Laifuffukan yaki: Amnesty ta nemi a binciki Badeh da Ihejirika da sauransu
kungiyar Kare Hakkin dan Adama ta Duniya (Amnesty International) ta ce ya kamata a tuhumi wasu manyan sojojin Najeriya da laifin cin zarafin dan Adam da kuma laifuffukan yaki. A wani rahoto da ta fitar kan yaki da Boko Haram, kungiyar Amnesty International ta ce a cikin shekara hudu fiye da mutum dubu bakwai maza […]
kungiyar Kare Hakkin dan Adama ta Duniya (Amnesty International) ta ce ya kamata a tuhumi wasu manyan sojojin Najeriya da laifin cin zarafin dan Adam da kuma laifuffukan yaki.
A wani rahoto da ta fitar kan yaki da Boko Haram, kungiyar Amnesty International ta ce a cikin shekara hudu fiye da mutum dubu bakwai maza da kananan yara sun mutu a lokacin da suke garkame a hannun sojojin Najeriya.
Rahoton ya bayyana sunayen wasu manyan Janar-Janar da ya kamata a bincike su kan laifin kisan kai da azabtar da jama’a da kuma batar da mutane, wadanda suka hada da Manjo Janar John A.H. Ewansiha da Manjo Janar Obida T Ethnan da Manjo Janar Ahmadu Mohammed da Birgediya Janar Austin O. Edokpayi da kuma Birgediya Janar Rufus O. Bamigboye a daidaikunsu ko bisa bayar da umarni inda suka aikata laifin yaki ta hanyar kisa da cin zarafi da batar da mutane.
Sauran manyan kwamandojin sojin su ne Janar Azubuike Ihejirika, Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya daga Oktoban 2010 zuwa Janairun 2014 da Admira Ola Sa’ad Ibrahim Babban Hafsan Tsaro daga Oktoban 2012 zuwa Janairun 2014 da Iya Cif Mashal Aled Badeh, Babban Hafsan Tsaro daga Janairun 2014 zuwa yanzu da Janar Ken Minimah, Hafsan Hafsoshin Sojin Najeroya daga Janairun 2014 zuwa yanzu.
Rahoton ya bayyana cewa sakamakon hare-haren Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas an tsare matasa kusan dubu 20.
Amnesty ta ce “A wasu lokuta da gayya ake barin mutane cikin matsananciyar yunwa kuma tun daga watan Maris na shekarar 2011 mutum dubu bakwai ne suka mutu a lokacin da suke zaman wakafi a wurin sojoji.”
kungiyar ta ce wajibi ne a dora wa wadannan jami’ai alhakin abubuwan da suka faru amma suka kasa daukar matakan da suka dace don hana aukuwarsu domin a hana sake aukuwar irin haka a nan gaba. Sai kungiyar ta yi kira ga sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen rashin bin doka a bangaren sojojin.
Sai dai a martanin Hedkwatar Tsaro ta ce rahoton na Amnesty wani yunkuri ne na zame kafar sojojin Najeriya a yakin da suke yi da Boko Haram. Kakakin Hedkwatar Tsaron Manjo Janar Chris Olukolade ne ya bayyana haka inda ya ce manyan jami’an da aka ambata a rahoton babu dalilin da zai sa su aikata abin da ake zarginsu.