Laifin me Arewa ta yi wa sauran yankunan Najeriya?
A yau GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci ne dangane da yanayin zamantakewar yankunan Najeriya, musamman ganin yadda a kowane lokaci ake samun sabatta-juyatta da hankalin jama’a, musamman ma idan dan Arewa ne ke kan madafar iko. Wadansu da ke ganin cewa su ’yan-ta-kife ne a yankin Kudu, sukan tsangwami al’ummar Arewa, suna nuna cewa lallai […]
A yau GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci ne dangane da yanayin zamantakewar yankunan Najeriya, musamman ganin yadda a kowane lokaci ake samun sabatta-juyatta da hankalin jama’a, musamman ma idan dan Arewa ne ke kan madafar iko. Wadansu da ke ganin cewa su ’yan-ta-kife ne a yankin Kudu, sukan tsangwami al’ummar Arewa, suna nuna cewa lallai kasar nan tasu ce, idan ba su ba sai dai kasa da sama su hade. Hakan ya sa da an motsa suke yi mana barna marar iyaka, mu kuma mun zama damo sarakan hakuri. Muna ji muna gani suka hallaka mana shugabanni na kwarai a Jamhuriya ta Farko. Ko a kwanan nan, wadansu tsageru a yankin Ibo sun fara maganar wai za su balle, su kafa kasar Biyafara. Shin abin tambaya, idan ma aka ce za a raba kasar nan, shin Arewa na da kaico? Mu duba mu gani:
Daga lokaci zuwa lokaci, wasu yankuna ko a ce wasu rukunnan mutane kan motso da yunkurin raba kasar nan, kowa ya kama gabansa. Suna ganin wai yankinsu yana da dukiyar fetur. Suna ganin cewa al’ummar Arewa, wadanda suka dade suna kira da sunan kaska-rabi-mai-jini ko cima-zaune, za su sha wahala idan aka raba. Ni kuwa na ce, anya? Shin a wannan batu na neman raba Najeriya, wa ya ki a dama, kuturu ko mai maho?
Ko ka taba zama ka tambayi kanka game da wadannan al’amura da suke gudana? Ina magana ne game da al’amuran da suka shafi zamantakewa a tsakanin kabilu da sassan kasar nan. Ka taba tambayar kanka cewa, shin a da can kafin a ce an hada sassa da yankunan kasar nan, a kirkiri Najeriya, shin yaya al’ummun kasar nan suke zaune? Haka kuma, bayan da Turawan Yamma suka yi abin da suka yi, suka cakude mu zuwa dunkulalliyar kasa mai suna Najeriya, yaya aka zauna tun daga farko, har zuwa lokacin da yankin Ibo ya fara hankoron neman kasar Biyafara? A yanzu kuma da ake ta wannan hauma-hauma, yaya muke zaune? Idan an raba kasar, me zai faru kuma wane yanki ne zai balbalce, ya rasa tudun dafawa? Amsoshin wadannan tambayoyi ne ya kamata mu yi, matukar muna son rufe bakin tsanya, wato idan muna son a daina yi mana barazana da batun raba kasa.
Tun farko ma abin da ya kamata a tambayi masu son a raba Najeriya shi ne, shin gida nawa za a raba ta? Raba ta za a yi ta fuskar kabila ko yanki? Shin za a raba ta biyu ne tsakanin Arewa da Kudu ko kuwa? Idan haka ne, yaya zama zai kasance a tsakanin al’ummar Yarabawa da Ibo da sauran kananan kabilun yankin Neja-Delta?
Misalin a ce mun amince a raba kasar zuwa biyu, Arewa da Kudu, to idan an raba din, yaya abin zai kasance? Ni kuwa na ce matukar muka natsu muka yi nazarin yanayi da tarihi, muka kalli abin da zai je ya zo, babu shakka babu abin da zai tsoratar da Arewa idan ta samu cin gashin kanta, a matsayin kasa.
Idan muka dauki batun mulki da siyasa, yankin Arewa sai dai ya koya wa wani yanki yadda ake yi. Su kansu Turawan mulkin mallaka, sun samu yankin da tsarin gudanar da mulki mai inganci da wayewa. Idan an raba kasar, abu ne mai sauki al’ummar Arewa su iya gudanar da tsarin mulki mai inganci da dacewa, yadda za a gina kasa bisa doka da oda. Mulkin da zai wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Idan muka dubi batun addini da al’ada kuwa, nan ma sai mu ce sam barka, domin kuwa al’adunmu kyawawa ne masu dauke da basira da wayewa. Ta fuskar addini kuwa, idan muka duba kuma muka yi nazari, ko a can baya ko a yanzu, kowane irin addini da ake a Arewa, da gaske ake yin sa. Idan ka dubi yanayin mabiya addinin Kiristan da ke Arewa, za ka same su sun fi tafiyar da addinin bisa gaskiya daidai gwargwado fiye da kininsu na Kudancin kasar nan. Haka ma batun yake idan ka duba mabiya addinin Musulunci, na Arewa sun fi inganci fiye da na al’ummun Kudu. Don haka za a iya amfani da koyarwar addinan nan, a samu hadin kai da juna, a samu zaman lafiyar da za ta samar da ci gaban kasa.
Wani al’amari da ake kallo ana yi wa Arewa gori, har ake son a raba kasar saboda shi, shi ne arzikin fetur. Ana ganin cewa fetur din ne babbar kafar kawo wa kasar nan kudin shiga, don haka da zarar an raba Najeriya, za su mallake shi su kadai, kuma ga su ’yan tsiraru. Ni kuwa na ce bayan tiya akwai wata caca, domin kuwa ba nan gizo ke sakar ba, wajen fidda abawa.
Ga masu wannan hasashen, su saurari wannan batun: Allah Ya albarkaci Arewa da ingantacciyar kasar noma, inda za ka iya noma duk wani tsiro da kake so mai albarka kuma a same shi. Idan ka dauki gyada, za ta iya samar da kudin shiga fiye da fetur. Litar fetur daya ba ta kai Naira 200 ba, amma nawa ake sayar da kwalbar man gyada, wadda ba ta kai lita daya ba? Ana sayar da ita sama da Naira 300. Kuma wahalar da ake wajen tace fetur, ba ita ake yi wajen matse man gyada daga tunkuza ba. Mace na zaune ma a gida za ta iya haka, wanda haka zai kara bunkasa sana’a da tattalin arzikin kasa.
Idan ka dauki auduga, ka dauki ridi, ka dauki dabbobin da Allah Ya hore mana, za ka ga cewa arziki na gani-na-fada yana nan Arewa. A yanzu haka, fata ko kirgi, ita ce ta biyu wajen samar da kudin shiga a Najeriya. Idan ana batun fetur da iskar gas din ma, akwai su kimshe a Arewa. Siyasa ce kawai ta hana a mai da hankali wajen hako su. Idan kuwa aka raba kasar, shi ke nan an samu damar cin gajiyar wannan dukiya.
Baya ga wadannan, Allah Ya albarkaci yankin Arewa da sauran ma’adanai a kasa masu daraja, kamar gwal da zinare da sauransu. Don haka, idan ma har an ce za a raba kasar nan, to ina ganin Arewa ba ta da damuwa, matukar dai za a mai da hankali wajen fuskantar gina kasa da gaske.