattawa mai kula da Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu ta Kasa, ya tuhumi Ministan ma’aikatar, Lai Mohammed da gaza karasa ayyuka a ma’aikatar.

Kwamantin ya kalubalanci Lai Mohammed kan gazawarsa ya karasa ayyukan da ke cikin kasafin ma’aikatarsa na bara a lokacin da ya je kare kasafin ma’aikatar na 2021.

Ayyukan da majalisar ta ce ya gaza a kai sun hada da na gidan talabijin ta kasa da ke Gashua, Jihar Yobe, wanda aka kashe wa miliyan N250.

Kwamatin ya dasa ayar tambaya kan rashin gama aikin, ya kuma ce akwai tambayoyi da ministan zai amsa kan yadda ake gudanar da ayyukan ma’aikatar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa