Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar
Wannan na zuwa ne bayan wasu hare-hare da Lakurawa suka kai wasu yankuna a jihar.

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Arewa domin inganta tsaro.
Ya yi wannan roƙo ne bayan ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira a Kangiwa, bayan harin da wasu da ake zargin Lakurawa ne suka kai musu.
- Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
- ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3
Harin da aka kai a ranar 9 ga watan Maris ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da ƙone ƙauyuka bakwai.
Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro, da Garin Rugga.
“Sansanin soji a yankin zai taimaka wajen gaggauta kai ɗauki idan an kai wani hari,” in ji Gwamna Idris.
“Dole mu yi duk abin da za mu iya don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”
Yayin ziyarar tasa, gwamnan ya yi alƙawarin taimakawa wajen sake gina gidajen mutanen da suka rasa matsugunansu.
Haka kuma, ya umarci hukumomin ƙaramar hukumar da su riƙa samar wa ’yan gudun hijirar abinci, tare da yanka saniya bayan kwana huɗu.
Bugu da ƙari, ya umarci a yanka raguna biyu don jarirai huɗu da aka haifa a sansanin yayin rikicin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa, Alhaji Sani Aliyu, ya gode wa gwamnan bisa ƙoƙarin da yake yi.
“Gwamnatin jiha tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar tsaro, amma muna buƙatar ƙarin tallafi daga Gwamnatin Tarayya,” in ji shi.
Gwamnan ya buƙaci mutanen da abin ya shafa da su ci gaba da haƙuri da addu’a, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.