Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Janar Olufemi ya ce da taimakon Sakkwatawa ne kaɗai za su samu nasarar kawar da sabbin ‘yan ta’addan.

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yi kira ga al’ummar Jihar Sakkwato da su taimaka wa dakarun rundunar da bayanai, bayan ɓullar ’yan ta’addan ‘Lakurawa’. 

Yayin ziyarar da ya kai Jihar Sakkwato, Janar Oluyede ya bayyana cewa, manufarsa ita ce duba shirin sojoji a jihar don tabbatar da suna cikin shiri.

“Na zo ne don ganin sojojina, na duba shirinsu na aiki, da kuma ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da aiki tuƙuru don kare ƙasar nan,” inji shi.

Babban Hafsan ya ziyarci Ƙaramar Hukumar Tangaza, ɗaya daga cikin yankuna da ke fuskantar barazanar daga ’yan ta’addan Lakurawa.

Har ila yau, ya gana da shugabannin al’umma, ciki har da Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni, inda ya jaddada masa muhimmancin goyon bayan jama’a ga aikin sojoji.

“Muna buƙatar goyon bayanku. Idan ba ku goyi bayanmu ba, ba za mu yi nasara ba, idan kuma ba mu yi nasara ba, Najeriya ba za ta samu tsaro ba,” in ji Janar Oluyede.

“Kullum za mu fuskanci ƙalubale, amma abu mafi muhimmanci shi ne yadda za mu magance shi. Ina tabbatar muku da cewa sojojin Najeriya ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin kare ƙasarmu.”

Jirgin Janar Oluyede ya sauka a jihar da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

Ya ziyarci yankin Masallaci da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza wanda ke da tazarar kilomita 25 zuwa Jamhuriyar Nijar.

A sansanin sojojin da ke yankin, ya samu bayanai daga kwamandojin rundunar, ciki har da Kwamandan Runduna ta 8 da Kwamandan Garrison.

Bayan haka, Babban Hafsan ya kuma ziyarci yankin iyakar Illela, inda ya sake samun bayani daga kwamandojin rundunar.

Sai dai ya roƙi goyon bayan al’ummar yankin wajen taimakawa aikin sojojin.

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe